Daga sanya waka a waya na zama dillalin sayar da waya – Buhari Na-Malam

06 Disamba, 2019


Alhaji Buhari Na-Malam

Daya daga cikin manyan ’yan kasuwa masu sayar da wayoyin hannu a Sakkwato, Alhaji Buhari Na-Malam ya ce daga sanya wakoki a wayoyi ne ya fara harkar sayar da waya har ya zama dillalin wayoyin.

Alhaji Buhari Na-Malam wanda shi ne shugaban shagunan Welcome to China Communication da ke Sakkwato. ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce bayan rasuwar mahaifinsa a shekarar 2008, lokacin yana aji biyu a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato, sai ya yanke shawarar fara harkar tura wakoki daga kwamfuta zuwa ga wayoyin hannu don ya samu ya ci gaba da karatu. Kuma daga haka ne ya zama dillali a harkar sayar da waya ta yadda ta kai a yanzu babu wata kasa da ake kera wayar salula da ba ya zuwa ya saro wayoyin a can.

“Da na fara harkar tura waka da kwamfuta a wayoyin mutane tun babu bulutut da Zender , sai abu ya karbu na hada Naira dubu 80 na je Legas na sayo kayan waya, bayan wata shida na sayar da su, ina shirin komawa lokacin wayoyin China sun fito ina da sama da Naira dubu 400, nan na yanke shawarar komawa sayar da wayoyin. Na fara na ga abu yana bunkasa sai na bar harkar kayan wayoyi na koma sayar da wayoyi,” inji shi.

Ya ce a yanzu yana da matasa 31 da ke aiki a shagunansa na waya wadansu ana biyansu albashi wadansu kuwa ana biyansu kaso kan abin da suka sayar.

Ya ce “Matasa su kara tunani kan dogaro da kansu. Idan ka yi karatu ka yi sana’a; don a yanzu da karatuna nake amfani cikin kasuwancina domin da Kwamfuta muke aiki, na bunkasa sana’ata da ita, ina da digiri a fannin Physics ina karantarwa a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Umaru Shinkafi a nan Sakkwato. Son jiki da kasala ke lalata rayuwar mutum har ya shiga lamarin bakin ciki. Ina kira ga matasanmu musamman Hausawa da suka fi masu zaman banza a kasar nan, su tashi tsaye su jingine haka, su fahimci mai zaman banza fa ba ya cikin talaka da har zai yi korafin gwamnati ba ta aiki. Mai zaman banza shi batagari ne. Addininmu ya hana zaman banza kuma shi ke sa mutum ya zo yana zagin shugabanninsa,’’ inji Na-Malam.

Da yake magana kan kalubalen kasuwancin ya ce: “A Najeriya kasuwanci yana da wahala, ga rashin tsaro, hanyoyi ba kyau, bankuna na da matsalar sadarwa. Ga mutanenmu ba su da gaskiya su ci bashi su ki biya wadannan abubuwa ne ke kawo wa kasuwanci wahala sosai.”

“Akwai lokacin da na sayo kaya, jarina bai da karfi kayan Naira miliyan bakwai na sanyo aka dauko su da mota kirar J5 har sun kawo garin Dange kadan ya rage a shigo birnin Sakkwato motar ta bugi rami, nan take ta kama da wuta, aka kira ni na zo a gabana motar ta cinye tare da wayoyina kurmus, ban fitar da komai ba, wannan ya faru ne sanadiyar rashin kyan hanya. Ga matsalar sadarwa ta bankuna sai ka sayi kaya rashin sadarwa tsakanin bankuna ya hana ka biya ka yi hasarar ribar da za ka samu. Wani ya karbi bashinka kuma ya ki biya,” inji shi.

Ya ce sai dai ya samu nasara sai godiyar Allah. Domin kuwa ya yi gida ya yi wa wadansu, ga wadansu na cin abinci a karkashinsa. Ya yi kira ga jama’a su rika rainon sana’a ko kasuwanci, su cire tunanin da mutum ya fara yanzu kawai zai bunkasa. Ya ce kasuwanci da sana’a suna bukatar abu uku; mutum ya zama marar kasala ya zama mai lissafi kuma ya zama mai hakurin zama har ya samu masaya.

“Ni ina son taimakon matasa kan duk wani abu da za su yi na dogaro da kansu, ba domin addinina yana son a taimaki wanda ba ya da shi. Matasa 11 da muka tura su samu horo a kwallon kafa in sun samu nasara za mu sake ganin yiwuwar tura wadansu da ikon Allah,” inji Buhari Na-Malam.
Reactions
Close Menu