Lokaci yayi da ya kamata a koma yiwa rubutun Hausa kallon sana'a - Muttaƙa A. Hassan


Muhammad Muttaka Abdullahi, wanda aka fi sani da Muttaka A. Hassan. Haifaffen unguwar Kawo ne, cikin karamar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano. Marubuci ne kuma manazarci da ya karanci ɓangaren Hausa da kuma addinin musulunci kuma a halin yanzu ya shafe shekaru 14 da fara rubutu.
A wannan tattaunawar ta su da wakilin Mujallar ADABI Musaddam Idriss Musa za a ga yadda marubucin ya bayyana ra'ayinsa na son ganin marubuta sun koma yiwa rubutu kallon sana'a a maimakon abu na sha'awa kawai.

Mujallar ADABI: Mene ne tarihin rayuwarka?

To da farko dai sunana Muhammad Muttaka Abdullahi, wanda aka fi sani da Muttaka A. Hassan. Haifaffen unguwar Kawo ne ni, cikin karamar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano.

Na fara karatun addini tun ina karami a Tahzirul Aulad da Ansarul Haqq Islamiyya duka a Kawo. Na yi primary a Giginyu Special primary school daga 1997-2003. Daga nan na je G.S.S Tarauni inda na kammala karamar sakandire wato daga 2003-2006. Sai kuma na tafi makarantar kwana Gov't (Unity) Secondary School da ke Ringim, jihar Jigawa, inda na kamala a shekarar 2009.

A shekarar 2011 na samu gurbin karatu a Kwalejin Ilmi da Shari'a ta Malam Aminu Kano da ke jihar Kano, inda na samu kwalin diploma a Hausa/Islamic Studies/Education a shekarar 2013.


Mujallar ADABI: Yaushe ka fara rubutu kuma zuwa yanzu littattafa/labarai nawa ka yi?

To da na zo aji uku a sakandire (2006) na fara rubuta wani littafin yaki mai suna Karar Kwana, sai dai ban iya kammala shi ba (watakila saboda rashin sanin makamar aiki) haka na watsar. Amma da na je makarantar kwana na samu isasshen lokacin yin rubutu, inda na yi ta rubuce-rubuce da dama, sai dai su ma babu wanda na kammala. A takaice dai ban rubuta labari cikakke ba wanda za a kira littafi ba sai a shekarar 2011.

Adadin littafai kuma guda 7 ne, amma idan har da gajerun labarai ban san adadinsu ba. Saboda su nakan yawan rubuta su.


Mujallar ADABI: Me ya ja hankalinka wajen zama marubuci?

Sha'awa. Duk wani dalili da zan fada a bayan sha'awa ko na ce so yake. Wato tun ina furamare (lokacin ko karatun ban iya ba) ana karanta mana Magana Jari Ce na ji a raina ina sha'awar na zama marubuci, daga nan ne kuma na fara ji a raina lallai zan iya. Bayan haka kuma sai na lura rubutu wata hanya ce ta tattaunawa da al'umma da dama har na isar musu da sakona.


Mujallar ADABI: Yaya kake ganin rubuce-rubucen Hausa a yanzu?

Har yanzu ina musu kallo irin wanda nake musu a baya, wato hanyar isar da sako ga al'umma cikin hikima.


Mujallar ADABI: daga jerin littattafanka wanne ne ka fi so a ranka?

A cikin wadanda na kammala zuwa yanzu na fi son IDON MAKWARWA saboda shi ne wanda na fi shan wahala wurin rubuta shi. Sai dai ban sani ba ko nan gaba zan rubuta wani da zan so fiye da shi.


Mujallar ADABI: ka kasance daga marubutan ƙarni da suke tashe kuma ake damawa da su a halin yanzu. Shin waɗanne nasarori ka samu kawo yanzu?

Babbar nasarar da na samu ita ce; sakona yana isa ga al'umma har a samu wani ko wata ya gyara ko su gyara wata barna da suke yi, wannan babbar nasara ce a gare ni musamman idan na kwatanta da farkon farawata, lokacin da babu wanda ke karantawa sai ni da na rubuta abuna.


Mujallar ADABI: ba ya ga rubutun labarai kana nazarin rubuce-rubuce, ya aka yi ka samu kanka a wannan fanni?

