GURBATATTU DAGA KABILAR IBO NA CUTAR DA MUDaga Mohammed Bala Garba, Maiduguri.

Najeriya kasa ce mai al’adu da addinai da ma kabilu daban-daban da suka haura 200. Manya a cikinsu su ne Hausa, Ibo da Yarbanci, kuma kowannensu na da tsarin yadda yake tafiyar da mulkin jama’arsa.
Bayan da aka raba kasar zuwa yankuna uku, wato Hausawa da Fulani da sauran kabilunsu a Arewa, Ibo da nasu kabilun a Gabas, Yarbawa da nasu a yankin Yamma, sai Arewa ta fi kowane yankin yawa da girma, abin da sauran yankunan suka yi ta kokawa a kai.
A shekarun 1940 zuwa 1950 jam’iyyun da aka kafa domin yakin kwatar wa Najeriya ’yancin kai su ne NPC a Arewa da NCNC ta kabilar Ibo da AG ta Yarbawa, duk sun yi gwagarmaya musamman NCNC da AG wadanda ke neman a ba su ’yancin cin gashin kai, abin da suka ga zai yi wuya ba tare da hada kai da Arewa ba.
Hakan ne ya sa jam’iyyun uku suka yi ta gwagwarmayar tare, a karshe hakarsu ta cimma ruwa.
A ranar da za a bai wa Najeriya ’yancin kai, wato ranar 1 ga Oktoban 1960, Turawan mulkin mallaka na Ingila sun mika tutar ’yancin kan ne a hannu Firayi Minista, Sa Abubakar Tafawa Balewa wanda dan Arewa ne kuma Musulmi, yayin da Dokta Nnamdi Azikiwe, Kirista dan kabilar Ibo ke matsayin Shugaban Kasa.
Tun daga wancan lokaci sauran kabilun musamman Ibo ba su ji dadin lamarin ba, cewa ’yan Arewa ne ke mulkarsu, kuma wannan ne ya haifar da juyin mulki na farko da sojoji wadanda akasarinsu ’yan kabilar Ibo ne suka yi a 1966 a karkashin jagorancin Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu, inda aka kashe manyan shugabannin Arewa farar hula da soja,a karshe aka nada dan kabilar Ibo, Janar Johnson Aguiyi Ironsi a matsayin Shugaban Kasa.
Kananan hafsoshin soja ’yan kabilar Ibo, sun yi ikirarin cewa sun yi juyin mulkin ne saboda a cewarsu, shugabannin da ke jagorancin kasar sun nuna zarmiya, inda suka ce ministocin gwamnati suna sace kudaden baitu-mali domin amfanin kansu.
Sai dai kuma a wani bangare, akwai masu ikirarin cewa wannan juyin mulki na kabilanci ne, saboda daga cikin sojoji 8 da suka kulla juyin mulkin, bakwai ’yan kabilar Ibo ne, daya ne kawai Bayarbe. A gefe guda kuma dukkan shugabannin farar hula da aka kashe da manyan hafsoshin sojoji kasar, kusan duk ’yan Arewa ne.
Wadanda aka kashe a juyin mulkin sun hada da Sa Abubakar Tafawa Balewa, Firayi Ministan Najeriya da Firimiyan Arewa, Sa Ahmadu Bello sai Firimiyan Yamma Samuel Akintola da Ministan Kudi Festus Okotie-Eboh (wanda shi kadai ne dan kabilar Ibo da aka kashe) da Ahmed Ben Musa da Birgediya Zakariya Maimalari da Birgediya Samuel Ademulegun da Kanar Kur Mohammed da Kanar Shodeinde da Laftana Kanar Abogo largema da Laftana Kanar James Pam da Laftana Kanar Arthur Unegbe. Sai Saje Daramola Oyegoke da ya taimaka wa Nzeogwu wajen kai hari kan gidan Sardauna, amma a cewar ’yan sanda daga baya Nzeogwu ya kashe shi.
Kisan su Sardauna ya yi wa sojojin Arewa zafi don haka a ranar 28 ga Yulin 1966, wata shida bayan wancan juyin mulki, hafsoshin soja daga Arewa suka shirya nasu juyin mulkin, wanda ya kai ga kashe Janar Aguiyi Ironsi tare da Laftana Kanar Adekunle Fajuyi.
