Sama da marubuta 600 sun yi zanga-zanga a Indiya


Daga Musaddam Idriss MusaAn wayi gari ne jiya a kasar Indiya da wani gangami na daruruwan masu zanga-zangar nuna kin amincewar su kan sabuwar dokar da za ta baiwa 'yan wajen kasar wadanda ba musulmi ba shaidar zama 'yan kasa.

Ita dai wannan sabuwar doka da gwamnatin kasar take shirin kafawan dai za ta bai wa baki mazauna Indiya wadanda ba 'yan asalin kasar ba shaida ko damar zama 'yan kasa amma ga mabiya addinan da bamusulmunci ba. Kuma tsarin dokar zai shafi baki 'yan kasashe makota dake kusa da kasar ta Indiya ne wato kasashen Bangladesh, Pakistan da kuma Afghanistan wadanda suke zaune a kasar daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Kudurin zartar da wannan dokar dai ya samo asali ne daga ministan cikin gida na kasar Amit Shah wanda ya samu sanyawar hannu yayin zama da majalisar kasar "Lok Sabha" bayan fafata muhawara akai a shekaran jiya Litinin da misalin 12 na dare.

Inda nan take a wayewar garin jiya Talata daruruwan masu zanga-zanga maza da mata da adadinsu ya haura 600 suka fito don nuna rashin amincewa da wannan kuduri na gwamnatin kasar. 

Rukunnai na masu zanga-zangar dai sun hada da manyan marubuta na kasar, manyan mawaka, jaruman fim, malamai, da kuma tsofin alkalai. A jerin wasu fitattu daga manyan marubutan kasar da suka fita wannan zanga-zangar akwai Nayantara Sahgal, Ashok Vajpeyi, Arundhati Roy, Paul Zacharia, Amitav Ghosh da kuma Shashi Deshpande.

Hakanan kuma a bangaren mawaka akwai su TM Krishna, Atul Dodiya, Vivan Sundaram, Sudhir Patwardhan, Gulam mohammed Sheikh da kuma Nilima Sheikh.

A fannin jaruman fina-finai kuwa Aparna Sen, Nandita Das da kuma Anand Patwardhan na daga wadanda suka fito wannan zanga-zangar. Kazalika manyan malamai masana na kasar da suka hada da Romila Thapar, Prabhat Patnaik, Ramachandra Guha, Geeta Kapur, Akeel Bilgrami da Zoya Hasan su ma ba a bar su a baya ba. 'Yan gwagwarmaya da kuma fafutukar siyasa  kamar su Teesta Setalvad, Harsh Mander, Aruna Roy da Bezwada Wilson da ma tsofin alkalai na kasar irinsu Justice AP Shah, Yogendra Yadav, GN Devy, Nandini Sundar da Wajahat Habibullah su ma ba a bar su a baya ba wajen nuna kin jinin wannan mataki na shirin kafa sabuwar dokar wadda karara ta bayyana rashin rangwame ga musulmi kamar yadda daukacin masu zanga-zangar suka bayyana.

Masu zanga-zangar dai sun bayyana cewa, "kundin tsarin mulkin kasar Indiya yayi hani da nuna bambancin jinsi, harshe, matsayi na rayuwa, kabila ko addini", a cewar su wannan sabuwar dokar za ta haifar da wahalhalu ga al'ummar kasar kuma za ta ruguza tsarin kasar baki daya baya ga haifar da rudani,"

"Wannan shi ne dalilin da su da kuma sauran al'ummar kasar suke bukatar gwamnati da tayi watsi da wannan kudurin sabuwar dokar....kada gwamnati ta sabawa dokar kasa."

Jam'iyyun adawa na kasar sun nuna rashin goyon bayan su kan yunkurin dokar da zai bada damar zama dan kasa ta hanyar nuna wariyar addini wanda hakan shi ne karo na farko a tarihin Indiya.

Sai dai a martanin da jam'iyyar BJP mai mulki ta yi ta bayyana cewa, "a cikin wadannan kasashe ukun mabiya addinan Hindu da Buddha da Sikh da Jain da Parsis da kuma Kiristoti suna shan wahala." Inji Amit Shah.
Reactions
Close Menu