Abubuwa 15 da suka fi daukar hankula a Kannywood cikin shekarar 2019

Daga Amina Idriss Musa, 31/12/2019


A wannan shekarar mai karewa, Abubuwa da dama sun faru a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood inda wasun su suka jawo cece-kuce, wasu kuma suka jawo yabo ga masana'antar da jaruman ta.
Ga dai jerin fitattun abubuwan da suka fi daukar hankali cikin masana'antar kamar haka:
1. Rikicin Hadiza Gabon da Amina Amal
A watan Afrilu ne aka wayi gari da sabon lamarin ce-ce-ku-ce a Kannywood, kan batun alakar jaruma Hadiza Gabon da Amina Amal, inda Gabon ke zargin Amal na yada cewa "suna madigo tare."
Wani sako da matashiya Amal ta wallafa ne ya fara tayar da kura, duk da cewa ba ta ambaci sunan Hadiza a sakon ba, amma ba a jima ba ta fara mayar da martani.
Abin dai ya karade shafukan sada zumunta da janyo zazzafar muhara, bayan bullar wani bidiyo da Hadizar ta dinga kwada wa Amal mari, sannan tana maganganu cikin harshen Fulatanci.
Bidiyon ya janyo ana batun maka Hadiza Gabon gaban shari'a dan bin kadin dalilinta ''na cin zarafin Amal'' kamar yadda aka gani a bidiyon.

2. Ali Nuhu ya Maka Adam Zango a Kotu
Na farko dai shine yadda rashin jituwa a tsakanin fitattun jaruman farfajiyar fina-finan Hausa, Ali Nuhu da Adam Zango ya kai kololuwa a shekarar 2019.
A wannan shekara gaba dayan su suka shata wa juna iyaka da yakai ga har suna ambatar sunayen juna sannan har ma Ali Nuhu ya maka Adam Zango a Kotu.
Hakan ya kai ga Adam Zango yayi sallama da Kannywood inda ya ce zai garzaya ya bude tasa farfajiyar fina-finan sannan ya zargi Ali Nuhu da zuga yaran sa a farfajiyar su rika yi masa rashin kun ya.
Sai da manya suka shiga cikin maganar sannan Ali Nuhu ya janye wannan kara da ya shigar a kotu.

3. Cewar Adam A. Zango na yafi kowane Bahaushe suna A Duniya.
Adam A. Zango a watan Afrilu na shekarar 2019 ya fito inda ya bayyana cewa yafi kowane Bahaushe Suna a Duniya inda wannan magana ta jawo cecekuce sosai akai ta magana akai. Wasu ain rika dauko Su Dangote da Sarkin Kano da shugaban kasa, Muhammadu Buhari suna auna wannan magana ta Adam A. Zango dasu.
Saidai daga Baya adamun ya fito yace me hankali be kamata ya hadashi da wadancan manyan mutane ba idan yayi wannan magana.

4. Tir da shigar Rahama Sadau a bikin zagayowar ranar Haihuwarta – Maisana’a
Jim kadan bayan ragargajewa da akayi wajen bukin zagayowar ranar haihuwar jaruma Rahama Sadau a garin Kaduna wasu daga cikin mutane har da abokan aikin ta suka rika sukar irin shigar da tayi a wajen wannan party.
Rahama ta yi shigar bariki, cikin jar doguwar riga, guiwowinta a waje sannan ta rika rangwada rawa abinta babu kakkauta.
Jarumi Maisana’a ya fito karara yana sukar wannan shiga da Rahama ta yi sannan ya gargade ta da kada ta kuskura ta zo garin Kano da irin wannan biki.

