Cikinmu ya duri ruwa don tsoron rushewar Kannywood - Falalu Dorayi

29 Nuwamba, 2019
Masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood a Najeriya na fuskantar barazanar durkushewa kamar yadda masu sharhi kan al'amura suke cewa.

Masana'antar dai na fuskantar matsaloli da suka hada da satar fasaha da rashin zuba jari daga masu wadata da kuma rashin kulawar gwamnati, duk kuwa da cewa ta shafe gomman shekaru da kafuwa.

Falalu Dorayi wanda babban mai bayar da umarni ne kuma ya kan fito a matsayin tauraro a wasu fina-finan, ya shaida wa Mujallar ADABI cewa wannan hasashe na masu sharhi gaskiya ne.

Ya ce a yanzu halin da masana'antar ke ciki ya haifar da karayar arziki da durkushewar jari da kuma rufe wasu kamfanonin shirya fina-finai masu girma.

Jarumin ya kara da cewa tun farkon kafa masana'antar sun dogara ne a kan sayar da fina-finansu ta hanyar CD, "amma da yake yanzu an samu ci gaban fasaha sosai mutane kusan sun daina kallon fim a CD sai a wayoyin hannunsu da sauran sabbin hanyoyi," in ji shi.

"Idan a da kana yin kwafi na CD 100,000 to yanzu da wahala ka iya yin 5,000 kuma ko ka yi ba za su sayu duka ba. Don kana zaune wani zai sauke fim din (dowloading) daga manhaja ya aike wa mutum 100 a lokaci daya.

"Sannan kuma ko sinima ka kai fim dinka da wahala ka samu riba don kuwa babu sinima din da yawa a arewacin Najeriya kamar kudanci," a cewar Falalu.

Duk da cewa dai yanzu a duniya an yi ci gaban da dora bidiyo a shafin YouTube kadai na sa wadansu samun makudan kudade da shafin ke biyansu, har yanzu a masana'antar Kannywood ba a fara cin gajiyar abin sosai ba.

"Ai ko ka dora a Youtube din ba za ka samu irin kudin da zai samar maka riba ba, don wata tashar taka ta Youtube ma idan ba ka da masu kallonta da yawa ai ba wani talla da za ka samu balle har kudi su shigo.

"A takaice dai Youtube ba zai sa mu mayar da kudi har mu ci riba ba," in ji daraktan.

Falalu na ganin idan dai ba a tashi tsaye ba to lallai wannan na iya zamowa silar rushewar wannan masana'anta da dubban mutane ke cin abinci a cikinta.

"Sai dai kawai yawan mutanen da ke cikinta da yawan fadada tunani da ake yi to zai iya taimakawa a farfado da ita.

"Gaskiya akwai faduwar gaba don kuwa inda abincinka yake a ce yau yana tangal-tangal ai dole ciki ya duri ruwa."

"Fatanmu yanzu gwamnati ta shigo cikin lamarin, sannan masu kudi su zo su zuba jari su bude sinimu da yawa a yankinmu. Don kuwa masu harkar sinima sun ma fi masu shirya fina-finan samun kudi," kamar yadda daraktan ya ce.

Reactions
Close Menu