Duba kan cigaba, koma baya da kalubalen da masana'antar Kannywood ta fuskanta a shekarar 2019
Kusan a kowace shekara sai harkar shirya fina-finan Hausa, wadda aka fi sani da Kannywood, ta rikida kamar hawainiya. Wani lokacin kuma ta rika juyawa kamar kosai a kasko; yanzu za a ga ta yi fari, a lokaci guda kuma sai a ga ta koma ja jawur.


Kannywood dai babbar harka ce a arewacin Najeriya, inda mutane daban-daban suke kasa hajarsu domin sayarwa, ta hanyar baje kolin basirarsu.


MATAKAN CIGABA


A cikin shekarar 2019, an samu abubuwa da yawa na ci gaba da kuma ci baya, wanda wasu an san su wasu kuma ba kowa ne ya san su ba.

Daya daga cikin cigaban da aka samu shi ne kirkirar sabuwar manhajar sayar da finafinan Hausa a intanet mai suna 'Northflix', wadda aka samar domin kasuwancin finafinan Hausa.


Manhajar nan ta finafinan Amurka mai suna 'Netflix' ce ta bayar da tunanin kirkirar ta.

Manufar manhajar 'Northflix' ita ce ta taimaka wa masu shawa'ar kallon finafinan Hausa da ke zaune a kasashen ketare da ma na Najeriya, wadanda idan fim ya fita kasuwa sukan dade kafin su same shi, su samu saukin samun finafinan a ko'ina mutum yake a fadin duniya ta hanyar intanet.


Sai dai ga dukkan alamu ita ma manhajar ba ta samu irin karbuwar da aka so ba, domin har yanzu ba kowa ya san ta ba, sannan ba ko wane mai shirya fim ba ne ya ke bayar da sababbin finafinansa a dora a kanta ba.

Bugu da kari, su kansu masu ita sun yi karancin talla tare da wayar da kan mutane a kan yadda ya kamata a yi amfani da manhajar.


Cigaba na biyu da aka samu shi ne bayyanar gagarumin gyaran da aka samu wajen kokarin tantance duk wani dan fim ko 'yar fim da ake nuna fuskokinsu a cikin fim saboda a san asalin kowa domin samar da masu da tarbiyya. Inda tuni Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta aiwatar da aikin tantancewar.


A da, Kannywood ta zama tamkar kasuwar daji wadda kowa zai iya shiga ba tare da an tantance sahihancin halayyarsa ko inda ya fito ba.

Ko da yake ita ma tantancewar ta bar baya da kura, inda wasu sun je an tantance su, wasu kuwa sun bayyana cewa babu wanda ya isa ya tantance su in dai ba aiki zai ba su ba. Wasu na cewa wannan aikin ba hurumin hukumar ba ne.


Akwai ma masu ganin cewa saboda 'yan Kannywood wadanda suka yi jam'iyyar PDP ya sa aka kirkiri aikin tantacewar don a samu damar taka duk wanda ya karya doka.

Sai dai hukumar ta yi ikirarin sanya kafar wando daya da duk wani dan fim tun daga kan masu rubuta labarin fim har zuwa masu tace shi, in dai har ba su je sun yi rijista ba.


A gefe daya kuma akwai wadanda ke ganin kawai salo ne na neman kudi hukumar ta fito da shi, saboda yanzu an daina yawan finafinai barkatai wanda su ne hukumar ta dogara da su wurin samun kudin shiga, shi ne su ka bullo da yin rijista.


Ci gaba na uku da aka samu shi ne yadda ake ta fafutikar neman ilimin harkar, tare da mayar da harkar zuwa yanar gizo, wato "online".

A yanzu haka kusan kashi 80 cikin dari na 'yan Kannywood za ka same su da shafin YouTube inda su ke dora mabambantan shirye-shiryen da suka yi na baya da kuma sababbin da suka yi.


Bugu da kari, wasu daga cikinsu sun zage damtse wurin fafutikar neman ilimin harkar ta hanyar halartar makarantun Najeriya da kuma na kasashen waje, gami da taron bita da kuma kara wa juna sani irin wanda ake gayyatar takwarorin su na kudancin Nijeriya.


Ci gaba na hudu da aka samu shi ne kokarin yin wani kasuwancin na daban da 'yan Kannywood su ka zage damtse daga shekarar 2019 din data gabata. Sanin kowa ne cewa yawancin jarumai sun dogara da fim din Hausa kadai ne, ba su da wani kasuwancin na daban.


Amma a shekarar 2019 jarumai da dama sun bude shaguna: misali, Ali Nuhu da Adam A. Zango kowanne ya bude shagon sayar da kayan sawa na zamani; Sani Danja da Yakubu Muhammad sun bude gidan daukar hoto; Maryam Isah Abubakar (Ceeter) da Maryam Yahya da Samira Saje kowacce ta bude shagon gyaran gashi da sayar da jakunkuna da takalma da sauran kayan mata; Muhibbat Abdulsalam na sayar da man shafawa da magungunan gyaran fata, a yayin da kwanan nan Rahama Sadau ta bude katafaren gidan sayar da abinci da sashen yin kwalliya.


