Kannywood: Sharhin Fim Ɗin ‘Budurwar Wawa’ Na Kamfanin A.A Kabuga Production
 1. Suna: Budurwar Wawa
 2. Tsara Labari: Abba Harara
 3. Kamfani: A. A Kabuga Production
 4. Shiryawa: Hamisu Eng.
 5. Umarni: Abdulhamid Abdulkadir (Dan Jummai)
 6. Jarumai: Ado Gwanja, Maryam Yahya, Ahmad Tage, Hajara Usman, Zakiyya Lawan, Tijjani Asase da sauransu.
 7. Sharhi: Hamza Gambo Umar

 8. Budewa:
 9. A farkon fim din an fara da waka, yayin da daga bisani kuma aka nuna Kamalu (Ado Gwanja) zai fita daga gida sai mahaifiyar shi (Hajara Usman) ta dakatar dashi saboda ganin ya sanya ‘yar aikin gidan ta dafa masa abinci kuma tun bai ci abincin ba zai fita, anan ne Kamalu ya sanar da mahaifiyar tasa ya fasa cin abincin a waje zai je ya nema. Haka mahaifiyar sa ta dawo tana fama da shi a kan ta na son yayi aure, sai dai kuma Kamalu ya nuna sam ba aure bane a gaban sa.

 10. Yayin da a bangare guda kuma wani magidanci wato Kallo (Ahmad Tage) ya kasance mutum wanda ba ya wadata iyalan sa da abubuwan da suke bukata, sai dai ya fita wajen matan banza yana kashe musu kudi suna holewa, acan ne ya hadu da wata jarababbiyar mace Zee (Teema Makamashi) wadda ta kasance tana da tsananin son abin duniya, hakan ne yasa a koda yaushe takan yiwa Kallo karyar tana da bukatar kudi kuma ko bai yi niyya ba haka zata sa ya caje jikin sa har sai ta debi duk kudaden dake jikin sa dakyar take bar masa dan kudin da zai ci abinci.

 11. Sai dai kuma a duk lokacin da Jallo ya koma gida ko kudin cefane yana kyashin ya baiwa iyalan sa, haka ma ‘yar sa Budurwa Binta wadda take karatu baya bata kudin makaranta idan mahaifiyar Binta ta matsa da tambayar sa kudin makarantar yarinyar sai dai ya nuna Binta ta hakura da zuwa makarantar, amma jin hakan ba ya sa mahaifiyar Binta ta amince da bukatar sa, gashi kuma sam yaki amincewa ‘yar tasa ta tsaya hira da kowane da namiji wanda yazo da nufin yana son ta saboda yana tsoron kada a yiwa ‘yar tasa abinda yake yiwa ‘ya’yan wasu.

 12. Hakan yasa Kallo ko saurayi yaga yazo wajen ‘yar sa Binta da duka yake korar sa, yayin da daga bisani wata rana yaje wajen karuwar sa Zee sai ya tarar da wani kato a dakin ta wanda a kullum yazo idan ya ga katon sai Zee ta nuna ai kanin ta ne, har daga baya dai Jallo ya soma korafi akan yawan ganin katon a dakin ta, dalilin hakan yasa da ta bukaci wasu kudi masu yawa a hannun sa sai ya nuna mata taje ta dauko mayafi suje banki don ciro kudin, jin hakan yasa ta tafi tana murna sai bayan ta dauko mayafin ne ta tarar Jallo ya gudu, takaicin hakan ne kuma yasa itama ta sanar da gardin da ta ajiye a daki akan lallai itama ta gaji da ciyar da shi domin sanadin sa ne ya jawo tsohon da take samu a jikin sa ya guje ta.

 13. Shi kuwa Jallo a sanadin yawon bin ‘ya’yan mutane da yake ne watarana ‘yar sa Binta ta gan sa yazo wajen kawarta, tun daga wannan lokacin kunya ta kama sa, musamman da Binta ta soma bawa mahaifiyar ta labarin halayen mahaifin ta, hakan yasa ko zama ya kasa yi a wajen su.

