Bollywood: Jarumi Akshay Kumar ya shiga DubaiAkshay Kumar

Shahararren jarumin masana'antar fim ta Bollywood dake ƙasar India Akshay kumar ya haɗa komatsansa izuwa ƙasar Dubai don ɗaukar shirin fim ɗin nan da ake ta tsumayin ganin ya shigo kasuwa wato 'Laxmmi Bomb’.
Jarumin wanda ke cigaba da samun karɓuwa bayan fim ɗinsa na barkwanci mai suna ‘Good Newwz’, na cikin birnin na Dubai ɗin tun kwanaki biyu da suka wuce kuma yau ne ake sa ran zai koma ƙasarsa ta Indiya kamar yadda majiyar Bollywood ɗin ta bayyana.
Ayyukansa na Dubai ɗin dai sun haɗa da ɗaukar bidiyon waƙoƙin da za su fito a cikin fim ɗin wanda aka yi su a wasu sassa na ƙasar da suka haɗa da gaɓar tafkin Dubai ɗin wanda ke kusa da , Maidan sai kuma kan ruwan kogin Jumera.
Na wannan ne karo na farko ba da jarumin yake zaɓar shiga ƙasar ta Dubai don ɗaukar fim kuma ana sa ran fim ɗin zai ƙayutu matuƙa zai kuma burge ƴan kallo.

Reactions
Close Menu