Gwamna Ganduje yayi shirin kafa tarihi a masana'antar Kannywood

06 Disamba, 2019Gwamnan jihar Kano Alhaji (Dr) Abdullahi Umar Ganduje ya yi shirin kafa sabon tarihi a masana'antar shirya fina-finan Hausa da akewa lakabi da 'Kannywood' biyo bayan yarda da kuma bayyana amincewarsa na kawo taron BON AWARD karo na 10 izuwa jihar Kano tare da daukar nauyin gudanar da shi.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba bayan karbar bakuncin jaruman fim din Kannywood da kuma shugaban BON din ya bayyana cewa a jihar Kano a shirye take da ta karbi bakuncin bikin karrama taurari da jaruman fina-finai na wannan shekara wanda zai gudana a ranar 14 ga watan Disamba, 2019.

Da yake karbar takardar shaidar gabatarwa daga shugaban BON din, Gwamna Ganduje yace, "mun yi farin ciki sosai da ya kasance bikin BON na bana a nan jihar Kano zai kasance kuma wannan wani sabon tarihi ne ga jama'a jihar baki daya."

Daga jerin wadanda suka halarci ziyarar bada shaidar dai akwai Ali Nuhu, Bashir Maishadda, Gbenga Adeyinka, Segun Arinze dasauransu.

Oloketuyi ya bayyana cewa kamfanin mota na Peugeot da kafanin sufurin jirgi na Max Air, da LaCasera a bangaren abin asha sun bada gudummawa wajen samar da kyaututtukan da za a bayar na bana. 

Daga wadanda za a karrama akwai jaruman fim din turanci na Najeriya irinsu Sadiq Daba, Mama Rainbow, da Ngozi Ezeonu. A jaruman fim na Hausa kuwa akwai Maryam Booth kuma dan wasan barkwancin nan Gbenga Adeyinka zai halarci bikin na bana don nishadantarwa.
Reactions
Close Menu