Game da mawakin:
Dakta Aliyu Usman Tilde sha'iri ne, tsohon malamin jami'a, ɗan siyasa kuma marubuci kan al'amuran yau da kullum. A yanzu shi ne Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi.
RAHMATA
1. Sarki ga shi nai sammako
Ya Allah ka min taimako.
2. 'Ƴar waƙa na so zan yi yau
Fata ta ta zo mun da kyau.
3. Zan tsara a kan Muƙtadab
Don 'yar nan ta zam mai ladab.
4. Yarinya idan kin fice
Dan kyau kar ki zam kin ɓace.
5. Duk assha ki faɗa masa
Kar gobe ki zam kin rasa.
6. In niyyar ki bin duniya
Kwanan nan ki na wai-niya.
7. Don halin ta ne ɗaukaka
Bayan nan ko sai hallaka.
8. Paris har da New York daɗa
Las Vegas garin tambaɗa.
9. Tarbar ki da busa, kiɗi
Gayu sun yi caa ba faɗi.
10. Sheɗanu su na yin biki
Duk kunya su yaye miki.
11. Ba riga, zani, kallabi
Duk sunna ya zam ba ki bi.
12. Bayan kin nitse gun ɓata
Dunya ba abin tabbata.
13. Girma za ya zo ko ƙiba
In kin zo a ce, “Ke haba!”
14. Kullum sai cikin damuwa
Ba rol babu mai son zuwa.
15. 'Yan yara da kyawun sifa
Sirara da kyawun ƙafa.
16. Su ne za a ɗauka a sa
Ke kau an gama sai ƙasa.
17. 'Yar Fillo ina za ki ne?
Saurare ni ko ƙanƙane.
18. Vegas ba Elisha Cutbert
Sannan ba su Lacey Chadert.
19. Rachel Cook ina yau ta ke?
Mandy Moore a yau ta fake.
20. Suna duk idan ya zube
Gawa ce idan ta ruɓe.
21. Manya sun nasiha su na
Don Allah ki dawo mana.
22. 'Yar Fillo nasiha guda
Tsoron Jallah kullum daɗa.
23. Zazzau har Kano, Jos Kwata
Fata kar ki zam kin ɓata.
24. Zam gode wa Sarkin duka
Bin sunna ki zam kin riƙa.
25. Shi laifi tudu na sani
Hau naka ka hango mini.
26. Laifi na da tarin yawa
Jinƙan Jallah ya mar yawa.
27. Laifi na ya dala yake
Fata Jallah ba bincike.
28. Ya Allah ka shiryar da mu
Zan jinƙan mu ya Rahimu.
29. Sarki Rabbi nai tambaya
Ran gobe idan an tsaya.
30. Laifi nawa har Rahmata
Yafe min, ka yafe mata.
31. Tsira kan sa Al-Mustafa
Bawan nan da kab ba Shafa.
32. Tammat za ni ƙare haka
Na gode wa Mai-ɗaukaka.
0 Comments