"Na fara rubutu ne a dalilin ƙawata" - Ummyn YusraMalama Sakina Salees Al'eeman wadda aka fi sani a kafafen sadarwar zamani da "Ummyn Yusrah" ƙwararriyar marubuciyar yanar-gizo ce kuma babbar marubuciya daga jerin fitattun marubuta na jihar Bauchi wadda salon riƙon alƙalaminta ya fita zakka daga tulin dubban alƙaluman mata marubuta da muke da su a wannan zamani.
A wannan hirar da wakilin Mujallar Adabi, Musaddam Idriss Musa ya yi da ita za ku ji yadda marubuciyar ta faɗa harkar rubutu a dalilin wata ƙawarta da suke tare da kuma gwagwamaryar da ta sha biyo bayan zamowarta marubuciya.

Mujallar ADABI: Za mu so mu ji tarihin rayuwarki.

Ummyn Yusrah: Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu. Da farko dai sunana Sakina Salis Al-Eemam wacce aka fi sani da Ummyn Yusrah. An haifeni cikin garin Bauchi, a nan na yi karatuna na kuma yi aure.

Mujallar ADABI: makarantanmu za su so jin labarin yadda a ka yi kika shiga harkar rubutu musamman kasancewarki daga jerin shahararru kuma manyan marubutan da suke kan gaba a yanzu daga jiharki ta Bauchi?

Ummyn Yusrah: Na tsinci kaina a harkar rubutu ne ta dalilin wata ƙawata marubuciya, a lokacin tana rubuta wani littafi wanda na manta sunansa a halin yanzu, a ciki tayi rubutu kamar haka, "Maganar da ta ji ne ya sa ta zaman ƴan bori kamar yadda Ummyn Yusrah ta yi lokacin da ta kai yusrah asibiti ba lafiya a ka ce za a yi mata allura" Lokacin na basu labarin cewar muna asibiti ɗiyata yusrah ba lafiya. Da ta tashi rubutu sai ta rubuta hakan. Ni kuma ganin hakan ne yasa na ce nima a ranar zan yi rubutu kuma sai na rama abin da ta yi min. A taƙaice dai kamar wasa na fara rubutu wanda ban taba tunanin kwatanta yi ba. Don a baya idan na ga dogon rubutu jinjinawa Marubuta na ke da irin ƙoƙari da fasaharsu.

Mujallar ADABI: izuwa yanzu kin ɗauki shekaru nawa da fara rubutu kuma littattafai nawa kika rubuta?

Ummyn Yusrah: Shekaru biyu. Kuma littattafana aƙalla za su kai goma ko fiye da hakan.

Mujallar ADABI: za ki iya jero mana sunayensu tare kuma da waɗanda a cikin su me yiwuwa kika buga har a ka shigar kasuwa?

Ummyn Yusrah: akwai; Auren Awa Ashirin Da Huɗu, Hibbah, Yesmeen, Mijin Bahaushiya ko Matar Bahaushe, Rayuwar Asiya, Saina Auri Mijin Novel, Mawaƙi Ne, Rayuwar novel, Ka ƙi naka... Shi Ne Sanadi. Sai kuma ƙanana. Ban buga ko ɗaya ba.

Mujallar ADABI: wane labari kika fara rubutawa a farkon fara rubutunki, kuma meye labarin ya ƙunsa a taƙaice?

Ummyn Yusrah: Auren Awa Ishirin da huɗu na fara rubutawa. Wani aure a ka yi a unguwar mu, yadda a ka yi auren shine ya burgeni har na yi rubutu a kai. A na gobe za a daura auren ne, mijin ya ce ya fasa. Kafin ka ce me labari ya zaga unguwa, da dare ƙarfe takwas irin matasan unguwa suna hira sai wani daga ciki ya ke kokawa kan zancen, har ma ya ce da yana da hali da ya aureta a goben. A take abokan hirar tashi su ka ce in dai da gaske ya ke su za su yi komai game da bikin. Take ya yi na’am, nan a ka haɗa mishi sadaki da kayan lefe su ka nemi manya. A daren dai a ka tsara aure, washe gari aka sanar da iyayen yarinyar. A takaice dai a ka shirya duk wani shagali na bikin, ƙarfe takwas na dare amarya ta tare ɗakinta. Wanda ya zama cikin awanni ashirin da huɗun nan a ka shirya wannan auren.

Mujallar ADABI: kasancewar kin fara rubutu ne kamar wasa, shin yaya kika ji a karon farko, abin ya zo miki da sauƙi ne ko kuma kin fuskanci kalubale?

Ummyn Yusrah: A sauƙaƙe abin ya zo min gaskiya ban fuskanci wani ƙalubale ba, sai na ƙa idojin rubutu. Shima da na haɗu da ƙwararru abun sai ya zo min da sauƙi.

Mujallar ADABI: idan muka koma sashen rayuwarki kaɗan ta fuskar iyali, izuwa yanzu ƴanƴanki nawa?

