Yadda kama marubuci ya janyo gaba tsakanin China da Australia


Daga Musaddam Idriss MusaA taron ganawa da manema labaran da aka yi da Ministar waje ta kasar Australia Marise Payne wanda ya gudana a ranar Litinin din da ta gabata, ta bayyana damuwarta kan kama marubucin kasar tare kuma da tsare shi da gwamnatin kasar China tayi bisa zargin da ake yi masa na aikata laifin satar bayanai (sirrin) kasa.
     An kama marubucin ne yayin saukarsa cikin garin Guangzhou dake kudancin China bayan ya baro birnin New York na kasar Amurka tare da matarsa, Yuan Xiaoliang da 'yarta agola mai shekaru 14 da take tare da su.
      Marubuci Yang Hengjun ya kasance ruwa-biyu ne daga jinsin Australia da kuma China kuma an tsare shi ne tun watan Janairun wannan shekara bisa zargin satar bayanan kasa
       Payne ta bayyana cewa, "na damu kwarai" bayan ziyarar baya-bayan nan da suka kai wa marubucin kamar yadda suka saba kaiwa kowane wata, a wata sanarwa da ta fito daga ofishin kasar Australia.
        "Yanayin da yake ciki kan wannan kamun da aka yi masa ya kunshi dada nesanta shi da duniyar mutane da kuma jefa shi a cikin kadaici, baya ga takunkumin hana shi magana da iyalansa, abokanai da kuma komawa ga rayuwarsa da ya saba yau da kullum ga kuma tauye hakki," Payne ta bayyana hakan a jawabinta.
        Sai dai kuma a daya bangaren, daga birnin Beijing mai magana da yawun Ministan waje na kasar China, Hua Chunying ta tabbatar da cewa gwamnatin China za ta yiwa marubucin adalci kuma ta fadi cewa wani da ba ta bayyana sunansa cikin jawabin nata, a jerin jami'an tsaron kasar China din ne zai yi duba kan wannan lamari na Yang, "bisa tafarkin doka tare kuma da cikakken tabbaci na kiyaye hakkokin wanda ake zargi."
           "A iya sani na, mutumin da kika ambata a halin da ake yanzu yana halin lafiya. Babu kuma batun ikirarin nuna tirsasawa ko yi masa dole kan amsa wannan laifi," inji Hua.

          Kasar Australia din dai ta sha aikawa da gwamnatin kasar China da bukatar son jin laifin da ake tuhumar marubucin kasarta din wanda ya kai shekara 54 a duniya kamar yadda Payne ta bayyana amma abu ya faskara.
        A jawabinta na mayarwa Hua martani ta karyata ofishin takwaranta na China da cewa, "mun roka masa a lokuta daban-daban da a samar masa da tsayayyar gaskiya da kuma adalci gami da kiyaye martabarsa na dan adam kamar yadda dokokin kasa-da-kasa suka tanadar, wanda suka hada da ba shi damar ganawa da lauyoyinsa da kuma iyalansa, amma duk an ci gaba da yin watsi da hakan an hana shi," inji Payne. 
         "Hakan kuma ya hana kawo wani sauyi na a zo a gani kan managanin da ake masa bayan da aka gano jininsa ya hau kuma kodarsa ba ta aiki daidai"
          Firayim minista Scott Morrison ya nuna rashin amincewarsa kan cewa guda dan kasarsa daga jerin sauran 'yan kasashen wajen da hukumar China ta kama dan leken asiri ne.
          A zantawarsa da manema labarai a Canberra, Morrison ya bayyana cewa, "walwalar kowane dan kasar Australia tana gaba da komai, kuma gwamnati ta damu bisa kasantuwar Yang a gidan kurkuku har na tsawon wani lokaci." 
          "A kodayaushe kasar Australia shirye take don tsayawa 'yan kasarta kuma ya kamata mu zama masu gaskiya ga wadanda muke tare a matsayin mu na mutane." Inji Morrison ya kuma kara da sake jaddada cewa hukumar Australia na bukatar ganin cikakken bayanin tuhumar da ake yiwa Yang tare kuma da janye takunkumin hana shi ganin lauyoyi da kuma iyalansa. Ya kuma dora da cewa gwamnatin Australia za ta kashe makudan kudaden da adadinsu ya kai dala miliyan $59.58 wajen inganta tsaronta daga farmakin kasashen ketare. 
           Duk kuwa da bai ambaci sunan China ba, an san Morrison yana shirin ne saboda sanin karfin da Beijing take da shi a wannan yanki.
Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil-adama dake kasar suka shiga nuna bukatar ganin gwamanatin Australia din ta kara sanyawa Chinan kahon zuka.
Reactions
Close Menu