CI BAYA

Wasu manyan matsaloli da Kannywood ta fuskanta a cikin 2019, wadanda kuma aka yi ittifakin za ta ci gaba da fuskanta a wannan shekara ta 2020, sun sa ana ganin kamar ci gaban mai gina rijiya aka samu a wannan shekarar da ke shudewa.


Da yawa ana ganin cewa 2019 ita ce shekara mafi koma-baya da 'yan Kannywood suka tsinci kansu a ciki, sakamakon durkushewar da kasuwancin finafinai ya riska. Babbar matsalar da masu shirya finafinan Hausa su ke fuskanta ita ce ta durkushewar kasuwanci, sakamakon dogaro da suka yi da kasuwar CD ta Ƙofar Wambai a garin Kano, wadda ita ce babbar kasuwar hada-hadar finafinan.


Mujallar Fim,  ta dade ta na jan hankalin masu shirya finafinai da su lura da cewa kasuwar CD ta Ƙofar Wambai ta na kokarin mutuwa, amma sai wasu daga cikin 'yan fim din su ka dauki abin kamar al'mara. Sai a yanzu suka fahimci hasashen da aka yi ya tabbata.


In banda Kannywood, duk duniya babu inda ake sakin finafinai barkatai. An yi lokacin da sai a saki sama da guda 40 cikin mako biyu. Haka kuma idan ka kalle su za ka ga duk kusan labarai iri daya ne, kuma jaruman iri daya ne.


Idan Ali Nuhu da Jamila Nagudu ne a cikin fim din wane, to shi ma wancan in ya tashi shirya fim su zai saka saboda wai su ake tashe. Da haka aka gundiri 'yan kallo, su ka rika ja baya da sayen finafinan.


Wannan ya na ɗaya daga cikin dalilan da su ka sa kasuwar ta mutu.


Jigon finafinan ma ya zo ya rika yin kama da juna. A Kannywood ne idan furodusa daya ya yi fim a kan kishi ya samu karbuwa, to sai a samu akalla mutum goma da za su yi makamancin sa; sun kasa bude kwakwalwarsu ta yadda za su tabo abin da ya shafi Malam Bahaushe.


Kullum dai labarin soyayya ko aure ne, sai lafta rawa da waka a ciki! Ta haka aka rika bai wa jaruman lakabi, a ce wance ta fi dacewa da jigon mugunta, wane ya fi iya fim na soyayya, wance kuma gwanar kisisina ce, wane kuma gwanin rawa ne. Hakan ya sa da an ga fostar fim da hotunan wane da wane, to an san inda labarin ya dosa.


Amma duk da haka, za ku ga finafinai masu dogon zango (wato 'series') irin su 'Dadin Kowa', 'Kwana Casa'in' da kuma 'Gidan Badamasi' da ake nunawa a talbijin sun samu karbuwa a wurin mutane saboda bambance-bambancen da ke tsakanin su da irin finafinan da aka saba kaiwa a kasuwar CD ta Ƙofar Wambai.


Sai dai wasu na ganin wannan yanayin na tabarbarewar kasuwancin fim da masu harkar suka tsinci kansu a ciki lokaci ne ya zo da masana'antar za ta yi tankade da rairaya inda za ta wankacalar da wasu jaruman da daraktoci har ma da furodusoshi da duk wanda ya ki tafiya daidai da zamani.


Tun a yanzu ma ta fara wankacalar da wasu furodusoshin idan aka yi la'akari da cewa an rage yawan fita aikin fim. A yanzu in ban da irin su Abubakar Bashir Abdulkareem, wanda aka fi sani da Maishadda, da irin su Naziru Ɗanhajiya, ba kowa ne ke iya fita lokeshin ba. Tuni dai gwiwoyin wasu daga cikin masu harkar fim suka yi sanyi, kuma sun shiga tsaka mai wuya.


Saboda idan sun yi fim din ma babu yadda za su yi da shi. A ka'ida, duk bayan sati biyu ya kamata a saki finafinai 12, amma yanzu sai a kai wata biyu ba a saki fim 10 ba. Akwai ma makwannin da su ka zo suka wuce ko fim daya ba a saki ba.


Hakan kuma ya kan shafi 'yan wasan, wadanda da yawan su fatara ta addabe su. Wasu sun fara neman wasu hanyoyin na neman abinci. Babban misali shi ne Adam A. Zango, wanda kwanan nan ya bayyana cewa shi fa ya koma Legas da zama don ya rika halartar bukukuwan 'yan Arewa mazauna kudu, ya na samun kuɗi.


