Yadda masu fassara ke kassara Hausa a zamanin yau - Danladi

Daga Musaddam Idriss Musa, 27/12/2019Kasancewar Hausa harshe ne mai saukin fahimta game da basirar da Allah Ya yi wa harshen wajen aro kalma daga wani harshen ta mayar da ita tamkar ’yar asalin harshenta, ya sa harshen yake bunkasa a dukkan fadin duniya.
A lokacin da duniya ke kwance, duk inda Bahaushe ya je yakan fita zakka, kuma idan sun kai su dubu sai ya samu kulawa ta musamman daga masu ‘Jan kunne’ ko Larabawa. Har yanzu kuwa masu fita kasashen wajen na shaida mana irin daukakar da suke samu alfarmar harshensu da al’adunsu da addininsu.
To amma fa bunkasar Hausar na samun nakasu ta wajen abubuwa da dama. daya daga cikinsu shi ne yadda rubutun Hausa ke cikin tsaka mai wuya. Idan na ce rubutun Hausa, ina nufin rubutun da aka juyar da harufan boko zuwa harufan Hausa, ban san yadda ajami yake ba, wato rubutun Hausa cikin harufan Larabci, watakila shi ma akwai irin wadannan matsaloli da zan zayyano.
Yanzu ya zama cewa duk wanda yake iya fahimtar harshen ko da ta fuskar saye da sayarwa ne, sai kurum ya hau kankambar rubutawa, musamman wanda ke takama da ilimin boko, ba tare da la’akari da ka’idojin rubutu da masana harshen suka shimfida ba. Manyan ’yan bokon da suka fi yi wa rubutun Hausa illa su ne ’yan jarida, musamman masu rubuta tallace-tallace.
Na ci karo da wani katon allon talla a cikin birnin Kano an rubuta: “Mu na a Geyyara da Sayarawa.” Wai fa nufinsu “Muna gyara da sayarwa.” Wani allon kuma na ga an rubuta: “San u o zuwa.” Wai suna nufin: “Sannu da zuwa.” A wani rubutu ma da na gani a jikin wani gwangwanin madara shi ne yadda aka fassara, ‘breastfeeding is best for your baby’ wai sai aka rubuta da Hausa: “kirjin ci mafi alheri gare ku jarirai.”
Hakika wannan ta’addanci ne ake yi wa harshen Hausa, maimakon a dauki kwararren mai fassara kamar yadda ake dauka a wasu harsunan, amma ganin kyashi da azarb ab i da rashin girmama al’umar ya sa ake amfani da fassarar da aka ga dama.
Na biyu masu ta’addaci ga rubutun harshen Hausar, su ne masu gidajen rediyo da talabijin, musamman masu karanta labaru cikin Ingilishi da Hausa. Kasancewata mai sauraren labaran gidajen rediyon da ke birnin Kano, kwanaki cikin sanarwar da Hukumar Tsaron kasa (SSS) ta fitar game da binciken da ta gudanar a gidan tsohon Mai bai wa Shugaban kasa Shawara kan Tsaro, a labaran na Ingilishi sai suka ce: “…high calibre rifles, seb eral magazines and military related gears were found…” A labaran Hausar kuma sai suka ce: “an samu manyan makamai tare mujallar sojoji a gidansa.” Gidan rediyo na biyu kuma suka ce: “a gidan an samu wata mujalla da ke koyar da aikin sojoji tare da wasu manyan bindigogi.” Gidan rediyo na uku kuma suka ce: “…tare da wata mujallar soja ta koyar da yaki a cikinta.” Gaba daya fa sun kasa fahimtar cewa kalmar ‘magazine’ da aka fada a sanarwar, ba tana nufin mujalla ba ce, tana nufin jigidar albarusai, ko wani babban akwati mai dauke da albarusai musamman na bindigar nan mai sarrafa kanta (machine gun).
Wannan ma babbar tab argaza ce, kuma hakika ana cutar da harshen Hausa bisa wannan mummunar fassara da ake yi cikin garaje. Kuma ya zama kamar raina aikin manyan farfesoshi ne da ke hidima ga harshen a kullum, ba dare ba rana. Masu rubutu a zaurukan sada zumunci, musamman facebook da whatsApp da sauransu, suna gigita ka’idojin rubutun Hausa. Nan ne za ka ga rubutu babu wakafi balle aya, babu fasali balle kama, babu fasaha balle ka’ida. Nan ne za ka ga rubutu daga sama zuwa kasa, ko daga kasa zuwa sama kamar na ’yan China. Kuma wai su masu rubutun har buri suke a yi musu tsokaci, ko me za a ce da su? Oho! Ni kam ba na ko kallon rubutun nasu, domin ina gudun kada kwamacalar da ke ciki ta sa ni amai. Da a ce ina da iko, duk wanda na samu da irin wannan baragadar rubutun, sai na ci tararsa gwargwadon b arnar da ya aikata.
Makarantun firamare da sakandare, musamman masu zaman kansu, na taka muhimmiyar rawa wajen lalata rubutun Hausa. Da yawa saboda tsumulmula ta rashin daukar kwararrun malamai kamar yadda suke yi a wasu fannonin, sai su dauki Ngozi ko Chinyere ko Samuel a matsayin wadanda za su koyar da harshen Hausa da rubutun Hausa. Wannan wata mahangurb iya ce da ba ta haifar da da mai ido. A ganina ma ita ce ummulhaba’isin faruwar tab argazojin da na ambata a sama.
Don haka, ina kira ga hukumomin da abin ya shafa su mike tsaye su kara azama wajen kare martabar rubutun Hausa. A sanya doka mai tsanani ga duk wanda aka ga yana rubuta gurb ataccen rubutun Hausa a allunan talla, sannan a inganta hukumomin fassara ta yadda ba kowane karabiti ne ke da lasisin fassara Hausa ba, sai wanda ya ke kwararre.
dalibai kuwa a kara himma wajen nakaltar hawa da saukar rubutun Hausa, ko da ba ita ce abin da kake koyo a makaranta ba, za ta zame maka abin tinkaho duk inda ka je a fadin duniya. kasashen da suka ci gaba dukansu da rubutun harsunan kasarsu suke alfahari. Saboda haka ne ire-irenmu da ba Hausar muke karantawa a makaranta ba, amma saboda ita ce ta haife mu gaba da baya, ya sa muke nuna kishinmu game da ita.
Malamai kuma ya dace su kara nutsawa fagen bincike da kikkiro sababbin hanyoyin nazari da samar da tabbatattun ka’idojin rubutu. Ya kuma dace su shigo harkar zamani, musamman yanar gizo domin su kankare kura-kurai da gangancin da ake yi wa harshen Hausa.
Gwamnati kuwa da yake ita ce sha kundum, rubutun Hausa na bukatar agaji ta hanyar daukar nauyin malamai domin gudanar da bincike da karfafa dokokin da suka jib inci rubutun Hausa tare da inganta hanyoyin koyon rubutun, ta yadda zai zama ya tafi asin-da-asin tare da harshen ta fuskar furuci.
danladi marubuci ne kuma manazarci da ke zaune a Kano, Najeriya.
Reactions
Close Menu