SOYAYYA: Rubutacciyar waka

Faridat Musa (Sweery)

Daga Faridat Musa Sweery

Tsokaci: Faridat Musa (Sweery) matashiya ce da Allah ya yiwa baiwar iya zana labari wanda hakan ya kai ta ga zama marubuciyar harshen Hausa inda har ta rubuta littattafai da dama wanda ake iya samun su a shafukan sada zumunta dake yanar-gizo. Likkafar marubaciya Sweery din dai wadda ta kasance haifaffiyar jihar Bauchi kuma mazauniyar garin na Bauchi ta cigaba inda a yanzu ta kama hanyar zama daya daga rukunin matan da suka yi fice wajen tsara rubutattun wakoki.  Ga daya daga wakokin da marubuciyar kuma sha'ira ta rubuta wadda ita ce mace ta farko da ta samu damar shiga shafin Fasihiyyah na Mujallar ADABI.


SOYAYYA

Soyayya da dad'i a cikin rayuwa!

Idan ka dace ka more rayuwa!

Idanka rasa shi ko sai ka jika damuwa!

Ni na dace ba sauran damuwa !

Na shiga shauk'i har na
             mance yadda na ke rayuwa

Zak'inta ya zarce mad'i
                  da Zuma 'yan uwa!.

Duk sanadin soyayya ce 'yan uwa!.

Ni dai bani da haufi
                      kan soyayya 'yan uwa!.

Na samu babu rashi a cikin rayuwa!.

Wasu sun rasa ta sun
                         dandani d'acin rayuwa!

Wasu za ka ga sun d'imauce
                       har sunyin rashin rayuwa!

Wasu ko sun zauce sun
                             shiga halin d'imuwa!

Basa banbance fari
                          da baki a cikin rayuwa!

Wasu a sanadi na ta sun bar duniya.

Idan ka dace rik'e ta
            baka da sauran damuwa!

Domin ita ce jigon rayuwa!.

Ba haufi ko Matsala in ka
             dace ka samo rayuwa!.

Zaka jika daban da saura
              duk a cikin rayuwa!.

Ka rik'eshi tilo jal ba
               k'ari a cikin rayuwa!.

Sweery ta rairo wak'ar soyayya
                 duk a cikin rayuwa,
fatan alkhairi nai wa
          masoya wa 'yan uwa!.

Wallafar Sweery.

Reactions
Close Menu