5. Kicimewar Zaharaddeen Sani da Ummi Zeezee
A shekarar 2019 ne aka kicime tsakanin jarumi Zaharadden Sani da Ummi Zee Zee in da ta zargi Zaharaddeen da yin sama da fadi da kudaden alfarma da Atiku Abubakar ya rabawa Jaruman Kannywood.
Zeezee ta zargi Zaharaddeen, Sani Danja, Al’amin Buhari da laifin wawushe kudaden jyauta da aka basu su raba a lokacin kamfrn din zaben 2019 inda suka aika mata da wanda bai isa ta saka kati a waya ba.
Sannan ta yi musu kurin duk sai ta daure su a kurkuku badin an bata hakuri ba.
Zaharaddeen ya fusata, inda ya shigar da kara a caji ofis sannan ‘yan sanda suka fantsama neman ta kamar yadda Zaharaddeen ya ne mi a yi.
Tuni dai Zeezee ta ari na kare ta cika wa wandonta iska. Ba a samu dai an kai ga kamata ba har aka yi sulhu.

6. Barin APC zuwa PDP da Adam A. Zango yayi.
A watan Fabrairun shekarar nan ne Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango da yake tafiyar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bari ya koma tafiyar Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar inda ya zargi rashin adalci da nunamasa Godiya a APC duk da cewa ya kashe miliyoyi wajan tallata jam'iyyar.
Wannan lamari ya dauki hankula sosai.

7. Saka kaya masu nuna surar jiki da Fati Washa ta yi
A cikin shekarar nan ne dai tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Washa ta saka wasu hotunanta da suka jawo cece-kuce sosai saboda nuna shacin kirjinta da suka yi. Wannan lamari ya dauki hankula sosai inda akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.

8. Ficewar Adam A Zango daga masana'antar Kannywood
A ranar 15 ga watan Agusta ne fitaccen dan fim din Hausar nan Adam A Zango ya fito karara ya bayyana ficewarsa daga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood.
Zango ya bayyana cewa rashin adalci da kazafi da kage da bita-da-kullin da ake yi a harkar ne suka tilasta ma sa daukar matakin.
Sai dai ya ce a yanzu zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
A watan Satumba kuma Adam Zango ya karyata wani 'malami' da ya yi ikirarin cewa jarumin yana neman mata 'yan kasa da shekara 20 da zummar tantance su domin ya sanya su a wani sabon fim dinsa.
Sannan a Oktoba kuma Adam Zango ya sanar cewa ya biya kudin karatun wasu dalibai na shekara uku, inda ya kashe fiye da naira miliyan 46.
Sai dai batun ya jawo ce-ce ku-ce inda mutane da dama suka yi ta karyata lamarin, yayin da wasu kuma suka gaskata tare da jinjina wa kokarinsa.
Ya sake wallafa wani sako a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana cewa a yanzu ya samar da hanyar da zai rinka fitar da sabbin fina-finansa ta intanet, inda masu kallo za su je su siya kuma su kalla. Ba a dauki lokaci ba sai Adam A Zango ya sanar da yin hijra daga arewacin Najeriya zuwa birnin Legas domin 'tsira da lafiyarsa'.
A Disamba ne kuma dai Adam ya sanar da yin hijirarsa daga arewaci zuwa kudancin Najeriya "domin tsira da lafiyarsa."

9. Garkame Sunusi Oscar a gidan yari
A watan Agusta kuma hukumar ta ce fina-finai ta jihar Kano ta kama mai bayar da umarni Sunusi Oscar, kan zargin aikata ba daidai ba.
Wannan kamu da aka yi wa Oscar ya tayar da kura a Kannywood, inda 'yan fim kamar Sani Danja, da Mustapha na Baraska, da sauran abokan aikinsa suka kaddamar da wani gangami a shafin instagram da ke kiran a saki Oscar.
Ranar 16 ga watan ne dai kuma aka sake shi.
10. An kama Naziru Sarkin waka
A wata Satumba ne aka kama fitaccen mawakin nan Naziru Ahmad, wanda shi ne sarkin wakar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
An tuhumi Naziru ne kan wasu wakoki da ya yi kusan shekaru hudu da suka gabata, wato wakar Gidan Sarauta da Sai Hakuri.
Daga baya a watan ne kuma aka sake shi.

