Ya manhajar Mujallar ADABI take?


Manhajar Mujallar ADABI wato Mujallar ADABI app manhaja ce da aka ginata da harshen Hausa zalla. An yi matukar kokari kwarai wajen kirkira da kuma tsara fasalin siffar wannan manhaja ta yadda duk wanda ya kasance farin shiga a masu amfani da ita ba zai yi bakunta ba. Komai a bayyane yake a fili na daga madannai/zaurukan manhajar (menus), mai amfani da manhajar Mujallar  ADABI app ba shi da bukatar tambayar ko da abu daya ne don farawa/koyon amfani da ita. Bayan haka, akwai alamomin nuni (icons) bayyanannu da suke taimakawa wajen sanar da wadanda ba sa jin Hausa sosai matsayin wajen da suke son shiga. A takaice mai aiki da manhajar Mujallar  ADABI app yana iya kewaya ko'ina na cikinta ya kuma zagaya su acikin kasa da dakika 30 saboda matukar saukinta.

Mene ne sabo a Mujallar ADABI app?
Abu na musamman game da manhajar Mujallar ADABI app shi ne zallar Hausa da aka yi amfani da ita wajen ginawa. Domin sabanin sauran manhajojin da aka saba gani da sunan an gina su da Hausa sai kuma a tarar da Turanci ne ke da kaso mafi rinjaye, Mujallar ADABI app an gina ta ne da akalla kashi 99.9% na harshen Hausa. Saboda haka, idan zamu takaita bayanin kai tsaye muna iya cewa Mujallar ADABI app 'Bahaushiyar manhaja ce'.

Ya fasali/siffar manhajar Mujallar ADABI app yake?
Kamar yadda aka saba gani a sauran manhajoji irinsu Facebook, WhatsApp dss. Da zaran mai amfani da Mujallar ADABI app ya baiwa salularsa damar busawa manhajar numfashi (installing), zai samu manhajar akan teburin na'urar wayar tasa cikin jerin zaurukan dake kan wayar (menu). Zai iya gane manhajar ne ta hanyar tambarin Mujallar ADABI mai dauke da sunan kamfanin da kuma launin farin bango (background) wannan shi ne alamar manhajar (Application icon) a kasa da icon din kuma akwai sunan kamfanin a rubuce baro-baro kamar haka👉 Mujallar ADABI  

A wannan lokacin mai amfani da manhajar yana iya danna kan tambarin (icon) don shiga cikin manhajar inda abu na farko da zai fara bayyana a fuskar salulawayarsa rubutu ne na maraba kamar haka,👉 "Barka Dai! Muna godiya sosai bisa kasancewar ka/ki daga jerin ma'abota amfani da manhajar mu."
A kasa da wannan rubutun kuma akwai inda zaka ga karamin akwati kamar wannan👉🔲 idan ka taba shi kuma layin maki zai fito cikinsa kamar haka 👉✔ Amfaninsa kuwa shi ne dakatar da sake ganin wannan sakon na maraba a duk sa'adda aka sake shiga cikin manhajar idan an fita daga shigan farkon da aka yi din, wato idan ba a so a sake ganin rubutun.
  
Bayan wannan sakon ya dauke, abu na gaba da mai amfani da manhajar Mujallar ADABI app zai gani, shi ne katon hoto na tambarin kamfanin. 
Duba misalin a shafin gaba kamar haka👇Da zaran zagayen nan ya gama juyawa, za a kalli hotunan bangwayen Mujallar ADABI shirye kuma jere a layi bi-da-bi.

Idan tambarin ya dauke zai sake nuno wani farin bangon wanda a samansa akwai alamomi (icons) sannan za a ga wani zagaye yana motsi ta hanyar kewayawa alamar wani abu na shirin budewa (loading). Da zaran zagayen nan ya gama juyawa, za a kalli hotunan bangwayen Mujallar ADABI shirye kuma jere a layi bi-da-bi.

