"Ba Aikin Yi Ne Ba Mu Da Shi Ba" - Martanin Marubutan Hausa

"Ba Aikin yi ne ba mu da shi ba" - martanin marubutan Hausa
An dade ana yiwa marubuta labaran Hausa kallon hadarin kaji bisa abubuwan da wasu gungun mutane daga cikin al'umma ke yanke hukunci akan su ba tare da neman jin ta bakin marubutan ba.
Daya daga daga manyan abubuwan da suka kawo hakan biyo bayan wani bincike da mujallar ADABI ta gudanar shi ne marubuta da dama masu amfani da harshen Hausa ba a rasa zukatansu dauke da wani tabo na bacin rai ko bakar magana da wani ko wasu suka yi musu saboda tsintar kan su da suka yi a harkar rubutu musamman ma a daidai gabar da suke kokarin tasowa.
Bayan tattaunawa da jerin wasu marubuta da dama da Mujallar ADABI ta yi tare da tambayar tarihin yadda suka fara rubuce-rubucen labaran Hausa da kuma yadda mu'amalarsu ta kasance da al'umma bayan an fahimci cewa sun zama ko suna da niyyar zama marubuta, sakamakon ya nuna cewa wasu marubutan sun hadu da nau'ikan kalamai na cin fuska da kuma rashin martabawa inda har ta kai ga wasun na cewa an kira su da sunaye irinsu "mahaukaci" ko "marar abin yi" dasauransu.
A bisa wannan dalili ne Mujallar ADABI ta yi wani kwarya kwayar bincike ta hanyar tuntubar al'umma da ma su kansu marubutan don kokarin gano inda matsalar take.
Shafin Ra'ayi zai kawo muku cikakken rahoton tare da ra'ayoyi da ma martanin da marubutan suka yiwa masu yi musu wannan kallo.
Reactions
Close Menu