Yadda Farfesa Bogoro Ya Zama Limamin Raya Makarantun Gaba Da Sakandare

29 Nuwamba, 2019Shahararren masanin nan dan asalin kasar Amurka, John Mason ya taba cewa; “Wadanda za su iya, suna aikatawa ne. Wadanda ba za su iya ba kuwa, sai su buge da korafi.” Wannan zance na Mason yana nuni ne da cewa mutane masu hazaka suna da wata dabi’a iri daya, ana yawan kalubalantarsu. Yadda ka ke fuskantar wannan kalubale ne ke nuna jajircewarka.

Wannan na daya daga cikin abubuwan da suka sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo da Farfesa Suleiman Elias Bogoro a matsayin Shugaban Hukumar TETFund a ranar 21 ga watan Afirilun 2019. Wanda hakan ya sa aka yi ta san barka, domin mutane na ganin, Farfesan mutum ne da zai farfado da martabar bunkasawa da inganta makarantun gaba da sakandare.

Shugaba Buhari ya dauki matakin dawo da Farfesa Bogoro kan mukaminsa ne sakamakon fahimtar da shugaban yayi na cewa, mutum ne da zai dawo da martabar makarantun gaba da sakandare, kuma wanda zai iya tafiyar da hukumar TETFund yadda ya dace. Ai kuwa, saboda kwarewarsa da jajircewa, Farfesa Bogoro na ci gaba da nuna bajinta a wannan hukuma, ta yadda hatta makiya da magautansa sun fara shan kunya.

Daya daga cikin abubuwan da ake yabon Farfesa Bogoro da su akwai batun cewa, yana taimakon Shugaban Kasa Buhari a yaki da cin hanci da rashawan da yake yi. Ta yadda sunansa a yanzu yana daga cikin jami’an gwamnati na farko wadanda ke fada da rashawa. Har ta kai yanzu Hukumar TETFund ta cimma nasarorin bunkasa makarantun gaba da sakandare, ta dau nauyin horas da malamai a ciki da wajen Nijeriya a dan wannan kankanin lokaci na shugabancin Bogoro. A wannan rubutun za mu dan waiwaiyi kadan daga ciki domin yin bahasi.

An assasa Hukumar TETFund ne, wacce sunanta na farko shi ne ‘Education Trust Fund’ (ETF) a shekarar 1998, wanda a shekarar 2011 aka sauyawa suna zuwa ‘Tertiary Education Trust Fund’ (TETFund). Hukumar ce wacce aka kafata domin samar da tallafi ga makarantun gaba da sakandare. Babban makasudin wannan hukuma shi ne yin amfani da kudin da take da su wurin yin gyara, farfadowa da kuma daidaita makarantun gaba da sakandare a Nijeriya.

A ranar farko bayan dawowarsa ofis, Farfesa Bogoro ya sanar da ma’aikatan hukumar ta TETFund cewa wannan dawo da shi da aka yi bakin aiki a hukumar, wata dama ce da aka ba shi wacce zai yi amfani da ita wurin ganin ya kafa tarihi a hukumar, ta yadda za ta zama abar kwatance a Nijeriya.

Ya sanar da su cewa; “Ina yi wa Allah godiya da wannan damar da aka ba ni na sake shugabantar wannan hukuma. Sannan kuma ban san irin godiyar da zan yi shugaban Kasa ba kan wannan dama da ya bani. Na dau alwashin cewa, zan yi aiki tukuru sai inda karfina ya kare.” In ji shi

A kokarin cimma burinsa na horas da malaman makarantun gaba da sakandare, TETFund ta samar da wani tsari na horas da wadannan malamai a cikin gida da wajen Nijeriya. Wannan tsarin wanda aka yi wa take da ‘Academic Staff Training and Debelopment (AST&D)’ ya zuwa yanzu ana da malamai 24,194 suna karo ilimi a manyan jami’o’in da ke wajen kasar nan.

A wata zantawa da Farfesa Bogoro ya yi da wadannan malamai, ya shaida musu cewa; “Hukumar TETFund ba za ta kawar da kai ga damuwowin malaman da ke karatu ba, wanda wannan ne dalilin da ya sa na fara yawon zuwa kasashe don duba halin da malaman suke ciki a wuraren karatunsu.”

Jami’o’I da sauran makarantun gaba da sakandare sun tsunduma a murna yayin da suka riski labarin dawo da Farfesa Bogoro kan kujerarsa. Wanda ya zuwa yanzu, Hukumar TETFund ta dawo da martabar da aka santa da shi.

Aikin raya makarantun gaba da sakandaren Hukumar TETFund a karkashin Farfesa Bogoro ya zagaye ko ina a fadin Nijeriya. Misali mu duba Arewa masu yamma a matsayin zakaran gwajin dafi. Duk da matsalar tsaro da yankin ke fama da shi, a shekarunsa uku a Hukumar TETFund, Farfesa Bogoro ya yi gine-gine muhimmai a Jami’ar Modibbo Adama dake Yola.

Haka kuma ya yi aikin gine-ginen dakunan karatu dalibai masu diban mutum 250 a Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Mubi, ciki kuwa har da ofisoshin malamai. Haka ma a Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta Idris Alooma dake Geidam Jihar Yobe an gina musu sashe sukutum na kimiyyar kere-kere.

Sannan a Kwalejin Ilimi ta tarayya dake Azare Jihar Bauchi, Hukumar TETFund ta gina dakin kwanan dalibai mata, dakunan karatu. A Jami’ar Maiduguri kuwa Hukumar TETFund ta gina sashen hukumar gudanarwa ‘Senate Building’, gidajen manyan malamai, fadada kai wutar lantarki, gina burtsate guda tara, manyan motoci guda biyu da dai sauransu.

Haka ita ma Jami’ar ATBU ta samu tagomashin sanya mata injin janareto guda uku, biyu masu karfin 800KVA, biyu masu karfin 500KVA, biyu masu karfin 100KVA domin amfanin jami’ar. Sannan kuma Hukumar TETFund din ta gyara dakunan kwanan dalibai da ofisoshin malamai.

A Jami’ar Jihar Taraba kuwa Hukumar TETFund ta yi gine-gine ciki har da kayan asibiti da motoci. Haka ma Jami’ar Tarayya ta Wukari dake Jihar Taraba ta samu tagomashin ayyuka daga Hukumar TETFund.
Wannan ne ya sa ake ta tururuwar sa albarka ga Farfesa Bogoro saboda irin namijin kokarin da yake yi.
– Gidado shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-Tsare Na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).
Reactions
Close Menu