Wakar Ƙarangiya Na Malam Mudi Spikin


Alhaji Mudi Sipikin a cikin 1980

DAGA MALAM MUDI SIPIKINWaƙar "Ƙarangiya" Ta Malam Mudi Sipikin

1. Da ƙunci da ƙinci ga ƙaƙanci ƙulafuci

Ƙaranci ƙalancewa ƙanƙanta ƙuriciya2. Da ƙima da ƙyama ga ƙiyama da ƙanƙamo

Akwai kuma ƙamama ƙazama ƙurus ɗaya.3. Da ƙauri akwai ƙwauri da ƙwauro da ƙwarzaba

Da ƙwara da ƙwaro ƙwarƙwara ƙwai da ƙoƙiya4. Da ƙirji da ƙin ji ga ƙirinjijiya ka ji

Ƙagewa akwai ƙage ƙaranga ƙarangiya5. Da ƙeya da ƙyuya ƙi da ƙauna ƙalamusai

Ƙwalewa da ƙyalewa ƙalewa ƙalauniya6. Da yin ƙyanƙyasa kuma ƙeƙasasshe ƙasa-ƙasa

Ƙasashe akwai ƙas-ƙas ƙasa ƙansuwa ƙaya.7. Da ƙwarya akwai ƙarya ƙaraya ƙara-ƙara

Ƙirare da ƙarewa da ƙaro ƙaya-ƙaya.8. Da ƙanzo akwai ƙozo da ƙwazo da ƙwarnafi

Da ƙarfi akwai ƙarfe ƙarau ƙulla tankiya.9. Da ƙiri da ƙira ƙirƙira kuma ƙoƙori

Da ƙari da ƙarewa ƙurewa ƙalauniya.10. Da ƙaura akwai ƙaura ƙwarewa da ƙwarzana

Ƙagewa akwai ƙage da ƙuna da ƙugiya.11. Da ƙeta da ƙato har da ƙoto da ƙatuwa

Da ƙarti da ƙullutai da ƙulu ka tambaya.12. Da ƙunda da ƙwadda ƙaudaji har da ƙuddaji

Da ƙumba ƙarambau ga ƙurungu da karkiya.13. Da ƙwallo da ƙwalla ƙwalla ihu akwai ƙwala

Ƙwaƙwalwa akwai ƙwalama ƙalau ƙallabe wuya.14. Da ƙimi akwai ƙaimi da ƙima kawai kuma

Da ƙyalli da ƙyallawa kili ga ƙurus ƙaya.15. Da ƙulli na koko har da ƙullin mutum a rai

Da ƙulli sa'annan ƙulle-ƙulle da ƙyaliya.16. Da ƙulli na duka dabam-dabam

Da ƙaba ƙalata ƙeƙuwa masu karkiya.17. Da ƙwara da ƙaura ƙauracewa ƙiri ƙiri.

Ƙurewa da ƙarewa ta waƙa ƙirarriya.
Reactions
Close Menu