Lailai: Mataimakin Shugaban Kungiyar Yobe Authors Forum Yayi wa kungiyar Bankwana


A ranar Litinin din makon da ya gabata ne shahararre kuma fitaccen dan jaridan nan da yake da kwarewa ta musamman ta fuskar watsa labaran rediyo da kuma gabatar da shirin talabijin wato Muhammad Yakubu Lailai ya gabatar da jawabi kan matsayarsa yayin wata tattaunawa da wakilin Mujallar ADABI Musaddam Idriss Musa inda a bayanin nasa ya bayyana cewa ya zare hannayensa daga tafiyar sabuwar kungiyar marubutan nan da ake shirin kafawa a jihar sa ta Yobe din mai suna Gamayyar Mawallafa littattafa na jihar Yobe wato "Yobe Authors Forum" a turance tare kuma da ajiye mukaminsa da yake rike da shi na mataimakin shugaban kungiyar da ake yiwa lakabi da YAF a takaice.

Murabus din Lailai din dai ya faru ne biyo bayan bikin kaddamar da littafinsa na farko da aka gudanar a garin Nguru dake jihar Yobe yayin bikin kungiyar Muryar Talaka na Kasa wanda ya gudana a ranar Asabar din da ta gabata inda kuma anan ne cibiyar tsohuwar kungiyar tasa mai suna YAF din ake fatan zai zai kasance.
"...na ajiye waccan tafiyar, shirme ce kawai", inji Lailai.

Wani abin da ya dauki hankali shi ne yadda yin murabus din mataimakin shugaban kungiyar Yobe Authors Forum din ya zo kwatsam cikin kwanaki biyu kawai da barin sa daga garin na Nguru inda har aka gan su tare da shugaban kungiyar a wani hoto da suka dauka tare kafin ya baro garin inda hakan ya sanya wasu ke kallon cewa ruwa ba ya tsami banza musamman idan aka yi la'akari da rawar da Lailai din ya taka ta fuskar bada gudummawa wajen kafa kungiyar tun a farkon fara tafiyar lokacin da aka ambaceta da sunan Yobe Writers Association of Nigeria (YOWAN) kafin daga bisani ta koma Yobe Authors Forum a bisa ganin cewa sunan yayi kama kwarai da na tsohuwar kungiyar marubutan jihar da ake Kira Yobe Writers Association (YOWA) wadda fasihin  marubuci Bukar Mustapha Damaturu ke jagoranta.A halin da ake ciki dai yanzu Lailai din ya bayyana kudurin dawowa ainihin tsohuwar kungiyar tasa wadda a baya yake rike jagorancin ta na rikon kwarya wato Yobe Writers Association (YOWA) tare da yin bankwana da kungiyar Yobe Authors Forum da ake yiwa lakabi da gamayyar mawallafa littattafai na jihar Yobe wadda Ibrahim Garba Nayaya ke jagoranta.
Reactions
Close Menu