2019: Ali Jita ya lashe kambun gwarzon mawaka na bana

09 Disamba, 2019


Daga Musaddam Idriss

Biyo bayan bikin nuna fasaha da kuma karrama ma'abota fikira a fannonin rayuwa daban-daban da suka hada da bangaren wakoki, kwalliya, kunshi, zane da sauransu wanda kamfanin mujallar Tozali suke gudanarwa mai suna "Henna and Balls Awards Nights". A wannan karon mawaki Ali Jita ne ya samu nasarar lashe kambun gwarzon mawaka na wannan shekara inda aka ba shi kambun girmamawa a daren gudanar da taron wanda ya wakana a ranar Asabar.

Yayin da yake jawabin nuna farin cikinsa bisa nasarar da ya samu, Mujallar ADABI ta ruwaito kalaman mawakin inda yake bayyana cewa, "na ji dadi sosai. Wannan yana daga jerin manyan kambunan da aka taba shiryawa a arewa. Ina alfahari bisa kasantuwa akan abinda na tsaya kuma insha Allah zan cigaba da sanya ku yin alfahari da ni."Tuni dai sauran mawaka abokansa irinsu Nazifi Asnanic suka taya shi murnar samun wannan nasara a shafukan su na sada zumunta inda bayan nuna farincikin sa Nazifin ya dora da cewa, "ka cancanci haka".
Reactions
Close Menu