Me yasa Danjuma Katsina ke son yi mana zagon kasa? - Rabi’u Na’auwa

 

Rabiu Na'auwa

S

anin kowa ne a lokacin da muka dauko nauyin gabatar da taron marubuta a katsina Danjuma Katsina ne mutumen da ya fito fili ya ke sukar wannan taro, ya yi ta rubuce- rubucen da muka rasa dalilin yinsu, duk wanda ya ke zaurukan marubuta shaida ne a kan hakan. Duk wannan bai sa mun yi fushi ba, ni ne na rubuta takarda, na samu Danjuma har shagonsa na kai masa,  a kan ya taho muyi wannan hidima tare,  amma danjuma bai taba zuwa taron tattaunawarmu ko sau daya ba.


    Wannan bai sa gabanmu ya fadi ba, muka ci gaba da kokarin gabatar da taronmu.  kusan wata takwas muna ta shiri , sai da abu ya kankama ina tunin bai fi saura kwana goma ba sannan Danjuma ya kirani a waya, ya ce ya ji an ce munje ofishin sakataren gomnati neman gurin taro,  na ce masa haka ne,  ya ce to daman ya kirani ne ya bani shawara a matsayina na shugaban taro.  Naji dadin hakan saboda daman can ban rike shi da komai ba,  ni dai nasarar taro nake bukata. Wannan shi ne lokacin da Danjuma ya fara saka mana baki a shirye- shiryen taronmu.


    Bayan kammala taro na tabbatarwa da Marubuta cewa sai nayi publication ko dai na takardun da aka gabatar ko na gajerun labarai. a matsayina na Shugaban Kwamitin zartarwa Saboda karamci na gayyaci Danjuma Katsina da Bashir Abu Sabe su zo mu hadu muyi editing na wannan wannan littafi da zamu buga. Na kuma ba Kabir Assada aikin littafin.


    Abinda ya fara ba ni mamaki, Bayan mun gama tattara labarai daga Marubuta wadanda muka taru a kan a turawa Abu sabe a matsayinsa ne lead Editor wanda zai duba ka'idojin rubutu kumshiya da kuma tsari,  daga nan in ya gama ya turo mana.  shiru- shiru ba amo ba labari na kira Abusabe ba adadi ya na ce min in yi hakuri bai ida ba.  Kirana da shi na karshe sai ya ce min ya gama ya turawa Assada ya kuma tura min ya turawa Danjuma,  na ce masa ni dai ban gani ba ya ce zai sake tura min. Sai na kira Assada ya tabbatar min da an tura na ce masa to ya fitar mana da dormy copy ya fitar ya turo min da shi na je tasha na karbo na kai wa Danjuma na ce su fara dubawa zan zo in karba nima in duba in sun gama shima haka na yi ta binsu da waya daga karshe Danjuma ya kira ni ya ce ya turawa Assada,  na ce masa kai da ba kai ka karbo ba,  ba kuma kai kadai ne edita ba me ya sa za ka tura baka bani na duba ko sanar dani ba?  


    Ya ce in yi hakuri in sa ke turawa a sake fitar min da wani,  wannan ta wuce.  Na tuntubi Assada sai ya ce min Danjuma ya ce a cire sunana a cikin editors,  sai na tambayi Assada  Danjuma ne ya baka aikin littafi ?  ya ce" a'a."  Na ce to me ya sa zai ce a cire sunana in har ni Shugaban kwamiti kuma wanda ya samo kudin aikin littafin nan,  na kuma bada aikin  ban ce a cire wani ba,  wani zai zo daga gefe ya ce a cireni?


    Sai ya ce ya ce wai baka yi editing ba,  sai na ce masa ka sake turo min da wani copy sai in kara a kan wanda na yi.


Batun tace rubuce-rubucen

    Ni ne na rubuta jawabin godiya,  wanda daga karshe aka fasashi aka kara wasu abubuwa ya zama jawabin editors. Da ni aka zauna aka ware sunan littafin gobarau a shagon Danjuma da yamma. Littafin Gobarau ya yi kwana goma sha uku a hannuna ina editin a kansa,  daga karshe na fitar da wasu gyararraki kamar haka:

1. Ba'a saka ranar da aka yi taro ba,  a cikin jawabin godiya.

2. Wasu labaran sun shiga shafin wasu yakamata kowane labari ya zamo a shafi na kashin kansa,

3. Samar da tsarin baidaya ga duka labaran dake cikin littafin ba kamar yanda wasu suka saka lambobin wayoyi wasu Email was kuma ba ko daya.

4. Saka sunayen wasu marubutan da basu halarta ba aka saka wadanda suka halarta.

Rashin saka sunan uban taro da wakilin sarkin Katsina a cikin Jawabin godiya.

Da wasu gyare-gyare da dama.

    

    Bayan na kammala na kira Abusabe a matsayinsa na Edita mai jagorantar aikin ya ce in same shi a gidan man Total na kofar kwaya wajan Aminu mai faci.  Na same shi na kai masa gyare-gyaren da na yi ya duba ya ce shima ya ga wasu zai kara gyarawa in bashi lokaci ya tafi da nawa ya kara nashi.  Bayan kwana uku ya kirani na sake komawa wannan gidan man na karba na turawa Kabir Asdada sokoto. Ni na san na yi wannan,  ina kalublantar Abu Sabe ko Assada su fito su ce banyi wannan ba.


    Sannan ni na fito da nawa editing da na yi a littafin Gibarau ina Kalubalantar Danjuma Katsina ya fito ya fadawa Duniya gyaran da ya yi a littafin Gobarau.

 

    Taron da ya haifar da wannan littafi? Wanda ya nemo kudin da ka buga littafin? Kuma wanda ya jajirce sai an buga littafin?

    Me ya sa Danjuma Katsina yake son ya fitar da masu aikin da wadanda suka bada aikin shi ya kwace wannan littafi?


    In kuwa haka ne lallai adabi yana cikin Danja in har wani zai koma gefe sai marubuta sun gama wahala sannan ya yi masu fashin nasarar da suka samu.


    Ina kira ga marubuta da sauran masu hidimtawa Adabi da su tashi tsaye wajan kare adabi daga farmakin cima zaune masu fashin Nasara da ciwon hassada.

 

 

Reactions
Close Menu