Bauchi, Borno sun tashi a gaban Marubutan Yobe

Daga Amina Idriss Musa, Potiskum
27/12/2019
Sakamakon gasar da ta gabata wanda kungiyar marubutan shiyyar kudancin jihar Yobe da hedikwatanta take garin Potiskum wato POWA ta fitar ya bayyana cewa  Alhassan Beli wanda ya kasance marubuci dan jihar Bauchi shi ne ya zo na daya, yayin da kuma Muhammad Bala Garba da shi kuma ya kasance dan jihar Borno yake a matsayin na biyu sai kuma Aminullahi da ya zo na uku, Hussaini Muhammad kuma na hudu a gasar wadda jigonta ya kasance akan BUTULCI.

Gasar ta POWA din dai ana yinta ne a kowane karshen wata inda hakan ya kasance wani yunkuri da kungiyar tayi don samar da hanyar buga kundi na gajerun labarai wanda kungiyar za ta dauki nauyin bugawa kamar yadda shugaban kungiyar Musaddam Idriss Musa ya bayyana, "wannan wani mataki ne da muka dauka don samar da labaran da zamu buga a matsayin kundin farko na gajerun labarai karkashin wannan kungiyar tamu kana kuma mataki ne musamman da muka ga ya dace mu samar da shi don bada kofa a marubutan da basu da halin buga littafi domin su samu hanyar da labaransu zasu shiga cikin kundin yadda a kalla za suna alfaharin cewa ai su ma a littafi kaza idan aka bude akwai labari kaza nasu ne ga kuma sunan su a rubuce..."Tuni dai masoya suka shiga aikawa zakarun gasar sakonnin fatan alheri bisa nasarorin da suka samu kuma ana sa ran a yammacin yau za a bayyana jigon gasar wannan wata da muke ciki.
Reactions
Close Menu