Irin Sinadaran Abincin Da Ake Samu Ta Jikin Dabobbi

8 Disamba, 2019Kungiyar nan da ke ikirarin kare hakkin dabbobi wato, PETA ta tabbatar da cewa animal product kamar su kwai, da nama ko kuma abubuwan da suka shafi madara wato dairy product na dauke da antibiotics, da sinadarai masu guba, da kuma hormones, da kwayoyin cuta na bacteria da dai sauran sinadarai masu guba daban-daban. Wadannan abubuwa kuwa suna iya jawowa dan adam matsalolin lafiya masu tsananin gaske. Kuma bayan hakan, USDA sun tabatar da cewar kashi saba’in na abincin da ya shafi guba food poisoning na faruwa ne a sanadiyar cin naman dabbobi da basu da wani inganci.

A saboda da hakan ne da kuma yadda ake bukatar naman da sauran abinci da ake samu ta hanyar dabbobi, ya kuma sa manoman dabbobin suna amfani d hormone da su antibiotics domin sa su dabobbin girma da wuri. Wannan hanyar na haifar da antibiotic-resistant bacteria ga su dabbobin da kansu wanda hakan na iya haifar da carcinogenic substance (sinadari mai haddasa kansa) kuma daga karshe duk wannan matsalar zata kare ne a jikin dan adam.


Yadda Za Ka Samu Kariya Daga Cutar Sankara Da Dangoginta

Cin abincin began diet na da matukar amfani ga lafiya, domin kuwa cikin nau’oin abincinsu akwai abubuwa wadanda suke kara lafiya da kuma bayar da kariya daga cututtuka masu yawa. Suna da sinadaran da ake kira da suna antiodidants da kuma phytonutrients wadanda ke yaki da samuwar free radicals da ke haddasa lalacewar kwayoyin halitta na cell din da yake jikin dan adam da kuma haifar da inflammation wato matsala wadda ta kan iya shafar lafiyar jiki. Cell deterioration da kuma inflammation kan haifar da cututtuka kamar su kansa da kuma wadanda suke alaka dasu. Bugu da kari kuma bincike ya tabbatar da cewar idan mutum ya mai da hankalin shi akan abincin bda ya fi dace da shi, began diet zai rage hadarin kamuwa daga hawan jini da yawa da ga cututtuka irinsa.Hukumar  lafiya ta duniya, wato World Health Organization, ta tabbatar da cewar naman da ake sarrafawa, wato processed meat , ma’ana irin wannan yana taimakawa wajen kamuwa da cutar  kansa. Hakanan man sun ce jan nama ma watakila na iya haifar da kansa . Sai kuma akawai da yawan bincike da aka gudanar a kafofin bincike na kasashen Turai da su China wanda ya alakanta ciwon kansa da cin abinci da suka fito a jikin dabbobi. Bugu da kari kuma  a ko da yaushe aka ziyarci likitoci su kan bamu shawarwarin an rage cin nama, musamman idan shekaru suka fara ja. Saboda haka cin abinci da ya kunshi zallar tsirrai da ganyaryaki ai ba laifi ba ne, musamman ma idan aka yi la’akari da hadarinda yake tattare da yin hakan.
Reactions
Close Menu