Illolin Da Rashin Isasshen Barci Ke Haifarwa Ga Lafiyar Mutum

29 Nuwamba, 2019Mutum na iya kauce ma  duk wani al’amarin da yake dangantaka da barci, to amma fa wani abin daban shi ne idan aka cigaba da tafiya kamar hakan, zuwa wani lokaci abin yana iya haifar da, ko kuma sanadiyar kamuwa da cutar tabin hankali da zai iya saka mu bacci na dan wani lokaci.

Wani lokacin ma har  matsalar ta kan kai ga mutuwa, kamar dai yadda wani bincike wanda ya nuna a sanadiyar hakan mutane na iya fara nuna wadansu dabi’u wadanda kuma na iya nuna cewar sun hadu da matsala. 

Rayuwar al’umma tana cike ne da wasu abubuwan da suke rikirkita masu al’amura, bama kamar ma idan sun kai cimma wasu shekaru. To sai dai idan ana maganar abubuwan da suke ɗaukar lokaci, to akwai abin da ya sha gaban duk waɗannan, wanda kuwa wannan abu shi ne barci. 

A binciken da aka gudanar a kwanan baya akan illolin barci a (American Academy of sleep medicine). Sun gano cewa ya kamata mutum ya samu lokacin bacci sama da awa bakwai a ko wacce rana saboda samun lafiyarsa. Rashin samun yin isasshen barci yana da  nashi matsalolin da suke damfare a jiki, bayannan  kuma  idanhar aka samu damar yin yana warware wasu daga cikin matsalolin, da jiki ya samu kan shi a ciki. 

Binciken ya nuna cewar yawan yin barci da kuma yin sa a lokaci zuwa lokaci yana sa, a  samu saurin warkewa (idan aka ji rauni), yana kare garkuwar jiki, yana inganta karfin jiki. Bayannan kuma abin da ya fi komai shi ne mutum yana tashi a wartsake bayan ya samu damar yin isasshen bacci. 

Yana kuma sa hutu, yana kuma sa kwakwalwa ta kasance babu wata matsala, domin samun lafiyar jiki. Sai kuma wani abu shine a lokacin da ake yin bacci kuma yana da kyau a kawar da duk wasu abubuwa da za su iya tayar da wanda ke yin barcin, alal misalin irin karar da waya take yi. bayan nan kuma ya kasance dakin da duhu babu wani haske, wannan shine irin yanayin dakin daya kasance za a iya yin barci. 

Sai kuma a guje wa cin abinci mai yawa kafin a kwanta barcin, akwai kuma bukatar a rika yin hatisayi duk rana wato motsa jiki. Ta bangare daya kuma  rashin samun isasshen bacci yana iya haifar da ciwon sikaria ga kuma ciwon zuciya, yana ma iya haifar da damuwa da kuma ciwon jiki. 

Saboda magance wadannan matsalolin, idan dare ya yi sai jikin mutum ya yi rauni, a kama jin rashin dadi, a ringa fama da kasala, sai kuma a ji ido ya yi nauyi, yana kokarin rufewa. Idan kuma aka ci gaba da dagewa ana cewa ba za a yi shi barci ba, sai a kasa yin duk wasu abubuwa da ake yi, daga nan sai a fara manta abubuwa. 

Idan aka yi watsi da dukkanin wadannan alamu na bacci, aka ki yin barcin har zuwa samun wasu ‘yan kwanaki, kwakwalwa na iya shiga matsala ko kuma rudani, sai a fara wasu mugayen tunane-tunane, sai a ringa raya abubuwan da a zahiri babu su. A cewar Atul Malhotra daraktar sashen kula da barci a jami’ar California. 

Binciken da aka gudanar masu yawa  sun nuna yadda jikin mutum yake samun matsala sabo da rashin isasshen barci, yake kuma shafar yadda jikin dan adam yake yin aiki, musamman ma inda yake haifar da matsala a ƙoda. 

Akwai matsala da take shafar mutum na rashin isasshen bacci, ba tare da san ran sa ba, sannan kuma ta haifar masa da illa. To ga kadan daga cikin irin illoli da matsalar waɗanda ba su samun  yin isasshen barci ke afkawa cikin damuwa irin daban –daban kamar haka : 
1. Ɗimaucewa, a wani lokaci hadari sai ya riski mutumin ba tare da ya ankara. 
2. Haka kuma suna afkawa cikin matsalar ciwon hawan jini.
3. Ciwon bugun zuciya.
4. Ciwon asma.
5. Cutar kansa. 
6. Ciwon koda.
7. Ciwon sikari da dai  sauransu. 

To, sai dai fa duk waɗannan matsalolin da rashin barci ke haifarwa, ba sa kasancewa, suna kaucewa idan mutum ya samu isasshen barci. Idan ma akwai illa da hakan ke haifarwa, ta na gushewa daga baya. A cewar Farfesa Jerome Siegel, na sashen kula da barci na jami’ar California.Reactions
Close Menu