Babban Direba: Gajeren Labari

Daga Shamsuddeen Ibrahim Fatimiyyah"Bababan Direba mai kada karfe" kirarin da wasu yaran tasha tare da sauran wasu direbibi abikanin aiki suke yi mani kenan, musamman lokacin da aka gama yi mani lodi na shiga na tayar da motar tare da taka ta sosai. Kaina yana kara fadi musamman idan na ji sautin motar yana fita gwanin dadi.
      Idan har fasinja ya shiga motata to sai dai ya yi hakuri dimin inada ka'idoji nawa na karan kaina. Komi kankantar yaro idan har ba na goye ba nef to sai an biya masa judin mota. Haka ma idan ka na dauke da kaya komi kankantarsu ti suma sai ka biya masu kudi. Ba ruwa na da cewa kudin motar wani ba su cika ba wai na taimaka masa. Sabi da cikon naira goma ina iya ajiye mutum saman hanya na yi tafiyata.  Wata rana wata makauniya ta shiga motata tare da 'Yar jagorarta, sabo da cikon naira ashirin na sauke su daga cikin mota sai dai wani fasinja ya taimaka masu ya cika masu.
 Ban damu da gajeruwar tafiya ba, na fi yawan zuwa Legas ko kuma a yi mani lodin Mauduguri.
        Ranar wata Laraba ina cikin tashar Alaba rago cikin garin Legas motata na saman layi ana yi mani lodi, sai wani mutum ya shigo cikin tashar dauke da wani katon kwali a saman kafadarsa. Yana zowa ya fara tambayar 'Yan kamasho inda mota mai zuwa Kano take, a ka kawo shi wurin motata yace direban motar ya ke nema. Aka nuna masa ni ya karaso bangaren da nake muka gaisa sannan ya ce "Direba wani sako ne na gaggawa nake son akai mani Kano, sai dai ina son ka hadu da wanda za a ba sakon domin ka bashi sakon da hannunka don akwai kudin da zaya bada akawo mani."
    Na dubi wannan mutumin na ce " To ka san dai idan zamu kai sako ana bamu kudin mutum guda."
"Kada ka samu damuwa direba, wannan sakon mai muhimmanci ne, Idan har ka bashi sakon shima za ya ba ka sakon kudi idan ka dawo nan Lagas za ka bani."
Babbab direba ya yi murmushi sannan ya ce "Don wannan ba matsala, yanzu sai ka bada lambar wanda za a kaiwa kayan sannan kaima ka bani lambarka ta yadda idan na dawo zan kiraka." Mutumin nan ya ba shi lambar wanda za a kaiwa sakon sannan ya kuma bashi tashi lambar. Babban direba ya amshi kwalin nan ya sanya cikin mota.
    Bayan wani dan lokaci mota ta cika Babban direba ya shiga ya tada mota, bayan ya gama sallamar 'Yan kamasho ya biyo hanya. Tafe ya ke yana sauraren wakar da Sani Sabulu ya yiwa direbobi, bisa ga dukkak alamu wakar tana ratsa shi  kafarshi na saman totur hannayenshi rike da sitiyari sai faman gyada kai ya ke yi.
     Can saman titi sai suka hango wasu jami'an tsaro kusan su hudu a tsaye da bindigu rike a hannayesu sannan gefe guda kuma ga wata farar mota Hilux mai budadden ya tsaye kusa da motar wasu jami'an tsarin ne su biyu daya yana zaune  gaban motar bisa ga dukkan alamu shine direban motar.
   "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, ga barayi nan a gabanmu." wani dattijo da ke can baya zaune ya fada a razane.
     "Haba! Dattijo ya zaka dagawa mutane hankali jami'an tsaron ne baka sani ba." Babban direba ya fada. A dai-dai lokacin jami'an tsaron nan suka dakatar da motar ta hanyar da masu hannu tare da yin nunin su koma gefen titi. Sai alokan Babban direba  ya gane su, jami'an hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ne wato (NDLA). Biyu daga cikin jami'an nan suka tsaya kusa da kofar motar suna lalleka ciki suna duban mutanen da ke zaune cikin motar daya bayan daya.  Wani kuma daga cikin jami'an tsaron yana can bayan motar yana lelleka kayan dake cikin motar. "Wannan buhun menene a ciki?" jami'in dake can bayan mota ya tambaya.
"Atamfofi ne a ciki ranka ya dade."  "Wannan kwalin menene a cikinsa?" shiru babu wanda ya yi magana daga cikin motar, ya daka masu tsawa tare da sake tambayar kwalin na wanene?. Sai a lokacin Babban direba ya tuna da cewa an bashi sakon wannan kwalin. "Ranka ya dade a yi hakuri na manta, ni ne aka ba sakon wannan kwali zan kai shi kano".
"Zo ka bude muga abinda ke ciki." Wannan jami'i ya fada a fusace. A hanzarce  Babban direba ya zagayo bayan motar ya jawo kwalin nan sannan ya fara budewa. Kwayoyin TIRAMOL ne shakare cikin kwalin sai kuma wadan irin kwayoyi a bangare guda.
 Babban direba ya yi tsalle ya koma gefe tamkar wanda ya ga mutuwa a cikin kwalin.
Reactions
Close Menu