SHIN AREWA NE SUKA FI KO'INA MUSULUNCI A DUNIYA? (1)

29 Nuwamba, 2019
Muttaka A. Hassan (Abu Ahmad) matashi ne mai jini a jika kuma yana daga daga cikin fitattun matubuta labarai na harshen Hausa dake zaune a jihar Kano. Ba a rubuce-rubuce kawai matashin ya tsaya ba ya kasance gogaggen manazarcin labarai, masharhanci kan al'amuran yau da kullum kuma mai fafatukar raya harkokin adabi da harshen Hausa.

SHIMFIƊA

Ranar wata Juma'a a shekarar 2018 harkar sana'ata (P.O.P Ceiling) ta ɗauke mu ta kai mu PortHarcout, Jihar Rivers. Mu biyar muka tafi daga Kano wato; Patrick, Emmanuel, Isaac da Samuel sai ni cikon na biyar, kamar yadda sunayensu ya nuna dukkansu kiristoci ne, sai dai hakan bai hana mun tafi muna hira cikin raha ba.


 Mun sauka a Owerri, inda nan ma muka ɗauki wasu mutane biyu 'yan ƙasar Togo (na manta sunayensu) ɗaya dogo yayin da ɗayan gajere, duk da kasancewa da daddare ne amma na fahimci su ɗin ma ba musulmai ba ne, hakan ya sa tafiya ta zama mu bakwai amma ni kaɗai ne musulmi.


Lokacin da muka sauka a PortHarcout, aka kai mu gidan da za mu kwana kafin gari ya waye mu je inda za mu yi aiki, sai ya kasance gidan sun yi wasu baƙi mace da namiji dattijai, sai 'yanmata biyu (ina tsammanin dattijan iyayen mijin ne, 'yanmatan kuma ƙannensa) saboda haka aka ba wa iyayen ɗaki ɗaya daga cikin ɗakuna biyu da gidan ya mallaka. 

Har na je na yi alwala na gabatar da salloli muka yi wanka tare da cin abinci ina ta nazarin inda za mu kwanta, da inda 'yanmata biyun za su kwanta. 

A daidai lokacin ne kuma maigidan da matar gidan suka fita, bayan kamar minti goma sai ga su sun dawo da su uku kowannensu ɗauke da babbar katifa. Aka ajiye katifu uku a tsakiyar falo; ni da Patrick (wanda na zo garin sanadinsa) muka kwanta a kan katifa ɗaya, su ma mutane biyun da muka ɗauko daga Owerri suka kwanta a kan katifa ɗaya, yayin da ragowar katifa ɗaya Emmenuel, Isaac da Samuel suka kwanta a kai. 

Su kuma 'yanmatan sai na ga kowacce ta hau doguwar kujera ta kwanta abinta. Mamaki ya wanku raɗau a zuciyata, a raina na ce 'Lallai yau na zo ƙasar kafirai' ina ta mamakin yadda aka gauraya ƙarti bakwai da 'yanmata biyu a cikin ɗaki (falo) ɗaya aka rufe ƙofofi aka kashe wuta.  

Tsakiyar dare na farka na lalubi wayata sai na iske ƙarfe 3:30am daidai, na nufi bayan gida. Ko da na je ƙofar banɗaki na yi addu'ar da addini ya koyar, sai na tura ƙofa, ga mamakina sai na iske ɗaya daga cikin 'yanmatan nan a ciki, cikin wani yanayi da faɗarsa zai iya zama rashin kunya, na yi saurin ja da baya har ta kammala uzurinta ta fito ni kuma na shiga na rufe ƙofa, ina dai ta mamaki musamman yadda na ga ko gezau ba ta yi ba. 

Hakan ya sa na tuno ranar da muka taho motarmu ta yi karo da wata motar inda ta fara hayaƙi aka rikice a kan motar za ta iya kamawa da wuta; wasu suka riƙa fasa gilashin doguwar motar (luxerious) suna fita ta taga, wasu suka fita ta sama, waɗanda ba su samu damar fita ba suka yi ta kiran Jesus, yayin da cikin mutanenmu na arewa wasu suna addu'o'i a zuciya wasu kuma suna narko ashariya. 

Ina daga cikin waɗanda suka samu nasarar fita da wuri, inda wata Inyamura tana kuka tana miƙo ɗiyarta (jaririya) ta taga a kan a taimaka a karɓar mata ita, kowa ya ƙi saurararta wataƙila saboda ana tsoron dosar motar da aka yi imanin za ta iya kamawa da wuta a kodayaushe, da na tuno da mahaifiyata da kuma irin tashin hankalin da za ta shiga idan ta samu labarin mun yi hatsari, sai na ji tausayin Inyamurar nan ya kama ni, musamman da na lura ita ta hakura da rayuwa burinta kurum ɗiyarta ta rayu. 

Sai na doshi motar a zuciyata ina ta nanata 'Innalillahi...' Daga can nesa na jiyo Patrick na min ihun kada na kuskura na je. 
Reactions
Close Menu