Ba karamin kuskure ba ne hana matar aure yin aiki - Mansura Isah


A wannan tattaunawar tare da Mansura Isah tsohuwar tauraruwa a masana'antar Kannywood kana matar jarumi kuma mawakin zamani Sani Musa Danja wadda daya ce daga jerin matan da suka yi fice wajen fafutukar neman na dogaro da kansu tare da tallafawa jama’a, inda har hakan ya kai ta ga samar da gidauniyar tallafawa mabukata wato Today’s Life Foundation. Tsohuwar jarumar ta bayyana dalilan da suka sa aka ga ta himmatu wajen taba harkokin kasuwanci da sana’o’i daban-daban, inda hakan ce ta sanya muka nemi ji ta bakinta dangane da yadda mace ya kamata ta yi fafutukar neman na kanta a matsayinta na matar aure, ga kuma amsar da muke tafe muku da ita:

M.A: A matsayin ki na matar aure kuma mai iyali da ta tsinci kanta a sahu na matan da ke fafutukar neman na kansu, shin ya matar aure take kasancewa a wajen neman abin da za ta dogara da kanta?
Mansura Isah: To ka san mu a nan yadda rayuwar mu take musamman matan Arewa, daga mace ta yi aure, idan tana aiki sai ta bar aikinta, idan kasuwanci take yi sai ta bari domin tana tunanin duk wata dawainiya tata mijinta ne zai dauke da iyalan da za ta haifa, to amma idan ka duba yadda rayuwar take da yadda Allah yake al’amuransa wani loakcin, ba wai don namijin bai isa bane a wajen kulawa, to, amma idan babu tsufa akwai mutuwa, mun sha ganin miji yana da kudi iyalansa babu abinda suka rasa, amma sai Allah ya dora masa rashin lafiya, har ta kai duk abinda ya mallaka ya kare, daga karshe ya mutu, to a nan sai iyalan su dawo su shiga wani irin yanayi su samu kansu a rayuwa da za a yi ta mamakin irin daular da suke ciki a baya.

To wannan abin mun gani ya faru akan mutanen da muke rayuwa tare da su, don haka ba wai miji na ba zai iya ciyar dani ko kula da mu a matsayin iyalinsa ba ne, amma abin da na lura shi ne dogaro da mutum daya ba Allah ba akwai gajiyawa, kuma dalilin da yasa mutane su ke ta ganin kamar ina zafin nema in bude shago nan da can na yi wannan harkar kasuwancin da sana’a, abu ne da suka faru da yawa a baya wanda suka bude min ido kuma suka koya min darasi.

Domin kasantuwar lokacin da mijina ya yi hadari ya karye a kafa da hannu, kuma a lokacin babu inda ba mu je neman magani ba haka muka rinka daga filaye da sauran wasu kadarori muna ta sayarwa ta hanyar neman magani da addu’a, don ya samu lafiya wannan ya sa mun shiga wani yanayi. Don haka ya zaunar dani bayan ya samu lafiya, ya ke cewa dani yadda rayuwa ta kasance mana, ya kamata ke ma ki samu wani abu da zaki rinka yi a matsayin sana’a domin idan na kwanta ki samu ki dago ni, to wannan dalilin yasa na tashi tsaye kuma shi ma yana taimaka min da jari don ganin harkar tawa ta bunkasa.

M.A: Daga wannan darasin da kika samu idan na fahimce ki kina zaburar da mata ne dangane da sana’o’in dogaro da kai kenan?
Mansura Isah: E haka ne, domin abu ne mai kyau kuma ya dace, domin a nan kusa da ni akwai wadda ta ke yin sana’ar alawar gullisuwa, tun tana yi kadan har abin ya bunkasa ta saye gidan da yake kusa da ita, kuma tana da ma’aikata mata da suke yi mata aiki, tana da rufin asiri na rayuwa a yanzu, kuma abin da zai ba ka mamaki ko firamare ba ta yi ba, amma gashi ta yi amfani da basiranta Allah ya daukakata mutane da yawa suna ci a karkashinta, kuma a cikin gidanta take yi ba tare da ta je ko’ina ba.M.A: Amma a irin wannan fafutukar dogaro da kai din akan samu matan da yin sakaci da al’amuransu na aure ko abin da ya shafi kula da miji. Bakya ganin hakan ce ta sa ake kyamar sana’a ko aikin mata?
Mansura Isah: To ni dai ina kallon kaina ne, kamar yanzu da kazo ka same ni a shagona ne, na fito daga gidana zuwa shago kuma ga yara na da suke kula da wajen kafin na zo ko idan bana gari sannan ni nake zuwa na dauko yara daga makaranta ka ga ‘ya ta nan tun safe nake kai ta makaranta, sai yamma naje na dauko ta, in kuma bana gari awkai mai daukota, don haka idan ka ga mace ba ta kula da gida ba ba ta yi niyya bane, don haka sana’a ba zai hana ta kula da gidanta ba.

M.A: A wajen gudanar da harkoki na kasuwanci da sana’a wanne irin matsaloli matan aure suke fuskanta?
Mansura Isah: Gaskiya matan aure suna shan wahala wajen samun abin yi kamar aikin offishi za ka ga an san matan sun iya kuma za su yi aiki mai nagarta, amma sai a hana su dalili kawai don tana da aure, don haka sai ka ga an dauko wacce ba ta kware ba don ba ta da aure, a kawo ta kama idan ba ta yi yadda ya kamata ba a ce duk mata haka suke, to gaskiya hana mace mai aure aiki duk da an san za ta iya wannan ba karamin kuskure ba ne.

M.A: Ya ake so mace mai aure ta kasance a wajan aiki ko a kasuwancinta?
Mansura  Isah: Abin dai da yake wajibi shi ne ta sani akwai ka’idojin aure da suke kanta, kuma akwai yada doka ta iyakance mata wajen mu’amala da mutane, don haka dole, idan matar aure da za tayi aiki ko wani kasuwanci ta san cewa akwai abinda ya hau kanta wajan tafiyar da aikin ta a wajan da ba cikin gidan ta ba, don haka ina kira ga mata da su san irin mu’amalar da za su yi a wajen gudanar da aikin su ko kasuwancin da suke yi a wajen da ba gidan auren su ba.

M.A: To madalla mun gode.
Mansura Isah: Nima na gode.     
Reactions
Close Menu