SHIN AREWA NE SUKA FI KO'INA MUSULUNCI A DUNIYA? (2)

29 Nuwamba, 2019

Muttaka A. Hassan 


Cigaban kashi na (1)

A haka na karɓo jaririyar tana ta ihu, ni kuma hannuna na ta karkarwa kasancewar ban iya ɗaukar jarirai ba musamman idan ina tsaye.


Gefe na koma na zauna tare da zaunar da yarinyar a kan cinyoyina. Can a gefe kuma abarba ce ta warwatsu a kan titi sakamakon buguwar da motocin biyu suka yi, motar da ta ɗauko abarbar mutane biyu ne a ciki; dire da mai zaman banza (waɗanda ban tsammaci suna da rai ba) saboda yadda motar ta yi raga-raga ba ko kyan gani. 

Wasu matasa ne daga cikin mutanenmu na arewa suka doshi motar tare da ɓalla ƙofar da ƙyar, suka zaro mutane biyun da jikinsu yi ya yi kaca-kaca da jini, ɗaya daga cikinsu wanda nake tsammanin shi ne direba, shi ne yake motsi sai dai Allah ne kaɗai ya san adadin karayar da ke jikinsa don ko da aka ɗauko shi ƙafarsa ma lilo take tamkar ta riga ta rabu da jikinsa. 

Sosai na yaba da kyawawan ɗabi'u da tausayi tare da taimako da musulmai suka nuna a wannan lokaci, saɓanin kiristicin ciki da suka koma gefe suna ta iface-iface cikin rashin nutsuwa. Sai a lokacin na fara tunanin ta yiwu jaririyar ma da na karɓo hankalin mutanenmu ne ba ya wurin, suna kan ceto rayuwar mutane biyun da suke cikin jini shi ya sa ba su biyo ta kanta ba.


Bayan wasu mintuna  sai ga mahaifiyar ta samu nasarar fitowa a guje, ta kuwa yaye cinyoyi a gaban al'umma tare da sakin fitsari a tsaye. Kodayake dai tana cikin tashin hankali ne, amma na yi mamakin wannan rashin kunya. Da ta gama sai ta fara neman inda nake, ta zo ta karɓi ɗiyarta tare da kwararo min addu'o'i cikin harshen Nasara, na yi ta amsawa da ameen, sauran kiristicin kuma na taya ni amsawa da emeen.


To da wannan tunanin a zuciyata na ce 'Lallai kunya da kafiri sun yi hannun riga.' Na dawo na kwanta barci ya ƙara ɗauke ni, ina ta tsammanin jin kiran sallah, shiru. Da na farka sai na iske har shida na safe ta kusa. Na shiga bayan gida na ɗauro alwala, na tayar da sallah sai na ji matar gidan na sanar da ni ba gabas nake kalla ba, a hakan na juya na fuskanci alƙibla.


(Daga hagu) Muttaka A. Hassan tare da Ayuba Muhammad Danzaki


Bayan mun karya kumallo aka zo da mota muka zuba kayan aikinmu direba ya ja muka tafi. Lokacin da muka je wurin da za mu yi aikin nan ma dai kusan duka magina da masu tayel da masu saka tagogi da ƙofa da sauran ma'aikatan gidan duka kiristoci ne, idan an cire mutane uku waɗanda mutanen Jihar Jigawa ne wato; Saddiq, Jaafar da Usman. 

Ba mu daɗe tare da su ba suka kammala aikinsu suka nufo gida arewa suka bar ni a tsakiyar kafirai, kwanaki huɗu muka yi tare, amma a cikin waɗannan kwanakin na fahimci abubuwa da dama, wato Sadiq da Jaafar ba sa yin sallahr azuhur sai biyu ta yi, yayinda Usman yake ganin sallahrsu ma ba karɓuwa take yi ba matsawar ba za su yi ƙarfe ɗaya saura ko ɗaya daidai ba. 

Haka nan kullum idan suka zauna cikin ƙalubalantar aƙidun juna suke yi, wani abin takaici kuma duka su ukun suna zama lafiya tare da kiristicin gidan ba tare da wata sa'insa ba balle har su ƙalubalanci addininsu, wanda duk musulmi (kowace ɗariƙa/ƙungiya yake) ya yi imanin kiristanci ɓata ne fiye da kowace ɗariƙa/ƙungiya cikin a musulunci. 

Har wa yau dukkansu babu wanda ya ga kiristocin nan na ta ƙalubalantar ɗariƙa/ƙungiyar juna duk da cewa suna da bambanci a ƙungiyoyi, hana rantsuwa ranar da muka zo gidan, Lahadi, wasu mutane (mata da maza) sun zo ɗauke da wasu takardu inda suka bi kiristocin gidan suka ba wa kowa. 

Bayan sun tafi na ji Samuel na cewa Patrick, "Wannan mutanen suna da matsala." To da wannan ne na matsa na tambaye shi ko wace matsala ke gare su? A nan ya sanar da ni  'yan ɗariƙar 'Deeper Life' ne, kuma su inda kowane kirista ke samun matsala da su shi ne; suna da yawan buɗe makarantu da rubuce-rubuce, kusan kodayaushe cikin gayyatar al'umma suke wurin taronsu, amma su idan ɗan wata ɗariƙa ya gayyace su ba za su zo ba saboda su a ganinsu su kaɗai ne a kan daidai, kowa a kan ɓata yake.


To da wannan bayani na Emmanuel da kuma lura da na yi duk da wannan matsala ta mabiya ɗariƙar Deeper Life ba su zo sun zauna suna ƙalubalantar juna da ƙoƙarin cire juna daga kiristanci ba kamar yadda Jaafar, Sadiq da Usman ke yi ba, sai na ji lallai akwai buƙatar na nusar da su rashin alfanun wannan muhawarar da suke yi a kullum, don haka na samu Usman wanda nake ganin aƙidarmu ta zo kusan iri ɗaya, kamar zai fi saurin fahimtata. Ashe ban san sabon shafin matsala zan buɗe ba.


Za mu ci gaba a kashi na biyu kuma na ƙarshe in shaa Allahu.


Muttaka A. Hassan
Reactions
Close Menu