Faridat Sweery: Marubuciyar da ta koma mawakiya

Daga Musaddam Idriss Musa, Potiskum 
Faridat Musa (Sweery)

Matashiya mai tashen nan a rukunin mata marubuta da ake samu a yanar-gizo kuma marubuciyar littattafan da suka hada da Ni'imatullah, Kanin Ajali, Rayuwa Shirin Allah, 'Yar Maye, Rayuwar Hostel, Watan Wata Rana, 'Yar Sarki Ce dasauransu wato Faridat Musa wadda aka fi sani da lakabin alkami 'Sweery' ta kama hanya gadan-gadan na zama cikakkiyar marubuciyar wakokin Hausa. 

Sweery din dai wadda ta ta kasance haifaffiyar jihar Bauchi dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya kuma mazauniyar garin na Bauchi ta sha shiga rukunnan gasar wakoki na Mujallar ADABI mai sunan #postchallenge da kuma #voice-challenge a zauren Marubuta na WhatsApp kuma a yanzu marubuciyar ta rubuta cikakkiyar waka mai jigo akan soyayya inda ta yi amfani da tausasan kalamai cikin yanayi mai bayyana tasirin so a zuciyar mawakiyar a wajen rubuta wakar tata.

A yanzu haka dai marubuciyar ta daura damarar shiga gasa ta rubutacciyar waka wadda kungiyar Potiskum Writers Association take gudanarwa a kowane karshen wata. 

Malama Sweery tsohuwar daliba ce a makarantar Bauchi institute for Arabic and Islamic studies inda ta karanci ilimin kasuwanci wato (Business Education) kuma a yanzu haka malama ce a makarantar firamare ta 'Dan fodio dake cikin garin Bauchi..
Reactions
Close Menu