Kannywood: Sharhin Fim Ɗin ‘Abbas’ Na Kamfanin Easy Motion Pictures

Suna : Abbas
Tsara labari: Sulaiman Bello Easy
Kamfani : Easy Motion Pictures
Daukar Nauyi: Ibrahim I.Daneji
Shiryawa : Kabiru A. Yako
Bada Umarni: Sulaiman Bello Easy
Sharhi: Musa Ishak Muhammad

Jarumai: Nuhu Abdullahi, Malam Inuwa Ilyas, Ibrahim Bala, Kabir A. Yako, Sani Abdul, Hadiza Muhammad, Maryam Muhammad, Aisha Baby, Hajara Usman da sauransu.

Fim din Abbas fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani matashi mai suna Abbas (Nuhu Abdullahi) wanda ya kasance mai cikakken gata, domin kuwa mahaifinsa mutum ne Attajiri. Sai dai wannan arziki ba abinda ya karawa Abbas sai bin hanyar banza, domin bashi da abinyi sai bibiyen mata da yawan zuwa fati cikin dare.

Wannan mummunar dabi’a ta Abbas kullum tana bakantawa mahaifinsa wato Alhaji (Malam Inuwa Ilyas). Kullum ya na masa nasiha amma kullum kara shiga daji ya ke. A bangare guda kuma akwai matar mahaifinsa wato Hajiya Amina (Hadiza Muhammad) wadda ta rike Abbas kamar dan cikinta, sai dai shi kullum bai da abun yi sai wulakanta ta da kuma fada mata bakaken maganganu. Kuma haka kullum ya ke yi mata gorin haihuwa, saboda ita tsahon zaman da ta yi a gidan ba ta samu haihuwa ba.

A nan ne sai Alhaji ya rasu, a cikin kankanin lokaci, Abbas ya matsawa Hajiya Amina, a kan lallai a raba dukiyarsa a bashi a barshi. Nan ta bashi hakuri cewa ya yi hakuri so take ya kara girma sai ta dauki dukiyarshi ta bashi. Nan ya zazzage ta ya faffada mata bakaken maganganu yadda ya ke so.

A karshe Abbas dai ya gamu da gamonsa, bayan ya je ya samu wata Bafulatana ya yaudare ya yi mata fyade, wanda sanadinhakan su ka kai shi wajen boka a ka yi masa asiri wanda ya shanye jikinsa gaba daya.

Abubuwan Yabawa
1. Fim dinya samu labari mikakke wanda bai yanke ba.
2. Fim dinya nuna cewa rana dubu ta barawo ce rana daya kuma ta mai kaya, kamar yadda ya faru a kan Abbas.
3. Fim dinya samu aiki mai kyau.

Kurakurai
1. Ya kamata a nuna nadamar Abbas a fili sosai, domin iya abinda a ka nuna ba zai gamsar da bayyana nadamarsa ba.
2. An samu kutsen hotuna har sau 2 a gurare daban-daban.

Karkarewa
Fim din Abbas fim ne da ya samu aiki mai kyau kuma ya yi nasarar isar da muhimman sakonni a cikinsa. Ba a samu kurakurai masu yawa a cikin fim dinba.
Reactions
Close Menu