Taurarin Bollywood din da auren su ya mutu a karshen shekarar 2019

Daga Musaddam Idriss Musa, 31/12/2019
Ga taurarin fina-finan Bollywood dai musamman wadanda ke da aure karshen shekarar 2019 da muke yin bankwana da ita a wunin yau ta zo musu ne a baibai a sakamakon mace-macen auren wasu da dama daga cikin su wadanda ake ganin zaman auren bai yi musu dadi ba.
Rukunin jaruman da auren su ya mutu din sun hada da:
1. Jaruma Shweta Tiwari da mijinta jarumi Abhinav Kohli. Shweta wadda ta bayyana sakon mutuwar auren na su a wata hira da ta yi da gidan TV a yanzu haka ta dawo masana'antar ta Bannywood bayan wani tsawon lokaci inda a gaba kadan za a sake ganin fuskarta a cikin wani fim din Sony mai suna 'Mere Dad ki Dulhan'.
A yayin da take sanar da batun rabuwar su din, Shweta din dai ta bayyana cewa ta fuskanci tozarci daga jarumi Abhinav kuma ta cike takardar yin kararsa watanni kadan da suka wuce.   

2. Raqesh Bapat da Ridhi Dogra: mutuwar auren jarumai Raqesh da Ridhi, wanda aka daura auren su a watan Mayun 2011 ta girgiza kowa, bayan da suka fitar da sakon rabuwar ta su a karshen shekarar nan biyo bayan shafe shekaru 7 da yin auren su. Sai dai ko a yanzun da suka rabu suna cigaba da yin abota. Farkon haduwar Raqesh da Ridhi din dai ya kasance wani fim din sony ne mai suna 'Seven' sun kuma fara son juna ne yayin da suke daukar fim din kamfanin Star Plus mai suna 'Maryaada Lekin Kab Tak?'.

3. Shweta Basu Prasad da Rohit Mittal: fina-finan 'Chandra Nandini' da kuma 'Kahani Ghar Ghar Kii' su ne suka fito da jaruma Shweta Basu Prasad har ta yi suna. Jarumar sun yi aure da Rohit Mittal ne ranar 13, ga watan Disamban bara (2018), kuma ta fitar da sakon rabuwarta da mijin nata ne da shi ma ya kasance mashiryin fina-finai a masana'antar kwanaki kadan kafin gudanar da bikin murnar cikar auren su shekara daya.

4. Srishty Rode da Manish Naggdev: Srishty Rode, wadda tayi aure a shekarar da ta gabata bayan fitowarta a cikin shirin gidan talabijin mai suna 'Bigg Boss 12" auren nata da jarumi Manish Naggdev ya mutu tun watan farko na wannan shekara bayan an kore ta daga fitowa a cikin shirin. Ana rade-radin cewa mutuwar auren nata na da nasaba da kusancinta da daya daga jaruman da ke fitowa a shirin na BB 12 Rohit Suchanti kuma har yanzu dai ana alakantata da afkawa cikin soyayya da wani babban dan kasuwa mai suna Vijal.

5. Faisal Khan da kuma Muskaan Kataria: su ma wadannan taurarin ma'auratan sun rabu dukda hadin su ya matukar birge mutane da dama tun bayan sace zukatan 'yan kallo da suka yi a wani fim da suka fito mai suna 'Nach Baliye 9'. Rabuwar ta su dai ta faru ne biyo bayan raunin da Faisal din ya samu bayan gama wani wasa.
Rahotanni sun suna cewa, Muskaan ta datse alakar auren na su ne a daidai gabar da ake bukatar ta da nuna cikar alkawarinta na son da take wa mijin nata inda ta kare da zargin sa na cewa sau biyu yana cin amanarta shi da wata jaruma da suka fito a cikin shirin.
Daga baya dai Faisal ya zargi Muskaan din da yin amfani da shi ne don ta samu daukaka.
Reactions
Close Menu