10. Tuban Hadiza Gabon bisa kakkausan martanin da ta yi
A watan Nuwamba ne Hadiza Gabon ta roki gafarar Allah a shafinta na Twitter, bayan da aka yi musu ca ita da kawayenta Rahama Sadau da Fati Washa kan wallafa wani hoto da suka yi a shafukan sada zumunta.
Rahama Sadau ce ta wallafa hoton a Twitter inda ta yi masa take da "ma ki gani ya kau da idonsa".
Sun dauki hoton ne a birnin Landan, lokacin da suka raka jaruma Fati Washa karbar kambun tauraruwar taurari a harkar fina-finan Hausa.
Sun sha caccaka sakamakon sanya hoton inda aka dinga yi musu zargi iri-iri na zina da madigo, abin da ya tunzura Gabon mayar da "kakkausan martanin" ga wani Bala Boyi.
Ba a jima ba ta yi saurin janye martanin da ta maida wa Bala Boyi da cewa "Astaghfirul Laah kan martanin da na mayar marar kyau kan wata amsar rashin da'a da wani ya ba ni. Na goge sakon kuma na nemi gafarar Allah kan kokarin mayar da martani cikin fushi kan wani kuskuren da aka yi."
Wannan ''abin kunya'' ya rikide ya koma na yabo ga tauraruwa Hadiza, inda fitaccen malamin addinin Musulunci kuma ministan sadarwa a Najeriya Sheikh Isa Ali Pantami ya yaba da abin da ta yi.

11. Rasuwar Hajiya Binta kofar soro
Rai bakon duniya, a 2019 an tabo 'yan fim da mutuwar abokiyar aikinsu Hajiya Binta Kofar Soro, wadda ta rasu ranar Asabar, 4 ga watan Mayu a garin Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa, kafin rasuwarta ta yi fama da gajeriyar rashin lafiya.
Kafin rasuwar tauraruwar, ta wallafa a shafinta na Instagram inda ta bukaci al'ummar Musulmi da su yafe mata duk wanda ta yi wa laifi da wanda ba ta yi masa ba.

12. Karrama Ali Nuhu a Indiya
A watan Oktoba ne wasu dalibai 'yan Arewacin Najeriya da ke karatu a kasar Indiya da malamansu Indiyawa suka gayyaci tauraron fina-finan Kannywood Ali Nuhu bikin Ranar Al'adu kuma suka karrama shi a wajen taron.
Jarumin ya ce baya ga wadannan dalibai, wasu makarantu a kasar sun ba shi lambobin yabo, cikinsu akwai makarantar Dayananda Sagar School of Physiotherapy su ma sun ba shi lambar yabo kuma sun nuna jin dadinsu kan yadda daliban Najeriya ke mayar da hankali kan karatunsu.
Ali Nuhu ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan karramawa da kuma yadda malaman wadannan makarantu ke da sha'awar al'adun Hausawa.

13. Fati Washa ta zama tauraruwar fina-finan Hausa a Birtaniya
Fitacciyar 'yar fim din Hausa Fatima Abdullahi da ake kira Fati Washa ta ci kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a wani kasaitaccen bikin fina-finan Afirka da aka gudanar a Birtaniya a watan Nuwamba.
An sanar da Washa ne a matsayin gwarzuwar jaruma a taron karrama 'yan fim da aka gudanar a birnin Landan.
Fati Washa ta ci kyautar ne saboda rawar da ta taka a fim din 'Sadauki,' kuma ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a fim din da ta fito "Jamila" da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a "Uwar Gulma."

14. Rasuwar Mahaifin Hafsat Idriss (Barauniya)
A wannan shekarar ne mahaifin tauraruwar fina-finan Hausa, Hafsat Idris ya rasu inda wajan sanar da rasuwar a shafinta ta saka hotonshi da suka dauka tare. Hoton ya jawo cece-kuce inda wasu suka yi zargin cewa ta dauki hoto da gawar mahaifinta.
Daga baya Hafsat ta cire hoton inda tace tun mahaifinta na da rai suka dauki hoton ba da gawarshine ta dauki hoton ba.
Reactions
Close Menu