Abubuwan Da Suka Kamata A Kula Da Su A Wannan Lokacin Na Hunturu – Dakta Makarfi

29 Nuwamba, 2019A halinAbubuwan Da Suka Kamata A Kula Da Su A Wannan Lokacin Na Hunturu – Dakta Makarfi yanzu muna shigowa wani sabon yanayi ne wanda al’ummarmu ke kira da lokacin sanyi ko kuma lokacin hunturu. A kan hakan ne Mujallar  ADABI a yau Juma’a ta zanta da Dakta SHEHU ABDULMUMINI MAKARFI, shugaban Asibitin Musulmi da ke stadawa Tudun Wada, Kaduna, domin jin matakan da ya kamata al’umma su dauka wajen kaucewa cutukan da suke tattare da irin wannan yanayin. 

Dakta wane irin yanayi ne muke a cikinsa a halin yanzun?
Yanzun muna yanayi ne na hunturu, da kuma sanyin da ke shigowa, wanda a halin yanzun za a sami canjin yanayi, domin iska ce busasshiya wacce take dauke da zafi za ta rika bugawa, akwai kuma cututtuka masu yawa a cikinta, domin kura na tashi tana kadawa, tana dauko cututtukan da suke a karkashin kasa. A wannan yanayin, cututtuka da suka shafi sashen numfashi misali kamar masu ciwon Asma, mara, mashako da ciwon Nimoniya ga kananan yara duk za mu fuskance su.

Akwai kuma al’adar da mutanan mu suke da ita ta jin dumi saboda hunturun nan, inda za ka ga an hada wuta an zagaye ta ana shan dumi ana hira a lokacin yammaci, dare ko kuma da safe kafin a fita neman abin rayuwa. Wanda in yara ne ma sai ka ga sun fara ture-ture ta yanda har wani ma zai tura wani a cikin wutar, wanda daga nan ne cututtuka na kuna za su fara tasowa.

Akwai kuma manya masu kokarin su dauki wuta a zuba a kasko a kai daki domin a dumama daki ya yi dumi kafin a kwanta, wanda wannan shi ma kuskure ne babba, domin tana iya yiwuwa akwai bera a cikin dakin nan da zai iya janyo wani abu ya jefa shi a kan garwashin wutar nan alhalin kai kana barci ba ka sani ba. Ko kuma ma kai ba ka sani ba, ka janyo mayafinka da kafarka ko da hannunka. ka jefa a cikin kaskon wutar nan. Wanda a hakan wutar tana iya tashi, in ma wutar ba ta tashi ba, wannan hayakin wanda a mafi yawan lokuta shi yake kashe mutane ba ma wutar ba, yana iya turnuke wanda yake kwance a cikin dakin, sai ka ga an wayi gari wanda suke a cikin dakin nan suna cikin babban hadari.

In ma duk babu wannan, ita iska idan ta sami zafi takan kumbura iskan ne, to kuma ga daki a kulle yanda babu wata iska mai kyau da mutum zai shaka, sai ka ga in ba a yi da gaske ba, da safe sai an balle dakin sannan a dauki gawa. Don haka ya kamata a shirya wa cututtukan nan da suke fuskantar mu a halin yanzun a kiyaye. Farko fadakarwan a daina shigar da wannan rushin cikin daki a kwanta da shi, hikimar da ya kamata a yi shi ne a hura shi a waje in ya gama ci sai a shigar da shi cikin dakin ya sami ko da awa guda dakin ya danyi dumi sannan in za a kwanta sai a fitar da shi waje sannan a kwantan, wannan shi ne daidai.

Abu na biyu kuma kar a bar yara su kadai a gaban wuta da sunan suna shan dumi, domin wani ma sai ka ga ya dauki kara ya cokana ya je ya sanya a wani wajen, wanda da hakan sai ka ga gobara ta tashi.

A wannan yanayin na hunturu kuma ya kamata a saya wa yara kanana tufafi masu kauri da safar kafa da ta hannu da hula mai kyau wacce za ta rufe masu har kunne, musamman wadanda suke zuwa makaranta. A kuma tabbatar da an hana su yawo a kan titi suna gararamba, domin wannan shi ke sanyawa su shaki iska mai gauni sai su dawo suna tari suna mura har ma ka ga an kai ana kwanciya a Asibiti.

Saboda kuma bushewar iskar nan, za ka ga ita kanta fatar jikin dan adam za ka ga cewa tana bushewa tana tamukewa kaco-kaco kowa ma ba shi da kyawun gani a wannan yanayin. To shi ma ya kamata a kiyaye kullum a yi wanka, a kuma nemi man shafawa wanda yake da danko a shafa, wanda shi ne zai rufe hanyoyin fitar damshi daga jikin dan adam, sai ka ga an sami dumaman yanayi a jikin dan adam da zai hana masa wannan kaco-kaco din.
Reactions
Close Menu