Jarumai matan da suka fi yin tashe a BollywoodDaga Musaddam Idriss Musa

Kamar yadda aka saba fitar da jerin jaruman da taurarin su suka fi na sauran haskawa a masana'antar shirya fina-finai na kasar Indiya wato Bollywood,  jerin sunayen jaruman na bana na dauke da zakwakuran jarumai mata da taurarinsu suka haska a cikin wannan shekarar saboda bajintar da suka nuna.
1. Jaruma Taapsee Pannu ta sanu wajen iya fitowa a fim inda take taka rawa a fannin abubuwa na musamman. A shekarar 2017 ta fito a wani wasan kwaikwayo mai suna Judwaa 2 a matsayin wadda take da burin koyon fiyano. Kana kuma ta fito a matsayin mai ilimin kimiyar duniyar wata a fim Mission Mangal. 
2. Jaruma Yami Gautam mai shekaru 30 ne a duniya. Ta fara tashe tun wani fim din barkwancin da tayi mai suna Vicky Donor. A yanzu haka jarumar tana kan daukar wani sabon shirin mai suna Ginny weds Sunny wanda darakta Puneet Khanna yake bada umarni.3. Jaruma ta biyu wato Kriti Sanon ta fara haska duniyar Bollywood ne bayan daukarta a fim din barkwanci wanda darakta Sabbir Khan ya bada umarni a shekarar 2014 mai suna Heropanti. Fim din da jarumar mai shekaru 29 ta fito a baya-bayan nan shi ne Housefull 4.
4. Ta uku a jerin jaruman dake tashe a masana'antar Bannywood ita ce jaruma Kiara Advani wadda fim din ta mai suna Fugly da ya fito a shekarar 2014 ya zamo silar da tauraruwarta ta haska. Kwanannan ta fito a wani zazzafan fim na Kabir Singh wanda ya kasance daya daga fina-finan da ake rububin kallon su.
5. A shekarar 2011, Parineeti Chopra ta zamo jaruma ta musamman da fim dinta na soyayya mai suna Ladies vs Ricky Bahl, inda har ta kai ga lashe kambun gwarzuwar jaruma a Filmfare Award. Kwanan bayan nan ta fito a wani fim din tmai suna Jabariya Jodi.
6. Sara Ali Khan ta samu daukakarta ne bayan fitowarta a fina-finan Kedarnath da kuma Simmba wanda suka fita a shekarar 2018. Dukka fim biyun sun yi kasuwa kwarai kuma ta silar Simmba ta samu kambun gwarzuwar jarumai mata na wancan shekara. Sara ta kasance 'ya ga fitattun jaruman Bollywood din nan Saif Ali Khan da Amrita Singh sannan kuma ta bangaren uba jika ce ga Mansoor Ali Khan Pataudi da Sharmila Tagore.
Reactions
Close Menu