An bayyana sakamakon gasar Bakandamiya

8 Disamba, 2019Sannan marubucin nan na yanar gizo kuma marubucin littafin ‘Abin Sirri Ne’ wato Kamal Muhammad Lawan, dan asalin jahar Niger, wanda aka fi sani da Kamala Minna shi ne ya lashe gasar gajerin labari a matakin farko, gasar da manhajar nan mai burin bunkasa rubutun Hausa wato BAKANDAMIYA ta sanya. Kamala Minna dai fasihin marubuci ne da jin sunansa a matsayin wanda ya yi nasarar bai ba wa kowa mamaki ba, musamman ma dai wadanda suke bin rubuce-rubucensa a kafafan sadarwa na zamani. Kamala Minna ya samu wannan nasara ne da labarinsa mai suna ‘Nakasar Zuci’.

Wakilin Mujallar ADABI Musaddam Idriss Musa, ya zanta da gwarzon gasar Kamala Minna inda ya tamabaye shi da cewa: “Shin ko ya ka samu kanka da ka ji wai kai ne da wannan gagarumar nasarar?” “A gaskiya lokacin da aka kira aka sanar da ni cewar ni ne na lashe gasar jin abun na yi kamar cikin mafarki ba a zahiri ba, don safiya ne a lokacin sai na yi zaton kawai barcin safe ya yi mani dadi ne har ya kwaso mani batun cewa na yi nasara game da gasar wacce ko kadan ban taba kawo wa raina cewa zan yi nasara ba.”

“To dama ba ka taba shiga gasar rubutaccen labari ba?”

“Ba wannan ce ta farko ba, na taba shiga gasar gajerun labarai a watannin baya inda nayi nasara na zo a na 1 bayan wannan ban taba shiga gasa ba sai wannan ka ga kenan sau biyu ina shiga gasa kuma Allah ya taimaka ina yin nasara a mataki na farko.”

“Labarinka Nakasar Zuci, idan mun kalli nasarar da ya samu za mu ce lallai ya rubutu.

To shin kowanne irin salo ka yi amfani wajen rubuta shi?”

“Da farko dai zan ce maka nasara ce daga Allah ba wai ya fi sauran labaran da suka shiga gasar ba. Amma ana hawa hangen salon labarin Nakasar zuci da har ya kai ga nasara ya ta’allka ne ga rayuwar ‘ya mace yadda ake cin zarafin ‘ya’ya mata da keta musu haddi sannan a wani sashin ya tabo yadda wasu masu raunin zuciya suke nakasta rayuwarsu ta hanyar kin neman na kai su zauna suna faɗin sai Allah ya kawo.”

Hazikar marubuciya Kurratul’ayn Salees, ‘yar asalin jahar Kano daga Arewacin Najeriya, ita ce wacce sakamakon gasar ya bayyana sunanta a matsayin wacce ta lashe gasar a matsayin ta Biyu da labarinta mai suna ‘Jini Ba Ya Maganin Kishirwa’.


Marubuciya Kurratul’ayn sananniya ce a marubutan yanar gizo, musamman ma ga masu ta’ammali da zauren ‘MARUBUTA’ na manhajar whatsaap. Kurratul’ayn a tattaunawarta da wakilinmu cewa ta yi: “Ba zan iya misalta halin farin cikin da na tsinci kaina ciki ba, domin ko kusa ko da wasa ban taba tunanin zan zamo daya daga cikin wadannan zakarun gasar ba, amma da yake komai nufi ne na Allah sai gashi na samu, gaskiya na ji dadi sosai kuma na yi godiya ga Allah matuka.

Don ban taba shiga gasa ba wannan ce farko, sai dai a duk gasar da na gani ina da burin shiga amma wasu abubuwa suke kange ni, sai wannan Allah ya nufa. Shi ya sa nake kira ga yan uwana matasan marubuta, su dage su kuma daure sosai wajen cire tsoro da fargabar shiga ko wacce irin gasa, domin Bahaushe ya ce DA RARRAFE YARO KAN TASHI, tun kana shiga kana zuwa last wata rana hakanka zai cimma ruwa ka taka matsayin da baka yi zato ba bare tsammani. Allah (S.W.A) da kansa ya ce da bawansa tashi in taimake ka.”

Aisha A. Fulani gwana marubuciya ‘yar asalin Gusau dake jahar Zamfara, ita ce aka ayyana sunan a matsayin ta Uku a wannan gasa ta Bakandamiya da labarinta mai suna ‘Ma’aurata’. Da take zantawa da wakilinmu ta shaida masa cewa: “Na yi farin ciki wanda ba zai misaltu ba, saboda sosai labarin ya taba zucuyata, wai Aisha ce ta zo na Uku a wannan gasa. Sai na godewa Ubangiji wanda shi ne ya ba ni nasara ba wai iyawata ba.” Da wakilin namu ya tambaye ta ko me za ta ce game da manhajar ta Bakandamiya da suka sa wannan gasa?

Sai ta amsa da cewa: “Ina mai masu fatan alkhairi Ubangiji Allah ya saka masu da alkhairi Allah ya sa su fi hakan alfarmar Annabi S.A.W. kuma Allah ya cika musu buri ya karfafe su kan lamuran alkhairi da suka sa gaba.”

Mukhtar Musa Karami (Abu Hisham) shi ne jagoran sanya wannan gasa, da muka tamabaye shi ko me ne manufarsu ta sanya wannan gasa sai ya amsa da cewa: “Manufofi ne na musamman wanda kai tsaye za mu iya cewa don kishin adabinmu na hausa muka shirya wannan gasa, sannan kuma muna so hausawanmu su kara ganewa shigar da zamananci cikin harkar adabi yana taimakawa wajen karin yaduwarsa a duniya. Sannan abu na gaba ita wannan Manhaja ta BAKANDAMIYA an yi ta ne ta Hausa zalla wacce mutum zai shiga ya karanta duk wasu littattafanmu na Hausa musamman na karatun adabi, sannan akwai wani bangare na koyon wasu abubuwa irinsu zamantakewarmu ta hausawa da kuma koyon girki duk a zamanance. Manufa ta gaba shi ne don marubutanmu da manazarta su kara sanin wannan kafa ta BAKANDAMIYA inda ko babu komai wayewar zamani za ta shiga tunanin marubutanmu da yawa, yanda muma zamu zamo wadanda ake damawa da mu a duniyar rubutu.”

To wadanne matakai kuka bi wajen alkalancin wannan gasa?

Mataki ne mai sauki wanda kusan abin a bayyane yake, tun a sanarwa fara gasar mun rubuta cewa wanda ya fi kowa samun comments shi ne ya yi nasara, abin nufi idan mutum ya je yayi sing up a Manhajar www.Bakandamiya.com ya shigar da labarinsa to adadin mutanen da suka yabawa labarinsa koda kuwa ta hanyar suka ne ko gyara duk za mu tattara mu ga wanda ya fi yawa ta hakan muka zabi na Daya da na Biyu har zuwa na Uku.

To Mujallar ADABI na taya wadannan hazikan marubuta murna da du’a’in Allah ya kara basira da daukaka Ameen.

Reactions
Close Menu