ALAN Waka ya zama Sarkin Wakar Sarkin Dutse


Daga Musaddam Idriss MusaShagalin bikin nadin sarautar da aka yi wa shahararren mawakin nan kana kuma tsohon marubucin Hausa, Alhaji Aminuddeen Ladan Abubakar wanda aka fi sani da lakabin ALAN WAKA a matsayin sarkin wakar mai martaba sarkin Dutse dake jihar Jigawa a safiyar yau Asabar na cigaba da wakana.

Taron nadin wanda aka gudanar a cikin fadar mai martaba sarkin Dutse ya samu halartar daruruwan jama'a daga ciki da ma wajen jihar ta jigawa. Inda baya ga masu sarautun gargajiyar da kuma al'ummar gari mahalartan da suka samu damar zuwa nadin, wadanda suka halartan sun hada da tsofin fitattun marubuta, mawaka da masu wasannin kwaikwayo da suka hada da Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON, Malam Kabir Yusuf Anka, Malam Ayuba Muhammad Danzaki da sauransu.Wannan nadi da aka yiwa Alan wakan dai ya biyo bayan nadin da mai martaba sarkin Bichi ya yi masa ne a matsayin Dan Amanar Bichi watanni kadan da suka shude. 

Mutane da dama na ganin cewa tuntuni matsayin na Alan Waka ya kai ace ya samu makamanciyar wannan sarauta duba da yadda yake hidima gami da bautawa harshen Hausa ba dare ba rana. Wasun ma suna da ra'ayin cewa girma da kuma shuhurar mawakin ta kai mizanin da ya cancanci sarkin wakar Hausa na nahiyar Afirka ma baki daya.

Karni na ashirin da daya dai ya bude wani sabon shafi a kundin rayuwar mawakan Hausa duba da yadda suke dada samun kusanci da sarakuna da kuma masarautun da suke kasan su. Idan ba a manta ba mai martaba sarkin Kano a watannin baya can da suka shude ya yiwa mawaki Nazir M. Ahmad nadin sarautar sarkin wakar sarkin Kano inda kuma a yanzu Alhaji Aminu Alan waka ya zamo mutum na biyu da ya samu irin wannan sarauta daga masarautar Dutse.

Fatan Mujallar ADABI ga Alhaji Aminu shi ne Allah ya kara daukaka ya kuma taya riko.
Reactions
Close Menu