Cin Abinci Ba Nama Yana Taimakon Muhalli – Bincike

8 Disamba, 2019


Bincike ya tabbatar da cewar kamfanoni masu samar da nama sun dauki kamar kashi 18 zuwa 51 daga cikin kamfanoni masu gurbata muhalli, wato human-made pollution wanda da gangan ne mutum yake samar da shi. Kungiyar Earthsab ta tabbatar da cewar kafin a sarrafa pound daya na naman hamburger sai an amayar da 75kg na iska mai guba na CO2. Saboda haka idan aka duba kenan irin barnar da kamfanoni da suke sarrafa nama ke yi wa muhalli ya ma fi kamfanonin sufuri (transportation company) da kuma sauran masana’antun kere-kere.Cin abinci na tsarin began zalla na karawa mutum walwalaBincike ya nuna cewar mutane da ke bin tsarin began diet sun fi kasancewa cikin walwala da kuma koshin lafiya, wato a healthier mood state. Wannan na nuni da cewar suna da kariya mai yawa ke nan, daga bakin ciki da kuma damuwa, ga kuma yawan fushi, da kuma fatigue da dai sauran makamantansu. Abin mamakin shi ne shi cin abinci da ake kira da plant-based food yana karawa mutum walwalar ne sabodo da suna dauke da antiodidants masu yawan gaske.
Yana sa mutum ya kasance cikin kuruciyaAbinci na tsarin began na karawa mutum yarinta wato ya kasance yana da gwabi- gwabi, domin suna gyarawa mutum fatarsa da kuma gashi saboda yawan minerals da kuma bitamins da antiodidant da ke cike cikin ire-iren abincin. Wannan kenan a maimakon kashe makudan kudi wajen gyaran jiki da sayen makudan kanti wadda yawanci ma, ba wani inganci ne da su ba, me zai sa ba za a koma cin shi wannan plant-based food din ba? Sun fi arha, da kuma ba su da wani hadari ko kadan ga lafiya.


Daga karshe , za a iya cewar tabbas cin abinci na tsarin began yana da matukar amfani  wanda ba a iya misaltawa. Abubuwa kamar yadda zai kare muhalli daga fidda iska mai guba da kamfanonin sarrafa nama ke yi har izuwa yadda ya ke kare mutane daga samun cututtuka irin su kansa, sannan kuma zai taimaka wajen karawa mutum kuruciya.


Reactions
Close Menu