Wadanda suka shirya wannan juyin mulki su ne, Laftana Kanar Murtala Mohammed da Laftana Kanar Joseph Akahan da Manjo T.Y. Danjuma da sauran kananan hafsoshin sojojin Arewa, cikinsu har da Laftana Ibrahim Badamasi Babangida.
Juyin mulkin ya haifar da takaddama a tsakanin Kanar Odumegwu Ojukwu da Shugaban Mulkin Soja Janar Yakubu Gowon, inda a karshe aka kai ga kashe-kashe a tsakanin ’yan kabilar Ibo da al’ummar Arewa da ke zaune a Arewa da Kudu, lamarin da ya tursasa da dama daga suka yi kaura zuwa Kudu maso Gabas da kuma Arewa.
Samun man fetur a yankin Neja-Delta da ke yankin tsohuwar Jihar Kudu maso Gabas ya haddasa fargaba a zukatan kabilar Igbo, cewa gwamnati za ta yi amfani da kudin man domin gina Arewa da Yammacin kasar nan ne kawai, su kuma su zama ’yan kallo.
Wannan da kashe-kashen da suka biyo bayan juyin mulkin farko a Kudu da Arewa da kuma zargin da Ibo ke na cewa an tafka magudi a zabubbukan ’yan majalisa da aka yi a baya da suka bai wa Arewa nasarar kafa gwamnati, ya sa a lokacin Gwamnan Soja a Kudu maso Gabas Kanar Odumegwu Ojukwu ya nemi balle yankinsa daga Najeriya a ranar 30 ga Mayun 1967 domin kafa kasar Biyafara.
Wannan shi ne mafarin Yakin Basasar Najeriya da aka kwashe kimanin shekara uku ana yi, tsakanin kabilar Igbo da ke neman kafa kasarsu da gwamnatin sojin wancan lokaci a karkashin shugabancin Laftana Kanar Yakubu Gowon.
A ranar 6 ga Yulin 1967 ne dakarun Najeriya suka kutsa kai cikin yankin Biafran ta bangaren Arewacin yankin inda suka samu nasarar kwantar da tawayen.
An samu asarar rayukan kananan yara sama da dubu 10, yayin da yunwa ta yi ajalin dubbansu kuma dubbai daga cikinsu suka rasa iyayyensu da muhallinsu da dukiyoyinsu a dalilin wannan yakin. Kimanin fararen hula dubu 180, ne suka rasa rayukansu a yakin.
Sauran kabilun Najeriya ma sun samu kansu cikin jarrabawa babba saboda kasancewar kabilar Ibo na cikinsu, watakila nan gaba kadan wannan jarrabawar tana iya shafar dukkan kabilun duniya kamar yadda wani malamin masanin addinin Musulunci ya fada.
Mu lura da kyau, za mu fahimci cewa kusan duk wani babban sharrin da ke Najeriya, to lallai gurbatattu cikin kabilar Ibo ne suka fara kawo shi kasar nan, har aka samu wasu bangarorin kabilun kasar nan daga baya suka kwaikwayi irin wannan sharrin su ma.
Alal misali:
1. Gurbatattu cikin kabilar Ibo ne suka fara kawo musibar juyin mulki irin na kisan gilla a Najeriya.
2. Su ne suka fara kawo musibar daukar makamai domin wargaza Najeriya da ballewa daga gare ta.
3. Su ne suka fara kawo musibar cin hanci da rashawa cikin ma’aikatu.
4. Su ne suka fara kawo musibar daukar bindigogi da sauran miyagun makamai domin yin fashi da makami.
5. Su ne suka fara kawo musibar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
6. Abu mafi muni daga ciki shi ne, sace ’ya’yan mutane da suke yi daga sauran kabilu domin su sayar da su su samu kudi lamarin da ke jawo su sauya musu addini da kamanni.
Lallai ne a cikin kabilar Ibo akwai mutanen kirki wadanda suke fa’idantar da kawunansu, su ke kuma fa’idantar da al’ummarsu da kuma kasarmu Najeriya, to amma wadancan siffofi na sharri, tushensu daga gare su yake.
A karshen ina rokon Ubangiji Allah Ya kyautata halayyar gurbatattun ’yan kabilar Ibo da dukkan kabilun kasarmu, Ya ba mu lafiya da zaman lafiya a kasarmu, Amin.
Reactions
Close Menu