Tun kafin na fara rubutu, idan na karanta littafi ina ganin inda marubuciya/marubuci ya yi kuskure da inda ya yi daidai da kuma inda nake bukatar tambaya, nakan tara na kira wayarsa ko email na tura. To da kuma na fara karatun (diploma) a Hausa department sai na kara koya tare da nakaltar hanyoyi da dabarun nazarin ayyukan adabi, musamma a wasu courses da na yi kamar; Hausa Oral Literature, Hausa Writting prose da Hausa Literature. Har wa yau na duba wasu littafai na Prof. Sa'id Muhammad Gusau kamar Jagoran Nazarin Wakar Baka da sauransu, wadanda su ma sun taimaka matuka wurin gane hanyoyin da ake fede rubutu a fito da gyararraki ta salon da aka yi amfani da shi da sauransu.


Da nazari da kuma rubuta labari wanne ka fi jin dadin yi?

Ina yiwa rubutu kaunar da zai wahala a samu wani abu da nake so kamarsa, shi ya sa ma na fi yin rubutu a kan nazari. A takaice na fi son na yi rubutu.


Mujallar ADABI: wasu na ganin marubutan Hausa ɓata tarbiya suke. Me za kace akan haka?

E, to! Zan iya yarda, zan kuma iya karyatawa. Tabbas da sun ce 'wasu marubutan bata tarbiya suke yi' da zan yarda. Saboda batu na gaskiya akwai masu bata tarbiyar, wadanda akasari za ka iske su suna da hikima da basirar kirkira kamar sauran marubuta, sai dai suna amfani da hikimarsu wurin amfani da kalmomi masu nauyi wadanda ina da yakinin ko su ka ba wa ka bukaci su karantawa iyayensu ko wasu manya ba za su iya ba. To idan haka ne a wane dalili za su rubuta su mika wa iyayen wasu ko 'ya'yan wasu? Sai dai duk da haka ba zan gamsu da su ba idan suka yi jam'i ta hanyar cewa 'marubuta' maimakon 'wasu marubuta.' Domin tabbas marubuta mutanen kirki ne, kullum burinsu su yi gyara. Sannan kowace irin harka a kan samu nagari da bata gari, don haka kuskure ne a hukunta marubuta da kuskuren wasunsu.


Mene ne babban burinka game da rubutu?

Babban burina game da rubutu shi ne; wata rana na rubuta littafin da za a karanta shi a ko'ina a fadin duniya saboda muhimmancin sakon da yake ciki. Abu na biyu kuma ina matukar burin a ce rubutuna ya fadakar da ko da mutum 1 ne a cikin mutanen da suka karanta, saboda komai yana farawa ne daga daya.

Mujallar ADABI: wasu manazarta irinka na ganin online writers suna dakushe harshen Hausa ne. Ya kake ganin al'amarin?

E, to. Watakila wadanda suka fadi haka suna da hujjojin da suka dogara da su, ta yiwu kuma sun yi bincike ne ta hanyar nazarta ayyukan online writers din, da sauransu. Ko ma dai mene ne, fahimtarsu suka fada, kuma dole ne na girmama fahimtarsu.

Sai dai ni a nawa bangaren bana tare da wannan ra'ayi, wato a nan fahimtarmu ta sha bamban. Saboda da farko su kansu kafafen sadarwar zamanin (social network) da marubutan ke amfani da su wurin yin rubuce-rubucensu, ya kamata mu fahimci abubuwa akalla guda biyu zuwa uku a kansu: Na farko, yanar gizo wata duniya ce da ke tafiya kafada-da-kafada da duniyar zahiri, hakan ne ya sa duk wani abu na lalacewa ko gyarawa da ake yi a yanar gizo a zahirin ma ana yi, wato da marubucin online da wanda ba na online ba duka za su iya rubuta daidai ko kuskure, marubucin da ya so shi yake daukar rubutunsa ya mika wa wadanda za su yi masa gyararraki kafin ya mika wa makaranta. Na biyu, a yanzu da muke karni na ashirin da daya, amfani da yanar gizon ya zama kamar dole ga kowane dan adam ba sai marubuci ba. Don kusan kowace sana'a da muke da ita a zahiri, to akwaita a online. Hakan ne ma ya sa a yanzu kasuwancin littafin ya koma online. Ke nan za mu iya cewa kusan gaba daya an zama marubutan online.

Na fi gamsuwa dai idan aka ce wasu daga cikin marubutan online ba sa kokarin kiyaye ka'idojin rubutu, ba su damu da koya tare da nakaltar abubuwa da dama a rubutu ba kamar; bincike, salo da sarrafa harshe, zubi da tsari, direwar jigo da sauransu. Sukan shiga da ka, watakila saboda suna ganin ai ba bugawa za a yi a kai kasuwa ba.

