Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a Birtaniya


Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Fatima Abdullahi da ake kira Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a wani kasaitaccen bikin fina-finan Afirka da aka gudanar a Birtaniya.

Hoton jaruma Fati Washa a yayin da take karbar award


An sanar da Washa ne a matsayin gwarzuwar jaruma a taron karrama 'yan Fim da aka gudanar ranar Asabar a birnin London.
Bikin wanda ake kira Afro Hollywood Awards ya shafi karrama jaruman fina-finan harsunan Najeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma na Inglishi a sassan kasashen Afirka, Fati Washa ta lashe kyautar ne saboda rawar da ta taka a Fim din 'Sadauki.'
Jarumar ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a Fim din da ta fito "Jamila" da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a "Uwar Gulma"
Rahama Sadau ta wallafa hoton bidiyo a shafinta na Instagram, lokacin da Washa ta ke karbar kyautar, inda ta bayyana farin cikinta da godiya.
Ita ma Washa ta sake wallafa bidiyon a shafinta na Istagram.
Washa ta ce ta sadaukar da wannan kyautar ga masoyanta tare da gode ma su, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook da ba a tantance ba.
Karo na 23 ke nan da ake gudanar da bikin karrama 'yan fim din wanda jaridar African Voice Newspapers a Birtaniya da gidauniyar Esther Ajayi da Ned Nwoko ke daukar nauyi.
Wadanda ke shiryawa da daukar nauyin bayar da kyautar a Birtaniya sun ce Sama da fina-finai 500 ne daga Afirka suka shiga gasar wacce aka fara a 1996.

Reactions
Close Menu