Kungiyar HAF tayi bikin karrama gwarazan marubuta na shekarar 2019

Daga Musaddam Idriss Musa, 30/12/2019


Hoton wasu daga mahalarta taron karrama zakarun marubutan shekarar 2019


A jiya Lahadi ne kungiyar Inuwar Marubutan Hausa da aka fi sani da Hausa Authors Forum wato 'HAF' a takaice ta gudanar da babban taron da ta saba yi a duk karshen kowace shekara inda take karrama marubutan da suka yi fice bisa zamowar su zakaru a manyan gasannin da wasu kungiyoyin ko hukumomin suka shirya tun daga farko har zuwa karshen shekara.

Taron na bana dai wanda ya gudana a dakin karatu na American corner dake cikin laburaren Murtala a jihar Kano ya kasance zakaran gwajin dafi a baki dayan tarurrukan da suka gabata a bisa samun halartar manyan baki daga kusan kowace kusurwa na jihohin dake fadin Najeriya da suka hada da jihohin Bauchi, Yobe, Kaduna, Katsina, mahalarta daga sassan ciki da ma wajen birnin Kano mai masukin baki da sauransu.

Yayin da yake jawabi kan makasudin taron na bana, shugaban  kungiyar Malam Jamil Haruna Jibeka ya bayyana cewa, "..makasudin shi ne girmamawa da karramawa da kuma sada zumunci..." na daga dalilan da suka sanya su shirya wannan taro baya ga kokarin su na son ganin cewa sun karfafawa marubuta masu tasowa gwiwa tare da yabawa kokarin da su kayi na yin nasara a gasannin da wasu kungiyoyin marubutan suka shirya.

Shugaban ya kuma yin nuni da cewa marubuta baki dayansu 'yan uwan juna ne kamar yadda ya furta cewa, "...idan an sa gasa kin shiga ko mun shiga kin yi nasara ko ka yi nasara, to nasararki din ko nasararka din ta dukka marubuta ce...." inda hakan ya zamo makasudi na samar da shi wannan taro.

Rukunin farko daga jerin rukunnai biyar ns manyan gasannin da suka gabata a wannan shekarar dai wanda a cikinsu ne aka fito da gwarazan marubutan na bana da kungiyar ta HAF karrama a taron shi ne na gwarazan mata guda ukun nan da suka yi nasarar lashe gasar mata wadda BBC Hausa take shiryawa duk shekara wato hikayata wadda ta dayan ita ce Safiyya Ahmad daga garin Zariya na jihar Kaduna, sai mai bi mata Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo daga jihar Kano kana ta ukun kuma takwararta ce wato Jamila Babayo daga jihar Yobe.

Rukuni na biyun kuwa ya kasance na zakarun gasar Kainuwa Authors  Forum (KAF) inda Bukar Mustapha Damaturu tare da Musaddam  Idriss Musa duk daga jihar Yobe tare kuma da Adam Tukur Miyatti daga jihar Kano suka kasance zakarun da aka karrama a wannan rukuni. Sai kuma kashi na ukun wanda ya kasance rukunin zakarun gasar Gusau Institute wanda zakarun suka hada da shugaban kungiyar marubuta ta kasa reshen jihar kano, Malam Zaharaddeen Ibrahim Kalla tare da sauran zakarun gasar. Inda sauran rukunnai biyun suka kasance na gwarazan gasar Bakandamiya da kuma gasar Ga-ni-Ga-ka.

Baya ga wadannan rukunnai kungiyar ta karrama dattawan marubuta wadanda suka ui shuhura wajen ciyar da adabin Hausa gaba tare kuma da tallafawa marubuta masu tasowa inda wadanda aka karrama a wannan rukuni suka hada da Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, Hajiya Balaraba Ramat, Malam Dan Azima Baba, Hajiya Hafsat Azare, Malam Hashim Abdallah, Malam Bala Anas Babinlata da sauran su.

Haka nan kuma, marubutan yanar-gizo ma sun shiga sahun wadanda kungiyar ta karrama saboda kwazon su wanda kuma yin hakan shi ne na farko. Daga cikin wadanda aka karrama din akwai Rufaida Umar, Fauziyya, Xinnee dasauransu.

Manyan bakin da suka samu zuwa wannan taro kuwa sun hada da Malam Ibrahim Indabawa, Malam Ayuba Muhammad Danzaki,  Malam Suleiman SID, Malama Maimuna Idriss Beli, Malam Ibrahim Garba Nayaya, Malam Zahraddeen Nasir, wakilan kamfanin Mujallar ADABI Saifullahi Lawal Imam, Ummi Abiha Tasiu da kuma Editan Mujallar Adabi Musaddam Idriss Musa tare da sauran manyan baki.

Kafin karkare taron dai, an bawa mahalartan damar tofa albarkacin bakin su kan takardu aka gabatar da kuma wakoki da aka karanta kana kuma an bawa marubutan da aka karrama din damar yin jawabai na godiya da nuna jin dadin su kan wannan karramawa da suka samu.
Reactions
Close Menu