Bollywood: Jaruma Mona Singh ta yi aure

Daga Musaddam Idriss Musa, 31/12/2019

Karshen shekarar 2019 ya zamo tamkar kakar bukukuwan jaruman fina-finai ne a kasar Indiya, inda biyo bayan auren taurarin da suka hada da Mohena Kumari Singh, Ruhi Chaturvedi, Karan Goddwani da kuma Sonyaa Ayodhya a kwanakin bayan nan, ita ma jaruma Mona Singh ta shiga sahun jarumai matan da suka amarce din a ranar juma'ar da ta gabata.

Jaruma Mona din wadda tayi shigar amarcinta cikin jan lufaya (Sari) ta yi shuhura ne bisa rawar da ta taka a fim din 'Jassi Jaissi Koi Nahin', ta samu damar cika burinta na auren tsohon sarauyin da take so mai suna Shyam wanda rahotanni suka bayyana a matsayin ma'aikacin banki.


Reactions
Close Menu