"Sirrin rubutu na daga Allah ne" - Ayuba Muhammad Danzaki"Sunana Ayuba muhammad Danzaki an haife ni anan cikin birnin Kano a karamar hukumar Gezawa cikin wani gari da ake kira Danzaki....Asalin kasancewata marubuci ya samo asali ne a shekarar 1996 sanda na karanta wani littafi a lotan mai suna INDA BA KASA.."

Shin ko ya tarihin wannan gawurtaccen marubucin da ya kwashe akalla shekaru 24 yana rubuta labarai zai kasance?
Wadanne irin tambayoyi kuke zaton marubucin ya amsa a yayin wannan hirar da Mujallar ADABI ta yi da shi?

Ku biyo mu a wannan dandali na Facebook ko kuma shafin mu na intanet a ranar Asabar mai zuwa don karanta cikakkiyar tattaunawar da wakilin Mujallar ADABI Musaddam  Idriss Musa yayi da  wannan hamshakin marubucin da ya ga jiya kuma yau ma ake bugawa da shi a duniyar rubutun Hausa.
Reactions
Close Menu