Mujallar ADABI: wane hasashe kake da shi game da makomar rubutun Hausa a gaba?


A yanzu dai ma iya cewa makomar ba kyakkyawa ba ce idan aka kamanta da shekarun baya. Kuma tabbas idan a yanzu ba a gyara matsalolin da ke tunkarar rubutun Hausa ba, to a gaba makomar za ta kara lalacewa ne fiye da yanzu.


Mujallar ADABI: ko akwai wani kalubale da kake ganin rubutun Hausa na fuskanta?

Kwarai kuwa. A yanzu an samu karuwar marubuta sosai idan aka kamanta da shekarun baya, sai dai maimakon yawan ya amfanar sai ya kasance tamkar kamshin mutuwa muke yi wa rubutun, ta yadda za ka iske kullum abin baya yake yi maimakon gaba. Saboda a yanzu an zo wani lokaci da ba marubuci ne ke rubuta labarinsa shi kadai ba, hadin gwiwa ake yi shi da makaranci, ta yadda za ka iske marubuci ba shi da damar rubuta ainahin abin da ya saka a zuciyar sai dai ya rubuta wanda masu karatu ke so. Kwanakin baya muna hira da wata fasihiyar marubuciya (ba zan fadi sunanta ba) take sanar da ni tana dab da karkare labarinta, kuma a labarin ta tsara tauraruwar labarin za ta mutu duk da irin wahalhalun da ta sha a baya, to kuma sai makarantan ke ta tsokaci da cewar lallai ya dace ta warke daga wannan jinya (kada ta mutu), wannan ya sa ta tsayar da rubutun har take shawarta ta a kan anya idan ta kasheta ba za ta samu bore daga makarantanta ba? Tambayar ta ba ni mamaki. Kada kuma ka tsammaci hakan ga marubutan online kadai yake faruwa, har da masu buga littafi, don na san wanda hakan ta faru da shi kafin ya saki littafi na karshe.

Ka ga wannan babban kalubale ne. Domin idan har makaranci shi zai ce kaza za a rubuta, kuma a rubuta, to tabbas zai raina wannan marubucin, zai ji a ransa kirkirar ma da rubutawar duk ba wani aikin a-zo-a-gani ba ne. Wannan ma wani lamari ne da ya jawo durkushewar rubutu.


Mujallar ADABI: ana yin rubutun Hausa ne kara zube ba tare da wata kulawa ta musamman ba. Ba ka ga an kai matakin da ya kamata a karfafi harkar ta hanyar sanya takunkumi musamman ganin yadda wasu ta wannan hanyar suke cin abinci?

Wasu daga cikin marubuta sun yi yunkurin nusar da masu yin rubutun nan kara zube musamman a kafafen sada zumunta. To amma ba a wanye lafiya ba, saboda batu na gaskiya akasarinmu (mutanen yammacin Afirika) muna da tsaurin ra'ayi, karancin fahimta, da kuma taurin kai; wadannan dalilai ne ke sakawa da an miko mana gyaran da mu zai amfana, sai mu tsammaci kushe ko hassada ake yi mana. To amma duk da haka su ma wadanda suka so gyarawar, ina ganin kamar ba su bi ta hanyar da ya dace ba ne. Zai fi kyau a ce shugabannin kungiyoyin marubutan aka tara, aka musu gamsasshen bayani (saboda yana da wahala a samu shugaba marar fahimta) su kuma sai su isar da sakon ga mambobin kungiyarsu, ina ganin idan aka biyo ta wannan hanyar za a fi saurin samun gyaran da ya dace. Domin za su fi jin sakon da ya fito daga shugabannin kungiyoyinsu fiye da wanda ya fito daga wani wurin daban.


Mujallar ADABI: Shin kamar wadanne matsaloli ne zasu/suke tunkarar rubutun Hausan?


