Gudummuwar Alhaji Ado Yaro Gashua Ga Kungiyar RAYAAS Ta Kasa - Auwal Adamu Differences, Yola


Fitacce kuma goggen Dan-Jarida, Alhaji Yaro Yaro Gashua dan asalin jihar Yobe ne dake arewa maso gabashin Najeriya. Wakili ne a gidajen rediyo da tallabijin na jihar Yobe wato YBC da kuma YTV, kuma mai gabatar da shirye-shirye ne a tashar tauraron Dan Adam na Tauraruwa TV Sha-Kallo, da gidan rediyon Dandal Kura International da kuma tashar Liberty TV. Mutumin kirki ne kwarai, mai hakuri da zumunci kuma dukda ya ke na jima da sanin shi ta hanyar kafofin yada labarai da jaridu, na fara haduwa da shi ne ta hannun Alhaji Umar Fo-ever Gashua (Shugaban Kungiyar RAYAAS Reshen jahar Yobe).

Gudummuwarsa Ga Kungiyar RAYAAS
An fara hada mu da shi ta waya a lokacin da mu ke kokarin shirya taron kungiyar RAYAAS ta kasa baki daya karo na biyu wanda ya gudana a jahar Bauchi, bayan na zayyana masa bukatar da mu ke da ita musamman ta bangaren manyan kafafen yada labarai na rediyo da na talabijin na duniya.

Bayan kwana biyu bawon Allahnan takanas ta kano ya taso tun daga jiharsa ya zo har nan garin Jimeta-Yola, fadar jihar Adamawa domin ya kara bamu haske game da irin hanyoyin da ya kamata mubi wajen hada mu'amala da manyan kafafen yada labarai da mu ke bukata, sannan ya kara bamu wasu muhimman shawarwari kan yadda zamu rika shirya tarukan kungiyarmu cikin nasara da kwanciyar hankali a kowace shekara.

Sannan ya bamu lokacinsa wajen halartan wannan gagarumin taro da mu ka shirya tare da abokanensa 'yan jaridu, da kuma membobin jahar Yobe da su ka ta ke masa baya.

Bugu da kari ya kara tallata manufofi da aiyukan wannan kungiya a idanun duniya bayan mun rabu da shi a jahar Bauchi, a wajen wani babban taro da wata shahararriya kuma dadaddiyar kungiya ta shirya a jaharsa ta Yobe, inda jama'a da yawa su ka amsa kiransa na shigowa tafiyar kungiyar RAYAAS sanadiyyar bayanansa.

Bayan haka, Alh. Ado ya kara shiga zuciyarmu sanadiyya kyakkyawar tarba mai cike da karamci da girmamawa da ya yiwa, mai girma mataimakin shugaban kungiyar RAYAAS reshen jahar Adamawa, Hon. Muhammad Faisal Adam akan hanyarsa ta zuwa Maiduguri babban birnin jahar Borno, wadda ta kai ga sai da ya kwana a garin Damaturu fadar gwamnatin jahar Yobe, a gidan Alh. Ado Yaro.

Har iya yau, ya na daga cikin mutanen da su ka jagoranci tawagar shugabannin kungiyar RAYAAS zuwa ofishin tsohon kakakin majalisar Dokokin jahar Yobe, Alh. Adamu Dala Dogo (Murabus), kuma ya taka rawar gani wajen tabbatar da cewa kungiyar RAYAAS ta samu karbuwa a hukumance wajen gwamnatin jahar Yobe.

Alh. Ado yayi wasu muhimman abubuwa da lokaci ba zai bani damar kawo su yanzu ba...... Kuma har yau yana sahun gaba cikin masu bada shawara da masu nemawo kungiyar RAYAAS cigaba akoda yaushe.

Muna godiya mai sunan babana. Allah ya kara dankon zumunci.

Auwal Adamu Differences
Sakataren tsare-tsare na kasa a kungiyar RAYAAS.
Reactions
Close Menu