Ummyn Yusrah: Yarana huɗu. Biyu maza biyu mata.

Mujallar ADABI:  Masha Allah, kasancewarki matar aure wadda take ɗawainiya da yara, shin yaya kike samun lokaci har ki samu damar yin rubutu?

Ummyn Yusrah: Na kan yi rubutu ne da hantsi idan sun tafi makaranta ko da yammaci ko da dare. Wani lokacin ma ko aiki na ke ina ɗan taɓawa.

Mujallar ADABI: ko kin taɓa fuskantar suka akan wani rubutu naki?

Ummyn Yusrah: Sosai na fuskanta a lokacin da na ke rubuta A dalilin link. Labari ne kan wata da ke yawan bibiyar links na groups, inda garin haka har ta faɗa group na ƴan maɗigo, ita ma ta bi sahu. A lokacin sai ya zamana nima ina bibiyar duk wani link don samun ƙarin bayani kan rubututa. Hakan yasa duk wanda ya ganni ciki sai ya bi ni akwatin sakona yana yi min nasihar na ji tsoron Allah. Kai, a taƙaice ma wasu har yanzu kallon hakan su ke yi min.

Mujallar ADABI: shin izuwa yanzu kin taba shiga wata gasa ta rubutu?

Ummyn Yusrah: Eh. Na taba shiga gasar Marubuta WhatsApp group.

Mujallar ADABI: waɗanne nasarori kika samu a sanadin rubutu?

Ummyn Yusrah: Alhamdulillah! Na sami nasarorin haɗuwa da mutanen ƙwarai.

Mujallar ADABI: me yafi burgeki a halin yanzu game da rubutu da marubuta?

Ummyn Yusrah: Yadda a ke raya adabi da kuma sada zumunci, sosai hakan na burgeni.

Mujallar ADABI: a ganinki wane tasiri marubutan Hausa ke da shi a rayuwar al'ummarmu ta yau?

Ummyn Yusrah: Sosai suna da muhimmanci ta wajen warware matsalolin yau, nunawa al’umma alfanun gujewa hanyar ɓarna zuwa ga hanyar ƙwarai, ilmantarwa, faɗakarwa kai har ma da nishaɗantarwa. Zan iya cewa Marubuci jigone na al umma.

Mujallar ADABI: kina da ra'ayin daina rubutu zuwa gaba?

Ummyn Yusrah: Wannan na Allah ne. Amma bana fatan haka.

Mujallar ADABI: dukda cewa kina daga cikin marubutan da kawo yanzu ba su fitar da littafi kasuwa ba, sunanki ya shahara, idan a na batun mata marubuta dake sahun gaba a jihar Bauch. A ganinki me ya kawo haka?

Ummyn Yusrah: Hakan ba zai rasa nasaba da kishin Marubutan jahata da na ke yi ba. Sosai mu na da haziƙan Marubuta a jihar Bauchi, rashin motsi da boyewarmu a lungu ya sa   mu ka zama kamar ba mu. Hakan yasa mu ka yi yunƙurin bayyanuwa a fili don jihar mu ta san da mu kuma ta dama da mu ta hanyar kafa ƙungiya, wanda za mu yi taron buɗe ta a ranar shida ga sabon wata mai kamawa in sha Allah. Da fatan Mujallar Adabi za ta amshi goron gayyatar da za mu kawo mata.

Mujallar ADABI: Insha Allah. A halin yanzu me yake ci miki tuwo a kwarya dangane da harkarki ta rubutu?

Ummyn Yusrah: zaman rubutu ya fi ci min tuwo a ƙwarya.

Mujallar ADABI: a kan samu daidaikun korafi daga wasu mutanen cewa marubuta musamman mata suna da girman kai, meye ra'ayinki kan hakan?

Ummyn Yusrah: Wake ɗaya shi ke ɓata gari. A ko ina akan sami banbancin halayya da ɗabi a. Hakan na iya faruwa, domin ko ni na gani a zahiri.

Mujallar ADABI: wasu na yiwa marubutan yanargizo kallon marassa wayo saboda dora littattafansu a kafafen zamani da suke yi ba tare da sun samu sisin kobo ba, me zaki ce kan haka?

Ummyn Yusrah: Ba rashin wayo ba ne ba. Meyuwa ba sisin kwabon ne damuwarsu ba. Burin su, su isar da sako ga al’umma ne ta yadda za su amfana da shi.

Mujallar ADABI: To ya kike kallon batun cewa samun marubuta masu ɗora labaransu a social media ya haifar da mutuwar kasuwar littattafai kamar yadda masu ɗab'i da masu sayar da littattafa suke korafi?

Ummyn Yusrah: Gaskiya ya daƙusar da sosai, domin yanzu cikin sauki ba tare da ka kashe sisin kwabo wajen sayan littafin ba za ka samesu kan wayarka. Hakan ya kawo dakushewar tasu. Amma fa ba duk ba, domin har yau ana samun masu saye.
Reactions
Close Menu