Bollywood: Fina-finai 10 da suka fi yin tashe a shekarar 2020

Fitattu kuma manya a jerin fina-finan da masana'antar  Bollywood ta shirya sakewa a wannan sabuwar shekara da muke ciki kuma masu kallon fina-finai a kasar ta Indiya da ma sauran kasashen duniya suka kagu matuka wajen ganin an kai ga shigowa sabuwar shekarar don su morewa idanuwansu kallon irin dambarwar da suke dauke da su wanda masu hasashe suka bayyana su a matsayin fina-finan da za a rasa masakar tsinke a sinimomi na kasar  saboda dafifin da za a samu na 'yan kallo sun hada da:1. Tanhaji: wanda jarumi Ajay Devgn zai fito a cikinsa bayan ya tattara bayanai kan shirin fim din nasa da jigon ciki ya ginu ne akan tarihi na wata masarauta da ake kira Maratha. Babban jarumin na Bollywood Ajay Devgn zai bayyana a cikin akwatin talabin din 'yan kallo cikin wannan zazzafan shiri tare da jaruma Kajol da kuma Saif Ali Khan wanda suma suka fito a matsayin manyan taurarin shirin.

2. Laal Singh Chaddha: shiri ne da ya hada manyan jarumai da a cikinsa taurarin suka hada da Aamir Khan da kuma Kareena Kapoor Khan. Fim din Laal Singh Chaddha din dai, kwaikwayo ne aka yi na wani fim din Amurka mai suna Forrest Gump. Inda a yanzu bayan kayataccen shirin nan na 3 Idiots da ya fita a shekarar 2009, masoyan jaruman biyu cikin kaguwa suke wajen son sake ganin jaruman a cikin wannan sabon shiri da zasu sake fitowa a matsayin taurarin ciki.


3. Chhapaak: Ba za a kalli jerin sunayen fina-finan da za su yi shuhura din a bana a matsayin cikakke ba muddin ba a ambaci sunan Chhapaak ba wanda Diva ke ciki kuma Deepika Padukone ta yi aikin shirin shi.
4. Angrezi Medium: shiri ne da ya dawo da fuskar shahararren jarumin nan na Bollywood Irrfan Khan ga masu kallo bayan shafe tsawon lokaci da bacewar fuskar tasa a sakamakon jinyar da yayi ta fama da ita na cutar daji "ccancer"bayan kwantar da shi a kasar Ingila. Irrfan din zai fito a cikin fim din ne tare da jaruma Kareena Kapoor kuma zai fito ne a ranar 20 na watan Mayun 2020. Fim din ya karkata ne akan jinsin Indiyawan kasar masu dauke da jinin turawa wato ruwa biyu.5. Sooryavanshi: Wani katafaren fim din da zai fito cikin wannan shekarar shi ne wanda jarumi Rohit Shetty da kuma Akshay Kumar za su fito a ciki wato Sooryavanshi wanda shi ne fim na frako da aka hada jaruman guda biyu a cikinsa 

6. Radhe: Bayan ragargazar kundin da yayi a shekarar 2019 da fim dinsa mai suna blockbuster Bharat, Salman Khan zai cigaba da nishadantar da masoyansa cikin wannan sabon shiri mai suna Radhe.

7. Laxmmi Bomb: Fim din da zai farauci zukatan yan kallo a rukunin fina-finan ban tsoro a wannan shekarar shi ne Laxmmi Bomb wanda jarumi Akshay Kumar wanda a cikin shirin zai fito ne a matsayin mata-maza ana sa ran tikiti zai yi karanci saboda wanda za su yi turuwar kallon shirin. Jarumar da za ta kasance tare da shi a cikin shirin ita ce Kiara Advani wadda fim dinta na karshe a shekarar 2019 ya kasance shirin Kabir Singh.

8. Shubh Mangal Zyada Saavdhan: Jarumi mai rike da kambu wanda kuma tauraron sa ya haska fiye da koyaushe a cikin shekarar 2018 da fim dinsa mai suna back-to-back box office wato  Ayushmann Khurana zai kasance a gaban 'yan kallo cikin wannan shekara ta 2020 din ma a Shubh Mangal Zyada Savdhaan tare da taurarin da suka hada da Gajraj Rao da kuma Neena Gupta jarumar da suka fito tare a fim din Badhaai Ho.

9. Thalaivi: jaruma Kangana kamar koyaushe cikin wannan shirin ta sake fitowa cikin kayataccen shirin nata da shakka babu a wannan karon ma za ta burge yan kallo.

10. Sadak 2: shiri ne da taurari irin su Alia Bhatt, Aditya Roy Kapur, da kums Sanjay Dutt za su fito acikinsa wanda Sanjay zai fito a matsayin Ravi.
Reactions
Close Menu