An Yi Bikin Karrama Gwarazan Gasar BBC Hausa Na Hikayata 2019

Bikin na Hikayata wanda ya gudana a daren ranar Juma'a 26 ga Aktoba, 2019 an shirya shi ne don a karrama gwarazan gasar kagaggun labarai ta BBC Hausa ta mata zalla wato Hikayata, inda Safiyya Ahmad 'yar asalin garin Zariya na jihar Kaduna ta zo ta daya da labarinta mai suna "Maraici". An ba ta kyautar dala 2,000.


Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu wadda ita kuma ta kasance 'yar jihar Kano ce ta zo ta biyu da labarinta mai suna "Ba a Yi Komi Ba," wacce ta karbi kyautar dala 1,000.
Sannan labarin "A Juri Zuwa Rafi" na Jamila Babayo da ita kuma ta kasance'yar shiyyar arewa maso gabashin Najeriya daga garin Potiskum na jihar Yobe shi ne ya zo a matsayi na uku, wadda ta karbi kyautar dala 500.

Reactions
Close Menu