Ko Yakamata Maras Lafiya Ya Motsa Jiki?

29 Nuwamba, 2019Ko shakka babu motsa jiki muhimmin wani abu ne, domin ya na taimakawa wajen warware jijiyar jikin dan adam, baya ga kara tallafa ma garguwan jiki. A wani bincike da a ka gudanar a jami’ar South Carolina, an gano cewar mutanen da su ka mai da hankali wajen fita yin motsa jiki akai-akai su na samun kashi 20% na kariya da kamuwa daga wasu kananan cututtuka da ke shiga jiki, musammam ma waɗanda su ka shafi bangaren numfashi a kan waɗanda ba su fita.
Amma kuma sau da yawa mutane kan tambaya, ko za su iya yin motsa jiki a lokacin da ba su da lafiya? To, amsar wannan tambaya dai ita ce wannan ya danganta ne da irin tsananin cutar da ta ke damuwar mutum. Amma kuma sai dai abin da a ka sani shi ne motsa jiki ya na taimakawa wajen warware jijiyar jikin dan adam, ya kuma kara karfafa garkuwar jiki wajen fada da cututtuka masu karya garkuwar ta jiki.
Don haka ko ba ka da lafiya ka na iya yin motsa. Wannan kuma ya danganta ne gwargwadon karfin jikinka.
Kwararru wadanda kuma masana ne a wannan fannin, kamar su Dabid Nieman, Farfesa, kuma  darakta ne na Human Performance Lab a jami’ar Appalachian, yanayin cutar da kuma yadda take ita za ta nuna ko maras lafiyar zai iya fita ko ba zai iya fita ba saboda shi al’amarin na motsa jiki. Amma idan misali matsalar daga wuya zuwa sama ne, wato kamar abin da ya shafi hanci, a sakamakon mura, ko kaikayin makogwaro, ba zai hana mutum fita ya yi motsa jikin ba.  matukar yana kan jin kwarin jiki, amma kar ya dauki lokaci mai tsawo daga nan kuma sai  ya huta kadan.
Amma idan rashin lafiyarka ya shafi wasu abubuwa ne kamar amai, ko gudawa, ko  kuma daukewar numfashi, ko bugun zuciya, ko dai  abin da ya shafi gabobin jiki, ko zazzabi da dai sauransu. Likitoci na ba da shawarar kar a yi motsa jiki don jikin kai maras lafiyar ka samu kuzari. Amma a cikin irin wannan halin maimakon a samu lafiya sai kuma jiki ya sake rikirkicewa.
Saboda haka idan kana fama da irin waɗannan cututtuka kana bukatar yin hutu ne don samar ma  jiki lafiya, domin hutun zai sanya garkuwan jiki su yi fada da waɗannan cututtukan da suke damuwar jikin maras lafiyar, da ma wasu masu kokarin samun mafaka. Kuma ko da kana da kuzarinka wanda zai baka damar iya fita, yana da kyau ka yi la’akari da irin kayan da ake amfani da su wajen shi motsa jikin, don gudun kamuwa da wasu cututtuka ko wasu su kamu da cutar da take damun ka.
Reactions
Close Menu