Akwai kuma masu ganin zamani ne kawai ya durkusar da kasuwar CD, saboda a yanzu za ka iya shiga gida goma ba ka samu uku masu na'urar CD ba; kowa tauraron dan'adam yake amfani da shi.


A wani kwakkwaran bincike da muka yi, mun gano cewa a yanzu haka ba a iya buga kwafin CD sama da dubu biyar a fitar da shi kasuwa. Ko an buga su din ma sai an maido maka ragowa da yawa.


Hakan ya sa furodusoshi da yawa sun kasa ba 'yan kasuwa finafinansu.


Akwai ma wani da ya tabbatar mana da cewa yanzu duk kyan fim a Kasuwar Ƙofar Wambai bai wuce a saye shi N100,000 ba, ko nawa ka kashe wurin buga shi.


Fitattun jarumai irin su Ali Nuhu, Adam A. Zango, Sadiq Sani Sadiq, Sani Danja da sauran su kowannen su ya na da sabon fim a kasa, amma sun kasa fitar da shi kasuwa saboda tsoron asarar da za su yi, da tunanin makudan kudaden da suka narkar wurin shirya finafinan.


Ali Nuhu yana da 'Kar Ki Manta Da Ni', Adam A. Zango yana da finafinai irin su 'Gwaska Return', 'Gudun Mutuwa', 'Haseena' da 'Ramakon Gayya'; Sani Danja na da 'Akeelah', Sadiq Sani Sadiq da Rahama Sadau suna da 'Mati A Zazzau'. Duk wanda ka tunkara a Kannywood zai ce maka yana da fim a kasa, amma tsoron yadda kasuwar ta koma ya hana shi fitarwa.


Kuma a wani bangaren na sayar da fim, samuwar gidajen talbijin irin su Arewa24 da Farin Wata da African Magic Hausa ta haifar da koma-baya ba kadan ba.


Domin a shekarun baya gidajen talbijin da ke sayen fim sukan saya da tsada. Amma saboda son zuciyar wasu daga cikin 'yan Kannywood su ka lalata harkar, inda suka rinka bi su na karbar finafinan mutane su na sayarwa da tsada sai kuma su ba masu finafinan kudi kadan.


Su kuma gidajen talbijin din da suka gane, sai suka daina sayen finafinan da daraja. Wannan ya kara taba harkar fim ta kowane bangare.


Su ma 'yan kallo, sai su ka gwammace su kalli finafinan da wadannan tashoshin ke haskawa, maimakon su je kasuwa su sawo fayafayen CD su kawo gida.

Yanzu ba kowa ba ne ke saya wa iyalinsa fim ba, sai dai ya ce kawai su kalla a talbijin.


A bangaren gidajen sinima kuwa, bayan hankalin 'yan Kannywood ya dawo jikinsu, suka fahimci cewa kasuwar CD ta mutu, sai su ka rinka yin kwambar kai finafinansu a gidan kallo na Film House Cinema da ke cikin cibiyar hada-hada ta Ado Bayero Mall, a Kano.


Shekara biyu da suka gabata lokacin mutane na dokin abin, an samu finafinai wadanda aka yi tururuwar kallo irin su 'Kalan Dangi', 'Mariya', 'Mansoor', 'Rariya', da 'Gwaska Return'. A lokacin, akan dauki tsawon lokaci kafin a haska fim, wanda hakan ya sa duk lokacin da aka tashi nuna fim sai mutane sun yi dandazo wurin kallon shi.


Amma a shekarar 2019, mun ga abin ya canza zani, domin kuwa an samu karancin masu kallo; kusan duk sati sai an kai sabon fim, amma a satin idan mutum ya lissafa bai samun mutum 500 da suka shiga.


Sai furodusa ya yi sa'ar gaske kafin ya samu kudin da suka kai N200,000. Idan kuma aka gama kallon shi a can sai dai ka zuba masa ido domin babu wurin kai shi, ko da yake an samu wadanda su ka haska finafinan su a lokacin bikin Babbar Sallah a Kaduna da Katsina, amma su din ma babu wanda ya samu sama da naira dubu dari.


KALLO YA KOMA SAMA

A yanzu dai haka kasuwancin finafinan Hausa ya yi mutuwar kasko, kuma ba a san lokacin gyara shi ba. Kusan a ce harkar ta mutu murus, kuma har yanzu an kasa gano hanya mai bullewa.


A wannan shekara ta 2020, ana sa ran a ga abin da shugabannin Kannywood za su yi domin ceto sana'ar. Jama'a sun zuba ido su ga abin da Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya, wato MOPPAN, za ta yi.


Kwanan baya dai aka zabi sababbin shugabannin kungiyar, da Dakta Ahmed Sarari a matsayin shugaba. Sarari ya ci zabe ne bisa alkawarin zai gyara kasuwancin finafinai. To yanzu kallo ya koma kansa, ana jiran a ga da wacce ya zo. Wasu na cewa Allah ya sa dai duk kanwar ba ja ba ce!


Reactions
Close Menu