Kwalliyar Priyanka ta girgiza taron Grammy 2020 Award


A babban taron bikin karramawa taurari da aka gudanar daren jiya Litinin mai suna "Grammy 2020 Award", karo na 62 a cikin dakin taro na Staples dake birnin Los Angeles na ƙasar Amurka wanda Lizzo ce ta lashe kambun na bana.

Grammy Award dai shi ne taron da ake karrama mawaka mafi girma a duniya kamar yadda jaridar Bollylife ta wallafa inda kuma bayyanar Priyanka Chopra tare da mijinta wato shahararren mawaƙin nan Nick Jonas a ɗakin taron shi yafi komai ɗaukar hankalin waɗanda suka bibiyi yadda taron karramawar na bana ya kasance inda kuma a ɓangare guda masu sharhi ke ganin cewa ma'auratan sun zamo sanadi na ƙara hauhawar taron na bana izuwa matsayi na kasantuwarsa mafi girma fiye da sauran tarurrukan da suka gabata a baya.


Prinka tare da Nicky

Ba komai ne ya dauki hankalin mutanen ba illa kwalliyar da jaruma Priyanka din ta yi wadda ta kasance shiga mafi rikitarwa da aka taba ganinta a ciki tun daga farkon fara fitowarta a fina finan Bollywood zuwa yanzu.
Tawagar fitattun mawakan nan ma da ake jira da Jonas Brothers su ma sun halarci taron tare da matayen su. Joe Jonas tare da matarsa Danielle, Kevin da matarsa Sophie. An karrama mawakan da wata wakarsu mai suna "Suckers" Har ila yau kuma an basu damar rera waka a dandalin don nishadantarwa sun kuma sanya shauki a zukatan mutanen dake wajen.Karo na karshe da aka ga fuskar Priyanka din dai a cikin wata wakar kamfanin Jonas Brothers din ne mai suna What A Man Gotta Do wanda aka haskata tare da Nick. Amma kwana kusa za a sake ganinta cikin shirin The White Tiger", inda za ta taka rawar cikin shirin tare da jarumi Rajkummar Rao.
Ma'auratan uku bakidaya sun yi hoto tare sun kuma dora hotunan a kafafensu na sada zumunta inda sukan yi rubutu a jiki dake nuna tsantsar farincikin su.
Reactions
Close Menu