A madannan da suke sama (icons) wanda ratsin wani jan layi ya raba su da hotunan (bangwayen). Na farko daga bangaren hagu ta kusurwar dungu na wayar, wasu layi ne guda uku wani a sama da wani ta jikin su kuma hoton tambarin kamfanin ne. Wannan wajen shi ne babban zauren manhajar (Menu) inda dukkan sauran rassasashe (sub-menus) suke na cikin manhajar suke.

Taba wannan wajen (tambarin) zai bada dama a dukkanin rassan su bayyana inda za a ga sassa kamar haka
• Sashen Hotuna
• Sashen Labarai 
• Ra'ayi/Muhawara
• Shagon Oda
• Sabbin Mujallu
• Shafin Facebook 
• Sashen Tuntuba 
• Game Da Mujallar ADABI 
• Tsarin Amfani Da Manhaja

SASHEN LABARAI
▪ Sashen labarai: reshe ne da ake iya samun dukkan labaran mu da muke dorawa a adireshin yanar-gizo cikin kowace dakika idan aka samu sabbin labarai da dumi-duminsu. Babban sashe ne sosai yana da girma da kuma fadi akwai kuma tarin abubuwa kama daga labaran bidiyo, labaran sauti, hotuna da ma dukkan rahotannin mu kama daga tsofaffi da kuma sabbin rahotanni dss.

SASHEN RA'AYI DA MUHAWARA
▪A wannan sashen ma'abota bibiyar Mujallar ADABI suna da damar tofa albarkacin bakin su akan batutuwan da suke da abin fada akan su. 

Abubuwan da masu amfani da manhajar za su iya yi a wannan sashe sun hada da;
i. Rubuta sakonnin gaishe-gaishe ga 'yan uwa da abokan arziki. Su kuma wakilan mu zasu kwafi sakon tare da dorawa a adireshin mu na yanar-gizo da sauran shafukanmu kai har ma a cikin bugaggiyar Mujallar ADABI duk a kyauta.
ii. Gabatar da wani dogon rubutu na mukala, gajere ko dogon labari, rubutacciyar waka, wasan kwaikwayo, kasida, wa'azi, rubutun fadakarwa, rubutun girke-girke, ko rubutun tarihi/al'adu/masarautu da ma dukkan wani abinda mutum ya so gabatarwa. Ma'aikatan mu za su tantance rubutun tare da wallafa shi idan ya hau mizanin hakan.
iii. Har ila yau sashe ne da Mujallar ADABI ta ware don tafka muhawara akan batutuwan da za tana kawowa jifa-jifa. 
iv. Kana kuma dandali ne da za acigaba da gabatar da gasar waken nan na Mujallar ADABI wato #postchallenge da kuma #voice-challenge kai a yanzu har #videochallenge za a na gabatarwa a wannan sashe.
v. A karshe, baya ga duk wadannan a sashen akwai rukunnai da dama da suka yi daidai da zabira'ayin mutane mabambanta don kowanne ya samu wajen da zai leka yayi shawagi. 

Wannan daya daga cikin sassan fa kenan, kada a manta cewa a manhajar Mujallar ADABI app din fa akwai shagon sayen bugaggiyar  Mujallar ADABIn a ciki, akwai shafin Facebook,  akwai sahen labaran bidiyo zalla, sashen tuntuba kuma kowanne cikinsa dauke yake da wasu muhimman rukunnan. 
Kai! Abubuwan dake dankare a manhajar Mujallar ADABI bayani irin wannan ba zai gamsar da kai ba. Tuntubi lambar mu ta WhatsApp +2349063064582 ko kuma adireshin imel din mu mujallaradabi@yahoo.com don aika bukatar tura maka da manhajar kawai don ka fara aiki da taka yanzu-yanzun nan tare da ganewa idonka komai dake ciki.
Bissalam!
Sa hannu: 
Musaddam Idriss Musa 
Edita, Mujallar ADABI.
Reactions
Close Menu