A yanzu marubuta suna da yawa kamar yadda na fada a baya, kuma suna da matukar basirar kirkira da kokarin kamanta kiyaye ka'idojin rubutu da nahawun Hausa da sauransu. Sai dai kuma mu da kanmu muka ragewa rubutu kima da daraja har ta kai yanzu littafan namu ba sa sayuwa a kasuwa, shagunan online din ma da ake sayarwa an daina saya. Saboda da kanmu muke rubutawa kyauta a online, har ma mu yi ta neman kai da shi ta hanyar tagging din mutane don su zo su karanta, ko ka iske an hada document ana ta rabawa a whatsapp...to babu yadda za a yi makaranci ya je ya sayi littafi alhali ga shi ana ba shi kyauta yana karantawa. Wannan babban kalubale ne, matsawar ba mu taru mun gyara ba to a gaba lalacewar kasuwar sai ta fi haka. Abu na biyu kuma akasarin marubuta yanzu muna da kasala, ba ma iya zagewa mu yi bincike a kan abin da za mu rubuta, ta yadda za ka iske idan mun nufi bangaren likitanci a rubutunmu shirme ya yi yawa saboda ba mu tambayi likitoci ba, haka idan bangaren tsaro ne da sauransu, wanda wannan na jawowa idan makaranci ya san abin ya ga an rubuta ba tare da bincike ba sai ya raina rubutun. To dole ne sai mun gyara wadannan abubuwa kafin mu ga daidai.


Mujallar ADABI: me yake kawo irin ita wannan halayya ta biyewa son zuciyar makaranta?

Rashin kwarewa da kuma fara rubutun ba tare da saninsa ba. Saboda idan har akwai kwarewa, to marubuci zai fahimci lallai shi ke da ikon tsayar da alkiyar kowane tauraro, ya yiwa wasu hisabi, ya yi wa wasu rahma, ya raya wasu, ya kashe wasu...duka aikinsa ne saboda shi ya samar da su, ya samar da duk wata rayuwa da suke aiwatarwa.

A lokuta da dama ya kamata marubuta su gane, ko da kana da baiwar rubutu (ka iya) to akwai bukatar samun gogewa. Don a kan samu wanda ya iya, amma bai goge ba. Misali: Dalibin da ke karantar aikin likitanci (duk hazakarsa) ba zai yiwu daga fito da shi daga aji a kai shi asibiti ya yiwa majinyaci tiyata ba, dole sai an bi matakai da dama kamar; fara gwaji da wasu dabbobi, da kuma kai shi asibiti ya ga yadda likitocin ke yi, sannan ya fara. To shi ma marubuci komai yawan baiwarsa, akwai bukatar ya mu'amalanci marubuta da manazarta (ya shiga cikinsu) ta haka ne zai samu wata gogewa ta abubuwan da suka shige masa duhu.

Mujallar ADABI: ko lokaci yayi da ya kamata Hausawa su koma yiwa rubutu kallon sana'a a maimakon abu na sha'awa?

E, ya yi. Kuma a yanzu akasari suna masa kallon sana'ar. Tun da hatta masu dora littafansu kyauta a kafafen sada zumunta (online writers) a yanzu su ma sun yi masa farashi, sai wanda ya biya ne zai samu ya karanta. Kodayake zuwan wannan tsarin nasu ya sa sun samu kalubale daga makarantan nasu (watakila saboda sun sabar musu da karantawa kyauta) to amma a nawa bangaren sun burge ni. Don tabbas rubutu sana'a ce da ya kamata a ce an martaba ta, saboda ko mutum na sha'awar sana'ar sai yana da baiwarta zai yi.

Mujallar ADABI: Ko mene ne dalilin da manya da kananan makarantu basa amfani da littattafan zamanin mu na yanzu sai na da?

Ba wai makarantu ba sa amfani da littafanmu na yanzu ba ne, suna yi. Don lokacin da muna Kwaleji an saka mu nazarin wasu littafai wanda a cikinsu akwai na yanzu, wato MURADIN ZUCIYA na Hamisu Gumel, sannan akwai littafin wasan kwaikwayo mai suna MALAM ZALIMU na Ado Ahmad Gidan Dabino wanda 2009 aka buga shi, har wa yau a cikin makarantar wasu sun yi nazarin littafin wasan kwaikwayo mai suna DAKIKA TALATIN shi ma na Gidan Dabino (MON) wanda aka buga 2015. Duka wadannan za mu iya cewa na yanzu ne. Ke nan a makarantu ana nazarin littafanmu na yanzu, sai dai ko a ce adadin ya yi karanci, wannan kuma ba ya rasa nasaba da karancin ingancin rubutun yanzu idan aka kamanta da na baya. Sannan a makarantu an fi ba wa dalibai nazarin wasan kwaikwayo a kan rubutun zube, a yanzu kuma rubutaccen wasan kwaikwayo ya yi karanci ainun.

Reactions
Close Menu