Karo na farko Jaruman Bollywood sun yi fim a Najeriya


Manyan masana'antun shirya fina-finan nan biyu da suka shahara a duniya wato Bollywood dake kasar Indiya da kuma Nollywood wadda ke nan gida Najeriya sun hada hannu wajen shirya wani kayataccen wasan kwaikwayo na soyayya hade da barkwarci mai suna "Namaste Wahala" wanda zai fito a ranar 4 ga watan Afirilu mai zuwa.

Fim din dai shi ne zai zamo na farko a tarihi da masana'antun biyu suka yi tarayya akai kuma abubuwan dake ciki sun hada da soyayya tsagwaro, barkwanci, abubuwan ban tausayi cudanye da nuni kan yadda bambancin al'adu ke taka rawar gani gami da tasiri wajen zamantakewa.

Taurarin da suke cikin fim din dai wanda Hamisha Daryani ce ta shirya shi sun hada da manyan taurarin Bollywood na kasar Indiya wato Ruslaan Mumtaz da kuma Segal Sujata. Yayin da anan gida Najeriya kuma jaruman da suka hada da Mofe Damijo, Ajoke Silva, Inidima Okojie, Ruslaan Mumtaz, Segal Sujata, Adaora Lumina, Ibrahim Suleiman, Imoh Eboh, Osas, Eneeicha, Mexemania, Tience Pay, MI Abaga da sauransu duk suka taka rawa a cikin shirin.


Hamisha din dai wadda bayan shiryawan ma ita ta bayar da umarnin shirin, ta bayyana cewa sha'awar da take da shi na son harkar fim ita ta kai ta ga shirya wannan wasan kwaikwayon. Ta kuma kara da cewa rayuwarta na kasar Indiya da kuma wadda take anan birnin Lagos a Najeriya, su suka kai ta ga shirya labarin wanda  a ta wani bangaren a cewarta ya yi kama da fadi tashin da ta yi a rayuwarta kasar Najeriya.

Hamesha

Reactions
Close Menu