Amshi:
Gun shiga kin zarce amare,
Kar ki sa in ta shure-shure.
1 Na fada maki Kar ki mance,
Kar ki yi Mani kauce-kauce,
Sai na zamto abin kwatance,
Ko mutane su gan ni bare.
2 Kar ki yi mani zille-zille ,
Ba ni son ki da tsalle-tsalle,
Kar magauta su min kwalele,
Duk katangu na kinsu ture.
3 Duk kalaman zugarsu jure,
Ba su kaunar su gan mu tare,
Ni da ke so suke mu Ware,
Sai su rinka kiran gwagware.
4 Da kinai mani girke-girke,
Su gurasa tuwo da Buske ,
Sai na ci su kwarai da gaske,
Har ki sanya miya ta sure.
5 Kar ki manta fadar mutane,
Harshe har da hakori manne,
Sai su Saba abin hakan ne,
Har ta kai su da ture-ture.
6 Nai tunanin abinda ke sa,
Gingimemen dutse ya nisa ,
Yau da gobe tana a kansa,
Wataran Sai ki gan shi dare.
7 Kar ki yarda da ce -kucensu,
Aniyarsu kwa za ta bi su,
Ba su samun abin nufinsu,
Sun ki, so za su gan mu tare.
8 Sun fi ganewa zunde-zunde,
In ka ba su na tande-tande,
Sai su ba ka batu a murde,
Kai Ka afka cikin kirare.
9 In kwa kin biyewa batunsu,
Sharrikansu da ke asusu,
Za su bude su tankado su,
Dai da dai za ki gan su Jere.
10 Daga nan kwa Sai sake -sake,
Lamuranmu duka su sarke,
Sai ka ce masu zuke-zuke,
Mui ta Kara kama ya gyare.
11 Sai mu koma da rabe-rabe,
Tsare -tsarenmu sai su kwabe,
In na zo da kure ki karbe,
Mashahuri ya bi darare.
12 Shi tunani yana da tushe,
Hankali ke masa hasashe ,
Duk fushi sai ya zam a karshe,
An yi dace da gyare-gyare.
Nasir Usman Babaye 07033729220
0 Comments