Marubuciya Fauziyya ta sake samun kambun karramawa

Daga Amina Idriss Musa


Shugabar gidauniyar tallafawa gajiyayyu kuma shahariyar marubuciyar labarai da kuma fina-finan Hausan nan wato malama Fauziyya D. Suleman wadda ta kafa gidauniyar Creative Helping Needy Foundation ta samu lambar yabo na musamman daga gidauniyar Michelle Care Foundation bisa jajircewarta wajen yin ayyukan taimakawa al'umma tukuru ba dare ba rana.

Malama Fauziyya dai ta dade tana ayyukan taimakon gajiyayyu, majinyata, marayu, da kuma marasa galihu. A halin da ake ciki yanzu tana daga jerin fitattun mata na yankin arewacin Najeriya da suka himmatu wajen taimakon al'umma. 

Baya ga taya murna bisa wannan nasara da ta samu, fatan mu shi ne Allah ya kara mana yawan mutane masu zuciyar son taimakawa irin tata ya kuma saka mata da alheri.
Reactions
Close Menu