Fina-finan Tamil 5 da Bollywood ta kwaikwayaBollywood ta daɗe tana satar fasahar fina-finan wasu masana'antun da suka haɗa da masana'antar fim ta Amurka wato 'Hollywood' da kuma sauran masana'antun cikin ƙasar ta Indiya kamar su 'Tollywood' da 'Lollywood' inda ta kan  kwaskware su tare da fitar da su kasuwa wanda kuma a karshe fim din kan samu karbuwa sosai tare da zunzurutun makudan kudade.
Daga jerin ire-iren waɗannan fina-finai akwai wasu fitattun shirye-shiryen da sashen 'yan kasar ta Indiya masu amfani da harshen Tamil suka dagargaza kundi da su saboda farin jinin da suka samu inda a karshe ita ma masana'antar ta Bollywood ta kwaikwayi wadannan fina-finan inda kamar yadda ta saba abin bai zo bisa mamaki ba yadda aka kuma sake rubibin wadanda ta kwaikwaya din. Ga jerin fina-finan kamar haka;01.​'Suryavamsam'(Tamil) - 'Sooryavansham' (Hindi): fim din wanda Amitabh Bachchan ya fito a matsayin mutum biyo a cikin shi, an haska shi ne a kauyen nan mai tarihi wato Sarpanch inda a ciki karamin dansa Heera ya kasance jahili ne amma kuma ya san ya kamata, shiri ne da aka yi shi akan matsalar iyali kuma asali Tamil ne suka shirya shi tun a shekarar 1997 inda ana ainihin darakta Vikraman ne ya bada umarnin shirin yayin da jarumi Sarath Kumar ya kasance babban tauraron shirin. Rawar da Amitabh ɗin ya taka a 'Sooryavansham' kwakwayo ne na wadda Sarath Kumar ya taka a shirin 'Suryavamsam'.
02​'Thevar Magan'(Tamil) - 'Virasat'(Hindi): shirin 'Virasat' na Anil Kapoor, Tabu da kuma Pooja Batra shiri ne da ake yi masa ganin na musamman ba wai kawai don daɗaɗan waƙoƙin dake ciki kawai ba har da ma saƙon dake cikin shirin wanda kuma yayi nuni ne da cewa ilimi hanya ce ta tallafar rayuwar al'umma. Fim ɗin kwaikwayo ne na shirin Tamil wanda darakta Bharatan ya bada umarni mai suna 'Thevar Magan' wanda aka yi tun a 1992 inda jarumi Ulaganayagan Kamal Hassan, Sivaji Ganesan, Revathi, da kuma Gouthami suka fito a cikinsa. Fim din har wa yau an kwaikwaye shi a Kannada a matsayin 'Thandege Thakka Maga', kuma anyi fassarar shi izuwa harshen Telugu a matsayin 'Kshatriya Putrudu'.
03​'Run'(Tamil) - 'Run'(Hindi): shirin Tamil ne wanda ya fito a shekarar 2002 inda R. Madhavan, Meera Jasmine da kuma Raghuvaran suka ja ragamar shirin. Shirin ya samu yabo daga masu sharhi kuma na ɗaya daga shirye-shiryen da suka taka leda ta fuskar kasuwa. Bollywood ta kwaikwayi shirin ba tare da sauya sunan ba kuma taurarin da suka fito a ciki su ne Vijay Raaz, Abhishek Bachchan, da Bhumika Chawla a matsayin manyan taurari. Wanda ya bada umarnin shirin sanannen mai shirya wasannin gidan sinaman nan ne wato Jeeva. Sai dai shi wannan maimaici na fim ɗin Run ya zamo asara ne a ƙarshe domin bai yi kasuwa ba.
04​'Mudhalvan'(Tamil) - 'Nayak'(Hindi) siyasa ita ce jigon shirin fim ɗin 'Mudhalvan', wanda darakta Shankar ya bada umarni kuma jaruman ciki suka kasance Arjun, Manisha Koirala, da kuma Raghuvaran a sahun farko. Fim ɗin an kurara shi a matsayin shiri mafi soyuwa a zukatan masoya a lokacin da aka sake shi. Bollywood da suka kwaikwayo shi sunan da suka sa masa shi ne 'Nayak', kuma jarumi Anil Kapoor, Rani Mukerji, da Ambrish Puri ne jagororin shirin, tun a farko Shankar ya nemi Arjun din da ya ja ragamar shirin ana ainihin bayan da Rajinikanth yaƙi fitowa a ciki.
05​'Singam'(Tamil) - 'Singham'(Hindi): shirin wanda aka tsara shi akan rayuwar wani Ɗan Sanda inda Suriya ya kasance babban jarumin shirin ya kasance shiri mafi shahara na jarumin. Hari ne ya bada umarnin shirin inda kuma Rohit Shetty ya bayar da umarni a sabon da aka kwaikwaya wanda tauraro Ajay Devgn, Kajal Aggarwal, da Prakash Raj suka fito a cikin shirin. An fassara shirin izuwa harshen Hausa inda sunan ya kasance 'Singham Mai Gaskiya'.
Reactions
Close Menu