 14. Shi kuwa Kamalu (Ado Gwanja) tun bayan haduwar sa da wata budurwa me suna Halima (Maryam Yahya) sai yaji ya kamu da son ta, duk da kasancewar ita dai Halima labarin dukiyar da mahaifin Kamalu ya mutu ya bar masa ce tasa tazo ta shiga rayuwar sa, har ma ta amince da karbi soyayyar sa, da nufin bayan aure zata sace dukiyar sa ta gudu.

 15. Sai dai kuma bayan auren da dan lokaci wata rana da daddare Halima tayi nasarar sace jakar kudin Kamalu ta gudu, a bisa tsautsayi wasu matasa suka kwace jakar, takaicin hakan ne yasa tana tafe bata kula ba mota ta buge ta, anan ne tayi madama ta dawo neman gafarar Kamalu amma sai mahaifiyar sa ta bukaci ya sauwake mata igiyoyin auren sa dake kan Halimar, saboda dama sun kula da halayen ta kuma sune suka tura matasa aka kwace jakar da ta sace, anan fa Kamalu ya saki Halima suka koreta daga cikin gidan.

 16. Abubuwan Birgewa:
 17. 1- Labarin ya nishadantar da me kallo.
 18. 2- Sauti ya fita radau, hoto ma ba laifi.
 19. 3- Jaruman sun yi kokari wajen nuna bajintar su.

 20. Kurakurai:
 21. 1- Wakar da aka yi a farkon fim din sam bata da alaka da labarin fim din haka kuma a wajen wakar babu jaruman da suka taka rawa a cikin fim din.

 22. 2- Kwatsam sai ganin Halima (Maryam Yahya) akayi a gidan Kamalu (Ado Gwanja) a matsayin matar sa, alhalin ba’a nuna wa me kallo wata alama ta cewar sun yi aure ba, ya dace ko a rubuce ne a rubuta bayan auren Halima da Kamalu, yin hakan sai yafi gamsar da me kallo sakon da ake son a isar masa.

 23. 3- Shin ina mahaifiyar Kamalu take bayan auren sa? (Hajara Usman) tunda an nuna cewar a gida daya suke ya dace a cigaba da ganin ta musamman a inda Halima da Kamalu suka fito daga cikin daki saboda motsin wani abu da sukaji, ya dace ihun su yasa ta fito amma har suka gama tabarar su a gidan ba’a sake nuna ta ba sai a karshen fim din.

 24. 4- An nuna wata mahaukaciya wadda Halima (Maryam Yahya) taje wajen ta tana nuna tausayin ta akan ta, amma sai mahaukaciyar ta nuna ita ba hauka take ba akwai dalilin da yasa ta mayar da kanta haka, kuma daga baya zata bawa Halima labarin ta, sai dai kuma har fim din ya kare ba’a sake nuna mahaukaciyar ba, shin daraktan ya mance da itane ko kuma dama bata da wata alaka da labarin?

 25. 5- A karshen fim din an nuna Gambo (Zakiyya Lawan) kawar Halima a daya daga cikin wadanda aka hada baki dasu wajen tona asirin Halima, sai dai kuma ba’a bayyana dalilin da yasa Gambo ta yiwa kawar tata haka ba, domin itace ta bawa Halima shawarar auren Kamalu don su mallaku dukiyar sa, ya dace a nuna dalilin da yasa Gambo taci amanar Halima, ko kuma a bayyana ribar da ta samu sanadin aikata hakan.

 26. Karkarewa:
 27. Fim din ya nishadantar, kuma an nuna illar cin amana gami da illar budurwar zuciya ta wasu dattijan mutanen, sai dai kuma akwai abubuwan ba’a karkare ba da kuma wasu abubuwan da ya dace a kara inganta su. Wallahu a’alamu!
Reactions
Close Menu